← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 137

Sashe 84

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bala'un da Dan fulani ya jere masa je afka idan ne rabu da ita ba sun zarce na Malam Salisu, Hashimu yace
"Dama a garin aure aure tun mutum na kwaso Arziƙi harse ya ɗebo tsiya gashi dai ka gani ai se ka san abinyi tunda wuri dan duk abinda Malam Sallau ya faɗa da wuya kaga be faru ba, seda ya hanani Auran Saude naƙi gashi ko ina karbar sakamakona"
"Aishi ba Allah bane bare kace duk abinda ya faɗa seya tabbata" Audun ya bashi amsa. Hashimu yayi dariyar rainin hankali yace

"Na fika sanin haka, amma tunda muka yarda dashi har muka zo tambaya gabansa ai magana ta ƙare, ya rahe naka ka ɗauki matakin daya dace" a gurin sukayi sallama Audu ya juyo Kano zuciyarsa fal wasi wasi. Ya daukarwa Yakubu Alƙawarin baze sake sakin wata mace ba gashi kuma yanzu dole ta saka zeyi sakin kuma ya san duk ta yanda zeyiwa Yakubu bayani baze taba fahimtarsa ba. Maganar gaskiya kuma baze zauna yanaji yana gani ya rasa komai nasa dalilin wata mace ba.

*ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.*

*NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...*

*LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...*

*A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:*

*- HAIR SALOON*
*-HENNA*
*-SPA*
*-DUKKAN*
*-PEDICURE*
*-MANICURE*
*-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI*
*DOMINSU SUMA*

*-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA*😊
*- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...*

*IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....*

*AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY 💅💯*

*Address 👇👇:*
*KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA*
*TEL:08133379628.*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 32*

Bayan daya dawo a ɗakin Hadizan ya sauka ta karbi girki, ya ringa kallonta ga Aminu dake da shekara daya da watanni biyu ga ciki da ko yau ko gobe zata iya haifeshi. Tausayinta ya kamashi duk da halin da take ciki amma tana ta kaida kawowa tana hada masa abinci. A zamantakewa Hadiza bata da laifi, mace ce ta gaske dan ze iya cewa a duk matan da ya aura babu tsayayya kamarta. Ta iya kula dashi haka tsakaninta da sauran Matansa tana mu'amalantar kowacce da sigar data zo mata. Duk bala'in Binta ta sarara mata sedai tayi a bayan idonta amma ya zeyi? Shidai baze cigaba da zama da ita ba domin ko ita idan zata masa Adalci inta san itace matsalarsa yaci ta nemi rabuwa dashi da kanta kawai su haƙura da juna ze saketa badan baya sonta ba sedai dan hakan shine maslaharsu baki daya ze kuma cigaba da daukar nauyinta har iyakar rai ze cigaba dayi mata duk abinda ya kamata tamkar tana gidansa.

Da daddare harsun kwanta ya tashi zaune, cikin nutsuwar dashi kansa besan yana da ita ba ua shiga yiwa Hadiza bayanin halin da ake ciki.
"Kuma ka yarda? Tamkar fa kayi shirka ne Audu ka tara sani da Allah. Ya za'ayi ace maka nice silar Karayar Arziƙinka kuma ka yarda shin Allah baya jarabtar mutum haka nan dole se wani abu ya zama sila?" faɗa hawaye ma zubo mata.
Audu ya murtuke fuska, yasan gaskiya ta fada to amma magana ta ƙare tunda har aka gaya masa kuma ya yarda dan haka yace

"Kinga muyi haƙuri kawai nidai na rigada na yanke hukunci na sakeki saki biyu, kina da zaɓi na kici gaba da zama a gidan nan ba se lallai mutane sun san na sake ki bama".

Kallon kayi hauka tayi masa kafin ta miƙe tana kuka ta shiga haɗa kaya, se yayi fakare kuma yana kallonta duk yaji babu dadi, da ace da wata hanyar da ze magance matsalar sa ba lallai seta rabuqa da Hadiza ba daya bi amma babu yanda ya iya. Washe gari ta bar gidan, Binta ta ringa rawa tana shewa, satin Hadiza ɗaya da tafiya ta haifi Aliyu, tayi maza biyu kenan sunyi kankan kan da Binta wadda keda cikin da na biyar Aisha nada na biyu a sannan. Tun Binta na saka ran Aisha zata bi bayan Hadiza har suka haihu wannan karon ma kusan tare tsiran kwana goma tsakaninsu Binta ta fara haihuwa ta samu Yakubu takwaran Alƙali, seda Babanta ya shiga maganar kafin ta haƙura da wannan takwara da aka mata da babban maƙiyinta Aisha kuma Abdullahi suna kiransa Sarki Al'amuran Audu kuma suka fara daidaita sannu a hankali Arziƙi yaci gaba da bunƙasa harya fi nada.

