← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 137

Sashe 3

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*NAGODE*

*FREE PAGE 2*

ABDULWAHAB TIJJANI Shine Asalin sunansa, AUDU da mutane da suka sanshi dashi yasa ake daukar cewa ABDULLAHI shine sunansa kamar yanda duk inda kaji Audu a gurin bahaushe tunanin na karkata da cewar Abdullahi ne sedai shi Alhaji Audu ya samu sunan ne ta dalilin wata kakarsu tun suna yara ya tashi da bala'in son kudi, da sallah idan ya samu yan silallarsa na barka da sallah ya ringa yawo dasu kenan a aljihu yana karkadawa suna qara idan ka tambayeshi menene se yace
"Kudina ne tara su zanyi se sunyi yawa sosai" shikenan take kiransa da Audu kudi tun befi shekara biyar a duniya ba kuma sunan ya bishi aka manta da Abdulwahab sedai Audun kawai har girmansa kuma wannan dalili ya saka koda Yaransa suka Shiga makaranta Malamai sukayi musu register da ABDULLAHI TIJJANI BECHI a cewarsu Audu ba suna bane.

Alhaji Audu haifaffen wani qauyene da ake kira Bechi cikin qaramar hukumar Kumbotson Jahar Kano. A yanda labari ya iske su kakansu daya haifi Mahaifinsu Tijjani wato Malam Lawan shine me garin Bechi na farko ance seda suka shekara Talatin da matarsa Asabe kafin Allah ya basu haihuwar Tijjani hakan yasa suka dauki son duniya suka dora masa sedai Allah beyi zasuyi doguwar rayuwa tare ba domin kuwa shekarun Tijjani bakwai a Duniya Mahaifinsa Malam Lawan Me gari ya rasu wata hudu tsakani ya rage kwanaki goma Goggo Asabe ta fita daga takabarsa itama ta amsa kiran Mahaliccinta shikenan Tijjani ya tashi maraya gaba da baya riqonsa ya koma tsakanin dangin Mahaifinsa yau yana wannan gida gobe yana na can wanda gaba dayansu sunayi ne saboda tarin dukiyar qasar da Mahaifinsa ya mutu ya bar masa ba kuma sun bari ya girma ya samu komai ba se wata gona kwalli daya wadda itama wani qanin mahaifiyarsa ne yayi tsayin daka gurin ganin bata salwantaba se fili wanda gidan da iyayensa suka zauna ya kamachi a bashi amma Sabon me garin da aka nada wanda yake qanin Mahaifinsa ya gaje ya shiga ya zauna a ciki dukda cewar gadon Tijjani ne, badan ma suna tsoron tijarar Kawun nasa ba shine dalilin daya saka ya bashi wani fili daban yace ya gina.

Da wannan gona daya tsira da ita yaci gaba da kula da rayuwarsa ita yake nomawa abinda ya samu ya siyar yayi buqatunsa har yayi aure ya auri Fadi yar Kawunsa yayan mahaifiyarsa haka suka zauna tsayin shekaru cikin rufin Asirin Allah har tayi yaya biyar Maza uku mata uku Lawan da suke kira Baba se Hashimu, Maryam, Amina, Aminu da kuma Zulai. Bayan Baba da Hashimu sun tasa su suka cigaba da taimaka masa da gonar da ita kadai ce hanyar samunsu, abinda suka noma a ciki zaau cire abinci, ragowar a siyar a ringa buqatun yau da kullum wannan dalili ya saka rani damina koda yaushe cikin shuka yake musamman da Allah ya taimakeshi gonar tasa tana kusa da wata fadama dan haka bashida matsalar ruwa sabodan noman rani sannan tana da girma babu laifi shiyasa yake noma nau'ikan abici kala kala.

Suna zaune lafiya da Fadi lokaci daya ya bijiro da zancen son qarin aure bayan daya hadu da Hafsatu Farar bafillatana baquwa da sukazo qauyensu kawo Amarya Tijjani na ganinta yace tayi masa, be samu matsala da Fadi ba, inda ma yar tangardar take be wuce damuwar yanda al'amura zasu kaya musu ba idan ya qaro auran dalili da cewar lallaba rayuwa sukeyi ba shida wata hanyar samun kudi idan ba noman nan da yakeyi ba dukda rayuwa nada sauqi a wancan lokacin amma nauyi ze qarar masa idan yayi auran, rarar da suke samu ta amfani gona har a siyar bw zama lallai aci gaba da samu ba tunda wacce ze auro din itama haihuqa zatayi wata rana wannan Fadi taso ta fahimtar dashi amma ya nuna komai na Allah ne shi yake ciyarwa kuma yanda ya nufeshi da qarin auran ze hore masa abinda ze cigaba da kulawa dasu haka kuwa akayi ya auro Hafsatu zaman au gwanin dadi da Fadi tana bata girma sosai a matsayinta na wadda ta girmeta kuma tana sama da ita a gidan aure wannan ladabi nata yake qarawa Malam Tijjani sonta.
Shekara daya ta haifi Da Namiji aka saka masa Yakubu, shekarar biyu ta haifi Audu se Bilkisu, Aisha da kuma Muktar me sunan Babanta suna ce masa Baballiya.

