← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 137

Sashe 16

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tsarabar da Yakubu yayiwo wa matarsa data qaninsa harda qananan kaya irin wanda Arna suke sakawa, a cewarsa daya kalli haram a jikinsu gara ya kawowa Balaraba ta saka masa yasan zasuyi mata kyau matuqa ya kuma hado da Bara'atu itama tayiwa dan uwansa kwalliya harda Bilki da Aisha dasu Amina ya warewa kayane riga da skirt wasu da wando irin me roba idan an saka suna kama jiki a lokacin su kansu Arnan basu fara shigar badala ta rabi tsirara suna yawo a gari ba amma dukda haka su a gurinsu irin wadannan dinma sababbin abu ne. Aiko da yar bafulatanat tasa ta saka ba qaramin kyau tayi ba, seda Audu yazo Bechi Bara'atu ta tsantsara masa kwalliya da nata kayan, yanda tayi kyau ta burge shi ya sakayi cewa Yakubun mezzo hana su fara kawo ire iren qananan kayan na Mata dana yara harda ma na Maza dan suma yazo musu da Jeans da shirts tunda yace duk akwai su kuma suna da sauqi a can.

Haka kuwa akayi Bayan Yakubu ya koma ya qullo dila guda ya aikowa Audu. Tun kafin kayan su iso daman yayi tallarsu dan haka yana bude dila bata rufe sati ba se burbudi masu siyan daidai da sari sun kwashe, yanda mata suka dinga zuwa suna siya da siyawa yaransu ya bashi mamaki, kuma a lokacin bakin Asibiti kaf shi kadai ya bude irin kayan wannan dalili yasa saya tashi turawa Yakubu kudi ya ninka wanda suka siyo da farko kamar wasa se gashi sana'ar ta karbeshi ya zama wata dilar ma idan ya kwance bata kwana dan ya dena siyar da guda daidai ma yan sari ne suke kwasa a qasa da wata shida se gashi ya kama hayar Rumfa a cikin kasuwar sabon gari inda akafi siyar da ire iren wadannan kayayyakin ya kumayi suna idan ka shiga kasuwar tun daga qofa daka tambayi shagon BECHI za'a kaika. Cikin wannan yanayi ludufi da budi yayi ta zuwar masa, be kuma tsaya kan iya kayan nan ba yaci gaba da gwada duk wata sana'a daya san zata kawo kudi, kantin da suka bude a gida kuwa kullum sake habaka yakeyi dukda kwanaki sun samu Asara an farke shagon an kwashi kaya daga baya aka kama yaran da sukayi kuma sukace Hashimu ne ya sakasu, Dada ce ta hana su daga maganar, an dai je har gaban Me gari akan ayi musu iyaka da Hashimun wanda a wanann karon Goggo Fadi kanta ta nuna masa bacin rai akan abinda yayi Audu kuma ya sake sarar kaya harma da wanda da babu a shagon ya zuba.

Tun haihuwar Bara'atu ya qudurce a ransa cewar ze kafa sana'ar siyar da fetur a Bechi, koda masu Ababen hawa da suke da buqatar Fetur din daidaikune amma abinda ya faru na rasa wanda ze taimaka masa ya kai Balaraba Asibiti yasa ya yanke shawarar ze fara Bunbutun koda kuwa ba za'a siya kullum ba wata rana tana iya daurowa a samu me siyar. Aiko ya samu wani Abokinsa Falalau da suke cewa Fala dan bakin Kasuwa ne a nan cikin Kano tare suke a bakin Asibiti kafin ya kuma bunburu da kuma siyar da kayan gyaran mota, a gurinsa ya sari Mai harda su man juye da sauran yan abubuwan buqata, anan qofar gidansu ya kafa Katako inda ya dora jarakunan Man, Baballiya na kula da shago yana kuma kula da Man shida Abdullahi kuma cikin ikon Allah da masu motocin daukar kaya suka gane da yawa basa damuwa da su shawo Mai a Kano kafin su dawo gida tunda sun san da akwai.

A cikin Kanon ma ya bude guri nan cikin Goron dutsen ya ajiye wani yaro yana kula masa da Man shi kuma ya tafi Kasuwa, an samu shekara daya a haka zuwa sannan Ya fara damuwa da rashin samun cikin Bara'atu domin Balaraba harta kuma samun wani cikin yanzun bayan zuwan Yakubu hutun qarshen shekara ta biyu a karatunsa na shari'a. Damuwarda Bara'atun take nunawa yasa ya danne tasa sannan kullum Dada na nuna musu cewar Haihuwa lokaci ne idan Allah ya kawo zasu samu tunda ga yar uwarsa Bilki nan me shekara biyar a daki har yau bata samu ba itama toh suyi haquri suyi addu'a ubangiji ya basu a lokacin dayafi musu Alkhairi.

Da Abokinsa ko muce Amininsa Lado ya tattauna maganar, shiya ke ce masa daman yawanci Matan matafiya basu cika samun ciki da wuri ba, Audu yace ya akayi Ita Balaraba ta samu ciki toh bayan yafi Yakubu yawan zuwa gida? Lado yayi dariya yace
"Ta yuwu lokutan da kake zuwa basu dace da irin lokutan da mace take daukar ciki ba, shi kuwa kaga idan yazo ya kanyi wata guda ko sama da haka a gida kai kuwa zuwanka a tsitstsinke ne wani sa'ilin ma baka wuce kwana biyu uku ka juyo, nima wani Abokina da yake karatun lafiya naji ya fada an musu a karatunsu cewar da akwai wani lokaci bayan gama Al'ada da kwayayen halittar mata suke nuna su shirya daukar ciki to idan anyi dace an samu tarayya a irin lokutan nan shine zakaga an samu rabo bawai yawan kwanciya da mace ne yake kawo ciki ba".

