Sashe 65
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wasa ya wasa, qaramar Magana ta zama gaske, kamar yanda Audu ya barwa Hayatu sallahu ya isar da saqo dan Bara'atu na dawowa gida ya doma sallama kofar gidansu, ta fita suka gaisa, batayi mamakin ganinsa ba saboda Abokanan Audunna Bechi sukan leqa sa'i da lokaci suga Yaranta. Sukance Audu ya musu rana dan haka bazasu yada yaranshi da suke kusa dasu ba dan idan ka ture halin Audu na Rashin son gaskiya da shegen girman kai yana da kirki, kuma abun hannunsa be rufe masa ido ba daidai gwargwado yana kyautatawa Yan uwa da Abokanansa.
Bayan sun gaisa da Hayatun ta tambayeshi jikin matarsa datayi samu da jijjiga lokacin haihu da yake abun a gida ya faru se daga baya aka kaita asibiti abin se yaso ya taba mata kwakwalwa dakyar dai da taimakon Allah aka samu kanta dukda har yanzun dai bata koma yanda take a canbaya ba.
Seda suka gama gaishe gaishe kafin ya amayar mata da ainihin abinda ya kawoshi, tayi shiru tana sauraronsa harya gama kafin tace
"Shi Audun da kansa ya gaya maka ko kuma aike yayi maka?"
"Dakansa yazo lokacin baku gari shineya barmun sallahu akan nazo na tayashi biko da banbaki kafin ya dawo".
"Ya yardada gaskiyar ban kashe masa Da ba kenan yanzu?" Ta tambayeshi cikinkar yayyar murya, tausayinta ya kama Hayatun, Bara'atu mace ce me nutsuwa da matuqar haquri, sun taya Abokinsu baqin cikin rasata kuma a cikinsu da akwai wadanda sukayi niyyar neman Auranta se dai sanin waye Audu da tabbacin da suke dashi na cewar be dena sonta ba yasa suka gaza aiwatarda nufinsu saboda Tijarar Audu abar gudu ce tun zamanin yarintama balle a yanzu da karansa ua kai tsaiko.
"Bamuyi wannan maganar dashi ba, amma na tabbata a zuwansa baya raba nasaba da warwarewar komai, ta yiwu ya samu gamsuwar cewar baki aikata abinda aka zargeki dashi ba shiyasa ya dawo ku daidaita. Nidai abinda zan iya ce miki kiyi haquri ki mayar da komai ba komai ba ki koma dakinki kodan saboda rayuwar Yaranki. Kowa ya sani Audu be kyauta ba kuma shikeda laifi cikin duk al'amuran da suka faru amma kin sanshi, qi fadinsa baze barshi ya nuna gazawarsa ba sedai na tabbata ko be furta da baki ba zakiga Nadamarsa a aikace dan haka karkiyi wasa sa damar da ubangiji ya baki, kiyi tunani ki yankewa kanki hukunci".
Ta koma gida tana ta juya maganganun Hayatu, Inna Hajara bata ce mata komai ba dukda chanjin yanayin da ta ganta ciki se tayi tunanin kodai Hayatun yazo mata da Maganar Aure ne saboda irin zaryar da yakeyi tuntuni tasa tayi tunanin hakan.
Har aka kwana biyu da zuwan Hayatu Bara'atu bata sake ba, walwalarta ragu ainun, wani irin cakudadden yanayi take ji na farin ciki, damuwa da kuma zullumi. Farin cikinta Bikonta da Audu yayi domin ba zatayi qarya ba Allah ya sani tana qunar Audu ba kuma ta tsammanin zata iya zama da wani Namiji a duniya ta soshi bayan Audun wannan dalili yana daga abinda yasa zamanta a gida babu marshinshini be wani dameta can ainun ba,
Damuwarta kuma tunanin idan ta yarda ta koma wace kalar rayuwa zatayi a gidansa Alhalin Binta tana nan?