Aisha da Binta sukaci gaba da jera haihuwa, bayan su Yakubu Binta ta haifi Aisha wadda Audu yayiwa ƙanwarsa takwara ta rasu wata daya kafin haihuqar Bintan itama yarinyar watanta hudu ta koma a lokacin kuma Aisha ta haifi Ahmad shekararsa daya cif Binta ta haifi Jafar se suka sake jera haihuwa Binta ce ta fara ta haifi Faisal Aisha kuma Salim, shekara biyu suka sake yin mata duk su biyun Binta ta samu Hafsa suna kiranta Hajiya Ƙarama ita kuma Aisha Khadija. Daga nan Binta haihuwar ta dan tsayawa Binta har seda Aisha ta haifi Maimuna da Aslamiyya sanan Binta ta sake haifar Bashir da Lawal, burinta ya cika, ta tara yaya maza zarata har guda shida tafi kowa Kaso cikin dukiyar Audu.

Tsakanin Binta da Aisha zaman dai ba'a cewa komai, Binta bata fasa halinta ba ita kuma Aishar seta zame mata ƙarfen ƙafa domin dukta inda ta buga babu riba tayi tuggun tayi munafurcin amma abun yaƙi yaci. Audun da take taƙamar data san Lagonsa se Aishar ta fita bin yanda yake so domin zama tayi tamkar ruwa a cikinsu, hannu idan an saka mata ba zata ciza ba, duk abinda Binta zatace tayi idan ta titsiyeta ba zata musa ba koda batayin ba zata bashi haƙuri ta kuma baiwa Bintan ta yanda in Binta ta sake tada maganar daga baya a maimakon yaga laifin Aisha se faɗan ya juya kanta yace ta fiya son tada zaune tsaye.

Halin Aisha kuma ba Munafurci bane ko Kissa irin ta Binta Aa haka Allah yayita da sanyi, sedai nata sanyi ya zame mata Alkhairi ba irin na Bara'atu na haka ita bata ɗauki wargi ko rainin da har Binta zata bautar da ita ba kallo da ido idan bata ga dama ba zata mata ba idan kuwa zata kwana tana magana setaga dama zata ɗaga kai ta kalleta, da Binta ta buga ta buga taga babu riba seta saki lamarin Aisha ta koma kan Yayan gida wanda ruƙonsu gaba daya ya koma hannunta harda na Hadiza guda biyun ta saka an karbo su tun data yaye Aliyu an watsasu cikin yan uwansu.

Riƙo take musu irin na jeka ka mutu, iya babu kwaba, abinci me kyau idan sunci a gidan to ranar girkin Aisha ne wadda iyakarta dasu kenan in ta dafa abinci ta basu. Sanda aka maido dasu Aminu tacewa Audu zata ɗauke su har ta kai kayan yaran ɗakinta Allah kaɗai yasan me suka tattauna da Binta washe gari yace ta mayar dasu cikin yan uwansu saboda baya so kansu ya rabu sannan duk abinda ya shafi wani yaro a gidan muddin ba ɗanta ba babu ruwanta a ciki ƙarƙashin kulawar Binta suke.

Ita ɗin bata zurfafawa akan abubuwa dan haka bata tsananta ba ta maidasu kamar yanda yace ayi ba kuma ta shiga sabgar Yaransa muddin ba su suka kai kansu gurinta ba wannan zata musu duk abinda ya kamata sedai idan taga wani abun cutarwa ne take tsoma baki wani sa'ilin yaji ya sa a gyara wani lokacin kuma ya gwasaleta yace ai Yayansa ne ba kuma ta fishi sonsu ba, wannan halin sanyin nata da nuna ko in kula akan wasu abubuwan shiya janyo matsalar gidan bata tsaya iyakar kan Yayan tsakar gida ba ta shafi harda nata.

Da Binta taga ta kasa cin galaba akan Aisha seta haƙura ta mayar da hankali gurin ganin ta sake kama Audu a hannu da gidan gaba ɗaya, kamar yanda Turai tace mata ta bar batun Aisha domin ba wata tsiya bace ba kuma wani ji da ita Audun yakeyi sama da ita ba ta mayar da hankali gurin gina gobenta data Yayanta. Abinda yake a gabanta yanzu shine tasan duk ta yanda zatayi ta cusa yayanta a zuciyar Audu ya zamana bashida wani tunani idan bana su ba sannan tayi duk me yuwuwa ta dakusar da ragowar a gurinsa, karta barshi ya shaƙu dasu ta hakane kawai Yaranta zasu zama sune kan gaba a kamai nasa hakan kuwa akayi babu Boka babu Malam seda ta san yanda tayi ta raba tsakaninsa da Yaran dukda daman shiɗinma ba wai yana ta tasu bane sosai domin tunda harkokin Arziƙi suka sake buɗe masa ya zamana bashida isashshen lokacim zama a gida ma balle yayi hira da yaran yasan matsalarsu.
Chapter 84 · 0% Book details