← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 137

Sashe 85

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wani abu na gidan a hannun Binta yake kama daga abinci, sutura harkar karatu da duk wata buƙata kome ya tashi ita zece a tambaya, Riƙo take musu na mugunta ga Azabtarwa, a gabansa takan nuna ta damu da yaran ta ringa kai masa sukar duk yanda take ƙoƙarin jansu amma basa sakewa da ita irin dai yanda ta ringayiwa iyayensu, yaran Zubaida dana Hadiza da suka tasa se suka fara gudu suna tafiya gurin iyayensu dan itama Hadizar tayi Aure tuni, akan wannan Bintan ta haɗasu da Audu ya musu mugun duka dan tace iyayensu na zugosu duk zuwan da zasuyi se sun dawo da sabuwar ɗabi'a ya kuma kafa musu dokar hanasu zuwan daga ƙarshe ma tasa aka kaisu makarantar kwana banda Nata Yayanso se na Aisha data cw bata yarda ba sunyi ƙanƙanta, idan zasu tafi a Arziƙi irin na ubansu Garin kwaki ne da suga se ƙuli ƙuli provision dinsu idan ya bada kudi yace ayi musu siyayya seta soke ba kuma su isa su faɗa masa ba domin izayar da zasu sha se sun gwammace basu faɗa ba shima ɗin kuma be zama lallai ya yarda ba.

Yanayin matsatsi da damuwa da suke a ciki tasa cikin su shidan Hassan ne kaɗai se Aminu suke mayar da kai a karatu daman duk aji daya aka sakasu harda su Babannan da yaci ace sunkammala sakandire a sannan amma aka mayar dasu Aji daya na ƙaramar sakandire gaba daya. Banbancin da ake nuna musu ƙarara a fili tsakaninsu da sauran da iyayensu suke a gidan dukda Yayan Aisha ma ba wai sun tsira bane banbancinsu dasu uwarsu tana a gidan kuma ita bata jiran Audu ko Binta da komai na gida yake hannunta a yanzu duk abinda ya tashi na yaranta zatayi musu wanda sauran basa fahintar hakan gani sukeyi su aka tsana aka ware wannan tasa suka washshi uban da matan uban da sauran yan uwansu gaba daya kowanne ya ƙudire wani abu daban a zuciyarsa.

Haka rayuwa taci gaba da wullawa shekaru sun shude a kullum kuma rayuqar gidan Audu lalacewa takeyi a maimakon ta gyaru, ya saki komai a hannun Binta ya fantsama duniyar neman kudi kuma Alhamdulillahi rayuwar tana gara masa. Yanda ya faro tushen Arziƙinsa tareda Yan uwa da yayan yan uwansa wanda ba wani karatu me zurfi sukayi a wancan lokacin ba a sannu zamani yana canzawa sauye sauye suna zuwa a duniyar kasuwanci da akwai buƙatuwa ta mutane masu wata kwarewa ta musamman akan wasu al'amiran dole ya fara shigo da bare yana daukar Ma'aikata masu kwarewa ta musamman. Wannan ya zaburar da Binta, ta watsa yaranta zuwa ga fannonin da take da yaƙinin sune zasu riƙe manyan muƙamai a cikin Empire da Audu yake ginawa ta kuma cigaba da cusa masa su, ya zamana duk abinda zeyi ko kuma duk inda zashi tare dasu ne su su ukun nan Manyan su duniya ta sani a matsayin Magadan AUDU BECHI domin tun kafin Zakariyya ya gama makaranta Audu yake turashi ya wakilceshi a tarurrukan kuma a duk inda yaje ya kan gabatar da kansa ne a matsayin Babban Ɗan Audu Bechi, Yakubu yayi iyakar yinsa gurin ganin Audu ya daidaita amma abin yaci tura dole ya saki ya kuma zubawa sarautar Allah idanu domin a yanzun karan Audun ya aki tsaiko, ya isa, sunansa ya fantsama ya zaga ko ina Burinsa na zamowa ɗaya daga cikin mutanen da duk idan aka ambaci sunansu a faɗin Najeriya babbba da Yaro Mace da Namiji ya sanshi Allah ya cika masa wannan buri nasa.

Ga dai zuri'a ta taru amma babu hadin kai, babu shaƙuwa babu jan juna a jiki balle jinƙai a tsakani kowa ya tashi ta kansa kawai yakeyi a gidan. Wadanda babu iyayensu sun girma cikin wani yanayi sannnan sun samu labarurruka na gaskiya dana ƙarya akan yanda zamantakewar Audun da kasancw da iyayensu, ita kanta Aisha da yanzu akw kira da Momy ba dadin zaman takeji ba.

Itama ta tafka kuskuren da se a yanzu ta gano qautar da tayi, tayi saken da yaranta suka tashi akan tarbiyyar sauran yaran gidan, babu jitiwa a tsakaninsu kowa sabgar gabansa kawai yakeyi wata irin bahaguwar rayuwa tamkar a garin gwarawa haka ake a gidan Audu babu babba babu ƙarami kowa Tantirin kansa ne, tsakaninta da Binta har yau dai se a hankali dukda dai shekaru sunja kuma Bintan ta watsar da harkar kishi domin ta harba musu makamin da yayi musu illah sama da Hayaniyar zaman kishi, ta tarwatsa musu gida ta cusa muguqar Aƙidar yan ubanci a zuciyoyin Yaran gidan koda yake baza'a kira abinda sukeyi da yan ubanci ba domin ciki dayan ma kowa tasa ta fishsheshi akeyi sedai idan sabga ta haɗo tsakanin ɗan wani ɗaki da wani ba sannan ne sukan nuna haɗin kai kowa ya goyi bayan ɗan uwansa har kuwa Yayan Bintan dan abin yafi muni ma a tsakaninsu son kai da kyashi yayi tasiri a zukatansu.