Wannan magana da sukayi da Lado ta sakashi bayan yaje Bechi ya roqi Dada akan yana so su tafi Kano tareda Bara'atu ze kaita Asibiti dan yana so a gaya musu wanne lokaci ne mahaifarta take shirya daukar ciki, Dada bata qi ba suka tafi satinta daya ya maidata bayan tasha yawo a Kano ya kaita gurare dan wannan shine karonta na farko da taje, ya nuna mata gininsu da qiris ya rage a kammala ta ringa murna kuwa tana komawa ta qyarawa Balaraba dukda Audun ya gargadeta akan karta gayawa kowa tukunna amma murnar zasu koma Kano yasa ta kasa daurewa cikin ikon Allah kuwa komawarsa babu jimawa ta fara amaye amaye ko ba'a fada ba ansan ciki ne Dada ta ringa cewa gashi nan da suna garaje harda zuwa Asibiti ashe da cikinta ma lokacin bayyanarsa ne beyi ba. Da Audu ya sake zuwa kuwa haka ya kwashe su da Balaraba sukaje Kumbotso inda take Awo akayiwa Bara'atun itama register zata fara zuwa idan cikinta yayi wata hudu a sannan watansa biyu da kwanaki. Ko tari Dada batayi ba dan ba zata so a maimaita abinda ya faru a cikin Balaraba na fari ba shiyasa ko Audu bezo gari ba ranar Awonsu tazo da kanta take tasa su gaba ta rakasu ko kuma Bilki ba kuwa qaramin surutu take sha gurin Goggo Fadi ba wai rashin kunya ce.

Wani lokaci Audu yazo gida kamar yanda ya saba, a lokacin cikin Balaraba nada watanni takwas na Bara'atu kuma yana wata biyar. Da yammaci ta tasashi gaba da wai makani take so taci, ya rasa inda ze samoshi anyi shukar makanin amma ba'a fara kawoshi gida ba. Cikin Bara'atun irin me dan banzan tsirfa ne idan kuma ta rasa abinda take so haka zata wuni ranar tana kuka da baqin Rai haka Audu ya fita akan Sabon Mashin din daya siya saboda zirga zirgar kaisu Asibiti ya ajiyewa Baballiya, gurin Shamsu Abokinsa ya tafi yana tambayarsa inda za'a samu Makani, ya ringa tsokanarsa suka hau mashin din suka tafi gonar Usman da Shamsun yace yayi shukar makani kuma ko babu yawa za'a iya cirar wanda ya nuna. Gonar tasa tana can kusan babban titi wanda tanan zaka gangaro ka dauki hanyar shiga Bechin sun samu Usman din ya debo masa da yawa kuwa cikin wanda ya fara cirewa.

Sun fito daga Gonar suna magana hankalin Audu nakan wata mota can daya hango tsallken Titi tun shigarsu gonar ya ga motar a tsaye yanzu kuma har mutanen ciki sun fito sun bude gabanta da alama ko lalacewa tayi. Seda ya daure ledar Makanin a kan mashin kafin ya cewa su Shamsu yana zuwa ya tsallaka can gurin motar, tun kafin ya qarasa yake jiyo muryar mutumin da yake zaton shine me motar yanayiwa Driver sa fada cikin harshen turanci shi kuma se faman haquri yake bashi. Audu ya qarasa yayi musu sallama dukda bashida tabbacin Musulmaine, mutumin ya juyo ya kalle shi, tabon sallah daya gani a goshin sa ya tabbatar masa da cewar Musulmi ne. Mutumin ya amsa sallamar Audu yana qare masa kallo kamar yanda shima Audun yake kallonsa, Dattijo ne dan a qalla ze iyayin shekaru Hamsin da biyar zuwa sama fari tasa me matsakaicin jiki ya tsuke cikin Coat baqa kana kallonsa kasan ya juqu a Bako sannan motarsa zata sanar maka cewar babban mutum ne da gani.

Cikin Turanci Audu ya gaishe shi yana tambayarsa meya faru dan beyi zaton yanajin hausa ba tunda turancin yaji yana yiwa Direba ga mamakinsa se yaji ya mayar masa da Hausa yace
"Wallahi Motar muce ta tsaya, na dauka ma wani gyara ne kuma wai Ashe mai ne ya qare mana qarqaf kuma saboda shashanci wannan Direban be duba man ba kafin mu kamo hanya gashi yanzu a nan bansan yanda zamuyi ba babu kuma service din kira a nan gurin ballantana nayi waya cikin Kano a kawo mana wata motar" ya qarasa yana daga qata waya da sau daya Audu ya taba ganin irinta hannun wani Bature da yake siyan kaya a gurinsa.

Direban ya sakeyin qasa da kai yana cewa
"Kayi haquri Sir, nidai nafi zaton malejin motar ne ya samu matsala dan seda na duba komai kafin mu taso kuma naga man da muke dashi ze iya kaimu gida har yayi ragowa lokaci daya ya sauka kuma motar ta mutu"
Mutumin ya galla masa harara ba tareda yace komai ba tunda motar ta tsaya yake nanata masa maganar wai malejin ne be nuna masa daidai ba yaci gaba da daga wayarsa yana neman service yana kuma dan waige waige a fakaice dan a tsorace yake, koda yake duniya na kwance a sannan amma wannan Titi da yake shiru tun tsayuwarsu ko Keke be gifta ba balle mota se Audu daya fado musu katsaham kamar Aljani kar suje ba shi kadai bane a mamaye su ayi musu wani mugun abun.
Chapter 16 · 0% Book details