Zullumin da take ciki kuma shine na tunanin shin Audu ya gane cewar Binta sharri tayi mata ne da har ya nemi ta koma ko yaya? Zata so ta san amsar tambayar nan domin itace zata qara mata qwarin guiwar Amincewa buqatarsa ko akasin haka. Zata so su hadu dashi suyi maganar nan kafin ta kaiga yanke hukunci,
"Nikam lafiyarki Bara'atu? Yaro na tsaye kanki yana magana tun dazu kamar me bacci kin masa shiru alhalin idanuwanki a bude suke?" Inna Hajara data leqo daki dalilin maganar Babannan da take jiyowa yana ta maimaita abu daya, Gidan kitso Bara'atun tace yaje ya tambayo mata tunda ya shiga dakin yake fada mata matar tace taje yanzu bataji ba balle ta bashi amsa tayi zurfi cikin tunani har seda Inna Hajar tayi magana da qarfi kafin ta ankare.
"Banji shi bane Inna, me kake cewa kai kuma?" Ta fada tana gyara zamanta. Inna Hajara ta shiga cikin dakin da kyau tace
"Ai daman ba zakiji shi ba, kai yi tafiyarka wasa, ki fadamun me yake damunki tun randa Hayatu yazo gidan nan na ke lura dake yanayinki ya canza".
Barin maganar a ranta baze magance mata komai ba kuma a wannan gabar tabbas tana buqatar Abokin shawara wannan abun yasa ta fuskanci Inna Hajarar ta shiga fada mata yanda sukayi da Hayatun ranar da yazo.
Baki ta saki galala tana kallon Inna Hajara wadda ta taqarqare ta rangada guda kafin ta daga hannu sama tana cewa
"Allah na gode maka daka sa zanga wannan ranar da raina ban mutu ba, Allah na gode maka daka karbamun Addu'ata. Dama bangaya miki ba? Ba a banza Audu ya jibanci lamuranmu fiye da da ba, tun baroqarki gidansa ban taba yin salla na tashi ba tareda na roqi ubangiji daya bankada sirrin duk wani Azzalimi daya qulla miki wannan mugun shairin ba gashi kuma Allah maji roqon bawansa ya amsa roqon mu. To meye abin damuwar daya kika kasa walwala? Wannan ba abin kiyi rawa kiyi shewa ki godewa Allah ne amma shine kika tsangwami kanki kwana kusan uku bana tsammatar kinyi dariya? Ko kuwa bayan Batun komen akwai wata maganar ne?".
"Babu wani abu bayan wannan amma ni abinda ya dameni Inna banida tabbacin cewar Audu ya zabi ya maidani saboda gane gaskiyar abinda ya faru a baya ni nafi kyautata zaton zeyi hakan ne saboda Yayansa. Sannan Inna karki manta har yanzu fa Binta tana cikin gidansa, kina dai ji har ta kori Amaryar da yayi kin kuma ji rade radin da akeyi a gari kan itan ma wata qullalliyar ta qulla mata kenan bata canza zani ba tana nan da halinta babu abinda ya sauya" Bara'atun ta fada a sanyaye cikin karayar zuciya.
Inna Hajara ta galla mata harara tace
"Ai bari kiji, wlh wannan karon kika kuskura kika tsaya tsoron kishiya yayi tasiri a ranki se kinci ubanki. Ai maciji baya saran mumini a guri daya sau biyu, kin zauna da ita kinsan duk wani salon tuggu da munafuncinta dan haka kema seki shirya irin naki da zaki goga da bata hanyar cuta ko Ha'inci ba. Sannan da kike cewa saboda yayansa ne koma saboda menene dai abu daya ake fata kuma ya tabbata idan baki koma gidansa ba zaki cigaba da zama hakane babu Aure tunda dai kina kallo cikin Garin nan da kewaye labarinki babu inda be ratsa ba wanene ze Aureki?