Rayuwa ta qarayiwa Malam Tijjani da iyalan sa tsanani saboda sun qara yawa kuma madogarar tasu dai guda daya ce wannan gona, qari da haka hatta da Maryo da Amina yayan Goggo Fadi da aka aurar mazajensu duk suma ba masu qarfi bane se ya zama har dasu ake noma gonar Malam Tijjanin abinda aka fitar a raba kowa yaje yayi ta jalautawa da iyalansa wannan matsatsin rayuwa ya saka Audu tashi da burin son yayi kudi saboda Baffansa ya huta da wahala. A lokacin farko shigowar Boko Yaro dayane a garin yake karatun Bokon Shamsu wanda yake dan Me gari shima ya kaishi cikin Kano ne yana zaune gidan wani Hakimi se shekara shekara yake zuwa gidan. Sa'an Yakubu ne amma duka Abokanai suke dasu Audu tunda tazarar shekarun ba yawa kuma tare suke karatun Allo kafin aka kaishi birni idan Shamsu yazo kuma zeyita bawa su Audu labarin Birni da Turawan da suke koya musu karatu har yace suyiwa Baffansu magana suma akai su dan Malamansu sun gaya musu idan suka dage sukayi karatu zasu samu aiki a ringa biyansu Albashi wadanda suka iya turanci kuma har Ingila zasu tafi dasu.

Zancen kudi da Audu yaji yasa hankalinsa ya tashi ya kuma quduri niyyar zuwa Birni Yakubu kuwa da tun qaraminsa ya tashi da Burin Zama Alqali, ko wasa akeyi zece shine Alqali ayita zuwa gabansa ana kawo shari'a shima Shamsu yace masa a birni da akwai Kotu ba irin yanda ake shari'a anan ba sedai aje gaban me gari. Audu yacewa Yakubu suyiwa Baffansu maganar zuwa Boko amma se yace Aa dan shi yana da sanyi ba kamar Audun ba yana gudun yiwa Baffan magana yayi masa fada dan lokacin da aka kai Shamsu be manta ba harda Baffansu a masu cewa an kaishi ze koyo yahudanci Audu beyi qasa a guiwa ba ya samu Mahaifiyarsu da suke cewa Dada da zancen tayiwa Baffa magana ya samu me gari idan Shamsu ze koma birni su bishi take kuwa ta nuna rashin amincrwa itama dai kamar Yakubu ta tuna masa da Mahaifinsa na Adawa da Karatun Boko da ya shigo daga nan aka bar maganar badan har zuciya Audu ya haqura ba sedai yayi shiru ne kawai zuwa wani lokaci saboda tunda yaji zancen kudi fa hankalinsa yayi kan Birni kuma kota halin qaqa dai se yaje shi.

Seda aka shekara kafin dama ta sake zuwar wa Audu a wannan Karon a gurin Malamin da yake musu karatun yaji cewar ze kai Yara Birni can tsangayar Malaminsa Gwani Musa a unguwar Kabara. Audu najin wannan batu yana komawa gida ya sanarwa da Dada a wannan karon itama bata ce Aa ba tasan kuma shima mahaifinsu baze hana ba inda zaa iya samun matsala be wuci yanzu da suka tasa ba suna taya sauran yan uwansu aikin Gona amma tasan hakan baze zama wani abu ba. Haka kuwa akayi ta damu Malam Tijjani da batun yayi na'am har yace ze samu Malam Tsalha malamin tsangayar tasu yaji kanun maganar, bayan duk shirye shiryen da suka kamata Audu da Yakubu suka bi tawagar Yaran Gari zuwa birni Almajiranci, dukda Malam Tijjani yaso iya Audu ya tafi Yakubu ya tsaya amma Audu ya kafe kaida fata se sun tafi tare saboda shirinsu na karatun Boko wanda Yakubu ya fishi buri akan abu shi neman kudi kawai yake so yaje yayi a Birni ba wani Karatun Allo kona boko ba.

Seda suka shafe wata uku a tsangayar Gwani Musa suna kuma karantar birnin na Kano, basu san inda zasu nemi Shamsu ba balle ya kaisu makarantarsu, Audu a shige shigensa yayi Abokanai anan cikin Magashi suka shaqu da wani Yaro Sa'an sa Hayatu yaron gidan da Audu yake yiwa aikace aikace ne. Hayatu da sauran yan uwansa suna makarantar boko dan haka Audu ya nuna masa shida dan uwansa Yakubu suna sha'awar karatu kuma abinda ya fito dasu daga qauye kenan. Hayatu ya sanarwa da Mahaifinsa wanda a lokacin suna cikin mutanen da suka karbi Boko sosai yaji dadi kwarai da wannan abu dan haka ba tareda bata lokaci ba yaje da kansa ya samu Gwani Musa ya sanar masa da buqatar su Audu tayin karatun Boko. Da yake Malami ne me fahimta kuma shi kansa cikin yayansa akwai wadanda suke Bokon saboda yanda Sarakuna da masu kudi da suke samun damar fita Waje suke fada musu Alfanun Bokon be hanasu Audu ba, ya kafa musu sharadi dai na dole zasu cigaba da daukar Karatu, da safe suje bokonsu su dawo Yamma da dare su zauna a makaranta suyi karatun Qur'ani haka kuwa akayi su Audu suka fara zuwa makaranta shekara daya da haka yace shi ya gaji saboda Shamsu ce masa yayi idan anyi karatu za'a samu aiki a samu kudi shi kuwa kullum karatu ake dora musu bema ji ranar da za'a gama ba dan shekaru ake lissafowa Yakubu ne yayi ta tausarsa akan yayi haquri da sannu zasu kai matakin da suke buri.
Chapter 3 · 0% Book details