Ahmad da Jafar su kadai suka fita daban. Su biyun sun zama tamkar zakka a cikin Ahalin Audu, halaye da ɗabi'unsu sun fita daban dana sauran. Allah ya haɗa jininsu suna bala'in ƙaunar junanau yanda suke mu'amala ba zaka taɓa ɗauka ba uwa daya ta haifesu ba, Binta tayi masifar tayi Bala'in har Malamai ta shiga akan ta raba Jafar da Ahmad amma abu yaci tura, Jafar din duk cikin yaranta tafi jinsa a cikin zuciyarta, tana da burika masu yawa akansa sedai tun fara tasowarsa ta fuskanci kwata kwata Alƙiblarsa daban da tata yanda kasan an canza mata shi a Asibiti idan badan kamanni da yakeyi da ita ba tsaf zata ce ba ɗanta bane.

Duk abinda Jafar zeyi seya shawarci Ahamd haka shima Ahmad ɗin, makwancinsu daya, a makaranta ajinsu daya hatta da kayan sawarsu basu banbantawa guri daya suke ajiyesu. Data rasa yanda zatayi domin tana so taja Jafar ta fara kitsa masa abubuwan da take so ya cimma tun da shekarun ƙuruciya amma abu yaci tura, Turai ce ta bata shawarar ta tura Jafar Makarantar kwana tunda Aisha bata ao bata taɓa tura Yaranta ba tasan bazata bar Ahmad yaje ba a haka zata janye Jafar sedai a banza domin tana tayar da maganar bata ma san anyi ba seda ranar tafiya tazo taga Ahmad ya shirya shima babu yanda ta iya ta barsu suka tafi akan zata sake shiri.

Daga sama Allah ya aiko mata da mafita, Jafar yana son kwallo tamkar ransa wanda ita kuma bata so domin tana gabin Kwallon na ɗauke masa hankali ta hanashi karatu Rana tsaka Babban Yayansu ya kirata akam ya samarwa Jafar gurbin karatu a Acadami ta Ƙungiyar Manchester dake Ƙasar Ingila ta sanarwa da Audu idan ya yarda a fara shiri. Da fari taƙi, tana gani za'a cuceta a cutar mata Ɗa ita da take da buri akansa acw ya tafi wata makarantar Ball, amma da Yayanta ya kwatanta mata irin Kuɗin da yan kwallo suke samu take ta amince ta kumayi murna ko banza ta samu hanyar raba Jafar da Ahmad.

Wannan tafiya ita ta raba Ahmad da Jafar, Ahmad baya bal Jafar kuma baze iya barin burinsa ba dukda a farko yaso yayi tirjiya akan baze tafi na se sun kammala sakandire idan Yaso Yaya Ahmad kamar yanda yake kiransa ya nemi Jami'a a can su tafi tare amma Ahmad ɗin ya ƙarfafa masa guiwa akan ya tafi basu rabu ba suna tare, hakan ko akayi shekarunsu goma sha uku a lokacin Jafar ya koma Ingila tareda kawunsa ya zama se Ahmad kadai a Najeriya, burin Binta ya cika na rabasu saura kuma na aiwatar da shirinta akan Jafar din domin ba wai kwallon ta kwanta mata bane har a rai Madarar kudin da Yayanta yace mata ana samu ne yasa harta yarda ta barshi ya tafin.

Rayuwa taci gaba da gurgurawa abubuwa da yawa sun faru na dadi da akasin haka, anyi rashe rashe yan uwan Audu gaba daya sun kwanta dama ya rage dashi da Yakubu se Bilki data dade da dawowa gidansa da zama tunda suka bar Goron Dutse suka koma Hotoro GRA inda ya tamfatsa gida Gari guda me sassa babu Adadi lokacin ne kuma ya ƙara aure ya auri Rabi'atu yar Malam Haladu Shugaban Maroƙa na wannan shiyya. Malam Haladun shiya tallatawa Ausu auran yarsa a lokacin Audun nada niyyar neman Aure domin yana ganin yaci ace ya ƙara mata dukda ya auri wata Fa'iza a can yawon Ƙasashen duniya suka haɗu da ita amma bata kai ga tarewa ba auran ya watse dalili yace sedai tazo gidansa ta zauna ita kuma tana ganin da uwar kuɗinta da gidanta sedai ya bita har an daura da taƙi tarewa ya sallameta iyalansa basu sani bama se bayan da auran ya mutu wannan tasa ganin Rabi'a tayi daidai da tsarinsa kuma yayi tambaya gun Malaminsa domin tuni shima ya zama dan hannu a sabgar Malamai baya abu da ka kamar yanda suke faɗi aka tabbatar masa Rabi'ar hadinsu yayi daidai shikenan ya Angwance abinsa.

Shekararta goma sha biyar kenan, da ace tana da zuciya koda yake acw iyayenta nada zuciya da tuni sun kashe Auran sun huta da gorin Binta. Bala'inta daya kwanta dama ta tattaro ta maido gaba daya ta ɗorawa Rabi'a, gorin safe daban na rana daban na dare daban yar matsiyata yar Maroƙa, tun ba data fara zuba Yaya tayi Namiji na fari daga nan hankalin Binta ya sake tashi, da tayi na biyu tagwaye mata se ta ɗan samu sassauci ana uku ma ta sakeyin Mace sannan ta dakata da haihuwar wannan yasa Binta data koma Hajiya a yanzu ta ɗan ɗaga mata ƙafa kadan daga kwarzabar da take mata ta sake mayar da hankali ga Audu da dukiyarsa da kuma yanda zasu gaje komai ita da Yaranta.
Chapter 85 · 0% Book details