Gidan san dai da kika gogo baqin fentin acan zaki koma ki wankeshi karma ki kuskura naji kin tado da wannan maganar balle har dalilin haka yasa ya janye muradinsa idan ma besan gaskiyar ba. Ko iya komawar da zakiyi ta isa ta karya Alqadarinta saboda ta dauki haqqinki ne saboda tayi silar ki fita daga gidan yanzu kuma Allah ya nufa zaki koma dan haka ma shiri zamu fara, yace da zarar kin amince yana zuwa za'a maida Auranko? To ki aika a kira Hayatun yau ki sanar masa kin Amince, in sha Allahu bazaki rufa qarshen watan nan cikin gidan nan ba zaki koma dakin Mijinki yan hassada da baqin ciki da masuyi mana dariya sedai su mutu Allah yayi abinda basu isa su hana ba".
Duk yanda taso fahimtar da Inna Hajara buqatar taja lokaci Audu yazo da kansa su tattauna kafin qulluwar kowacce magana qi tayi, daga qarshe ma takans taje ta samu Qanin Babansu ta sanar masa da cewar Mijin Bara'atu yazo biko bata ko tunanin maganar ta rushe tunda dama ba wani ginuwa tayi ba. Malam Sadi wanda yake cike da wulaqancin da Audu ya musu ya ginawa su Bara'atun sabon gida sannan ya siye gidan da sukaso tozartasu akanshi sedai kuma tsoron Tijarar Audun daya tuna furucinsa na cewar duk seya siye gidajen da suke ciki in suka bata masa rai sanda suka goranta masa cewar meye hadinsa da Bara'atun da har ze siya musu gida? banda Rashin zuciya matar data kashe masa Da ze dawo yana bibiya take ya kora musu gargadi sun kuma san ze aikata domin cefane Bechi yake tayi yana siyan gidaje da filaye tamkar wasu yan tsaki tuna wannan tasa yace babu komai duk sanda suka shirya suzo.
Dataga Bara'atu ba zata nemo Hayatu ba dakanta ta tura aka kira mata shi suka qulla magana ba'aja lokaci ba yayi takakkiya yaje ya sanar da Audu abinda ake ciki.
"Ashe har yanzu Bara'atu tana sona tana kuma muradin zama dani?" Audun ya fada kamar wani soko sanda Hayatu ya gaya masa yanda ake ciki. Hayatu ya karkace yace
"Bana tsammanin haka, domin munyi magana da ita kuma ban fahimci wata alama taso ko muradi a tattare da ita ba se Damuwar data nuna mun ta son sanin ka yarda da ita ko kuwa har yanzu kana mata kallon Mara Imani Azzaluma?"
"Bana son maido da wannan maganar tunda har wadda ta zalunta ta yafe mata magana ta qare a gurina" ya bawa Hayatu amsa yana wani dauke kai kamar bashi ya gama shauqi yanzun nan ba, Hayatun ya sake cewa
"Kenan har yanzu kana kan bakanka? Dagaske Zuciyarka ta aminta da cewar Bara'atu ta aikata abinda Binta ta zargeka dashi?" Hayatu ya tambayeshi yana tsareshi da ido, seya miqe tsaye yace
"Ya za'ayi kazo ka tsitsiyeni kamar wani yaronka kana tambayata? Wannan fa abu ne daya shafeni nida Iyalaina kuma ni nake zaune dasu duk wani wanda ze bayar da shaidar Halin Bara'atu bafa ze kai kamar ni da nayi zaman shekaru sama da biyar da ita ba, ku sanin zahiri kukayi mata ni kuwa na santa har badini dan haka ba ku zaku ringa gayamun abinda zatayi da wanda zatayi ba. Saqo na baka ka isarmun na gode kwarai kuma zan sallameka yanzu In Allah ya yarda cikin zatin da ze kama nima zan shigo garin" ya qarasa yana laluba Aljihunsa ya zaro Rafar Yan goma na Takadda sababbi qal ya irgi dari biyar ya miqawa Hayatun.