← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 137

Sashe 33

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ko me zasuyi dashi se Allah, a irin arziqinsu ai wlh nama dai yaci ya gunduresu yanzu amma Allah sa suma ba jida zasuyi su tafi dashi su aje qulli qulli a firiza yanda Hajiyar nan takeyi ba su basu ci ba su basu bawa wani yaci ya musu addu'a ba kai Hajiya Binta fa akwai Rowa alqur'an" Lantana ta shiga jero zance babu kai babu qafa. Yanda Bara'atu bata tanka ba haka Mairo kamar bata gurin, wannan nadaga abinda yasa take qara ganin girman matar. Ba ruwanta ta shiga sabgar da bata shafeta ba, aikin daya kawota gidan kawai take yi idan tazo da safe ta gama musu kalaci da wuri take dora na rana wata rana ma sha biyu ta gama data gama ta karbi rabonta zata tafi se kuma gurin qarfe uku ta dawo ta dora na dare shima tana saukewa zata tafi se kuma gobe da safe musamman yanzu da Binta tasa aka hade girkin tun zuwan Hadiza a yanda ta cewa Bara'atu ta dena girki da kanta, kwadayin Nama da Kazar daya kawo qanwar tata seta koma haka idan anyi girkin zata tsaya a raba ta kwashe duk abin arziqi ta hadasu da qasan tukunya ita bata ci ba ita bata bari wani yaci ba ta bakin Lantanar, ba kamar Mairo ba ita lantana idan tazo tun safe seta kai Taran dare har se Audu ya dawo Bintan ta fatattaketa sannan zata tafi yanda kasan bata da Miji balle Yara.

Haka suka gama suyar ko dandanon gishiri a harshenta ta koma daki. Washe gari tun sassafe aka ringa shigo da kayan cefane, guraren Goma Binta ta aiko kiranta, A falon Audu na sama ta sameta tasha kwalliya abinta ba zakace jego take ba. Ta gaidasu ta zauna tana satar kallon Audu da tun maganar jiya be sake ce mata komai a gidan ba dubasun da yake da Asuba ma beje ba yau. Kudi ya tura mata murya a daure yace
"Gashi nan, ki duba cefanen da aka kawo, abinda babu se a siya sannan su Bilki suna hanya bansan ko su nawa bane ki gayawa Mairo a saka abinci da yawa"

Tayi shiru a ranta tana mamakin yau kuma ita aka bawa kudin cefane sannan ita ake cewa ta fadawa Mairo a qara abinci abinda ko ran girkinta Binta ke fadar abinda za'a dafa.
"Shikenan na sallameki" ya sake fada seta miqe ta dauki kudin tana jin Binta cikin kissa murya qasa qasa tana ce masa
"Ko kaifa, ai ya kamata dai itama ta ringa jin matar gida ce ba wai ace komai sedai taga anayi ba kaga kar suzo a qara tafiya dani a baki ace na kankane komai"

Ta tafi tana mamakin Bintan a ranta, wato matar nan ko wagainiya Albarka shiyasa wani sa'ilin bata ganin laifin Audu saboda Bintan tamkar me rufa ido take. Bata taba mata Tijara ko cin mutunchi a gabansa ba, idan yana nan nunawa take nan dunita tafi kowa son su zauna lafiya da Bara'atu amma ita taqi bata hadin kai, da hakan take kanainayeshi kullum tana nuna masa laifin Bara'atu ne ita ce bata so su zauna lafiya, Bara'atu ce take fadawa yan uwansa mugun abu akanta shiyasa kowa baya sonta, Bara'atu ta tsaneta bata da buri illa na taga bayanta sannan ita kuma tayi ta nuna bajintarta da son jan Bara'atun da yayanta a jiki a gaban idonsa idan yana nan har kyautar abubuwa take kai mata ko yara yana fita tabi ta karbo abinta ta dora da Tijara shiyasa baze taba ganin cutar da take mata ba.

Maganar girkin kanta da farko ta hana ko gaidata masu aikin suyi da kuna ta canza ra'ayi ta karbe girki ita ta gaya mata ainin dalili amma shi se tace masa saboda Bara'atun ta huta ne hidima tayi mata yawa ga yara ga girki gara Mairo ta ringayi gaba daya tubda dai biyanta akeyi kuma dama kullum se tazo ko ba rabar girkin Bintan bane ire iren abubuwan da suke qara dagula zamansu kenan, shi tunda kunnene kawai se abinda yaji ba ruwansa da bin ba'asin ya akayi cikin kissa zata tunzuro shi ya dauki fushi da ita yanzu kuma da taso qulla wani abun shine zatace ya bata kudin cefanen abincin suna dan ta tabbata ba Alkhairi ya saka Bintan yin hakan ba.

Mairo taje ta samu tace ta duba kayan, data tambayeta me za'a dafa toh tilas ta koma ta sake tambayo Bintan tace mata Shinlafa da tuwo kawai zasuyi sauran abubuwan ta bayar da aikatau wannan yasa ta dan samu nutsuwa qila abincin iya jama'ar Bechi za'a bawa shiyasa ta barshi a hannunta. Tun rana suka fara rage aiki, su Bilki da Aisha da matansu Aminu ne suka yo gaba sauran dangi se gobe suna haka suka tasata gaba da tsiya harta rasa inda zata tsoma ranta wai daga dawowa harta tsomare a qauyen ma tafi kyan gani ta bari tsoron kishiya yayi tasiri a ranta.

Har an idar da Isha suka karbi baquncin mutanen Ikko, Yakubu da iyalansa Bara'atu ta rasa ina zata tsoma ranta saboda murnar ganin Balaraba. Suka rungume juna cike da kewa, Balaraba tayi kyau ta qara zama wata babbar Mace fata se walwali takeyi ita kuwa Bara'atu abin se godiyar Allah kawai. Daga gefe Aisha dake kallonsu tace
"Wato kwanciyar hankali duniyace, ku kalli dai idan daula da jin dadi ne Yaya Bara'atu tafi Yaya Balaraba samunsu amma kalle su ki gani banbancin kamar sama da qasa kowacce da ka ganta base an gaya maka matsayin da take a cikin gidanta ba"

"Aisha kenan kedai da Allah yasa kike ke kadai a gun Mijinki kici gaba da gode masa domin ba zaki gane qalubalen me Kishiya ba se kina da ita duk abinda zaki fada ko ki bada shawara akai hasashe ne kawai tunda baki san ya ainihin matsalar take ba" Sauda Amaryar Aminu ta bata amsa.

Bara'atu kuwa a dakin Audu ta sauki Balaraba, ta fita ta kawo mata ruwa da abin tabawa tace
"Bari na dora muku abinci wannan bazata haka ace zakuzo ko Yaya Audu be sani ba"
"Wai injiwa? Audun da shi yaje ya dauko mu daga filin jirgi" Balaraba ta fada. Bara'atu ta gwale ido tace
"Filin jirgi? A jirgi kuka zo?"
Balaraba ta harareta tana dariya tace
"Ji yanda kika gigice kamar wnada nace miki da fiffike mukazo, jirgi muka hawo mana abin Allah in gaya miki yau se ga Balaraba a jirgi qiris ya rage na haihu saboda tsoro" suka kwashe da dariya gaba daya. Bara'atu ta sake cewa

"Amma shine be gaya mun zaku zo ba?"
"Ba zata yayi miki gashi ai kinfi yin murna da muka zo yanzun, ke ni ba wannan ba ya naganki gaka qashi da fata ko laulayi kikeyi?" Balaraba ta fada tana kallon Bara'atun, seta miqe kawai tana cewa
"Bari naje na dora abincin"
"Karki wahalar da kanki seda muka ci abinci muka taho tafiya a jirgi kamar wanda Aljanu suka ragewa hanya? Ni banma san minti nawa mukayi ba kedau Allah ya qara mana arziqi me amfani Allah kuma yasa badi mu lula muyi tafiya me nisa a Jirgin muje mu sauke farali" cewar Balaraba.

Dukda haka Bara'atu taqi zama tace to bari taje su gaisa da Yaya Yakubu daga haka ta tsere, bata so ta zauna tunda Balaraba ta fara zancen ta rame ko ciki ne da ita tasan yanzu magana zata sake dagulewa sedai tana fita Bilki ta shige ta samu Balaraban ko kyakykyawar gaisawa basuyi ba dan tana sallah suka shigo yanzun taje ta gaida Yakubun kuma jira taje Audu ya matsa ra kwashe duk abinda ya faru da wanda yake faruwa ta gaya masa amma bari ta fara da Balaraban.

Tas ta labarta mata komai daya faru basa nan,
"Yanda kika san sallamammiya Bara'atu, na fada mata da nice wlh tun daga kan ginin nan gayyar zata watse. Hauka ma akeyi suci Talauci tare sannan dadi yazo ace ta zama yar kallo itafa da Boyi boyin gida babu banbanci. Idan anyi magana tace to ya zatayi? Na gaya mata taci abu ta kazan Yaya Audun tunda shi yake daurewa Bintan qugu tana mata iskanci kafin ta gangara kanta, ko Iskar qarya tayi ta musu rotse wlh duk zasu kiyayeta amma mata kamar Kazar da ruwa ya daka salaf salaf sedai tayita kuka in sun mata abu tana rama a haka fa kin ganta da kyan gani dalilin tajr Bechi kusan watanta biyar a can da ana gyaran gidan dawoqarta ne tayi wannan zabgewar to in aka cigaba a haka wata rana sedai azo a kwashi sauran qasusuwanta ai damuwa ta cinye tsokar tasa" Bilki ta fada cikin kumfar Baki.

Tsabar baqin ciki da takaici Balaraba kasa cewa komai tayi se qafa da take girgizawa, a haka Bara'atu ta dawo ta tarar dasu tana ganin Bilkin kuma ta tabbata ta gama kwaza komai. Fada Balaraba ta ringa mata kamar zata daketa da tayi tayi kuma seta koma banbaki da lallami dan lamarin Bara'atun ta rasa wannene ma zeyi amfani a ciki.
Banda kuka babu abinda takeyi ita kuma, haka suka kwana ko baccin kirki Balaraba bata iyayi ba, data rufe ido abin ze mintsineta ta tashi ta fara surfawa Bara'atun masifa can kuma tayi qasa tana lallashinta tareda bata dabarun kwatar yanci.

"Audu yana sonki, da ace baya sonki a yanda take wannan abun da ba zakiyi qarkon kawowa yanzu a gidannan ba. Wayo da dabara ne baki dasu, idan ta nuna miki wayewar Birni seki nuna mata ta qauye, akan me zaki ringa yiwa Kishiya kuka kin nuna mata kina tsoronta a fili ba dole ta takaki yanda taga dama ba, ai ko a ranki kina tsoronta ki dake idan ta fada ki mayar mata kar ki ganta wata zabgegiya kiji tsoron karta dake ki ai qarfi ba'a jiki bane idan kika qarfafa zuciyarki tsaf wlh zaki kaita qasa idan ma ta kaiku da dokuwa sannan shima karki raga masa tunda be dauki tsagin gaskiya ba. Wlh ki tashi ki kwatarwa kanki yanci idan ba so kike ki bata quruciyarki ki kashe kanki da kanki ba".

*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
Chapter 33 · 0% Book details