← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 137

Sashe 18

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana kwance tana bacci hankalinta kwance ya kai hannu ze tayar da ita Audu ya riqeshi yana cewa
"Haba dai ya zaka tayar da ita tana bacci"
"Na kasa nutsuwa saboda ita na baro Ikko babu shiri me ya samu Dada kullum cikin tunaninta nak abin kuma har ya zarce misali?" Yakubun ya fada yana duban Audu, Audu yayi waje yana cewa
"Babu abinda ya sameta kaje ka kwanta kaga dare yayi da safe se muyi magana" suka wuce, seda yayita kwankwasa qofar barinsu kafin Balaraba ta taso a dan rikice da alama tana baccin itama bugun ya riske ta, ganin Yakubu ne kuma se fuskarta ta washe da murna suka shiga suka maido qofa se sannan Audu ya shiga dakinsu zuciyarsa fal da wasi wasin abinda ya taso Yakubun haka koda yake ya sani shidin me qulafucin uwa ne ta yuwu rashin lafiyar Dadan ce ta taba shi har ya kasa zama ya taho ya ganta haka ya ringa juyi a gado sedai sam bacci ya qauracewa idonsa dan haka ya tashi ya dauro Alwala ya shiga Nafila Bara'atu dai tayi daidai abinta a gado dan cikin nata irin me baccin nan ne da se a iya sace mutum sedai ya farka ya ganshi a wata Nahiyar.

Asubar Fari kururuwar Baballiya ce ta saka Audu sallame sallar da yakeyi babu shiri ya fita daga daki da gudu, a bakin qofa sukayi kicibus da Yakubu da shima ya fito a rikice dan da gani ma daga wanka ya fito ya saka dogon wando ga rigarsa nan a hannu ko sanyin da ake busawa ma bayaji suka shiga turereniyar shiga dakin Dada inda Baballiyar yake qarawa Ihunsa qaimi matan kuma da duk suka fito suma harda Goggo Fadi sun tsaya daga waje kowanne abinda zuciyarsa ta bashi wuta ce tunda lokacin sanyi ana yawan samun wannan matsalar saboda Rushi da ake kaiwa daki dan aji dumi idan yazo da tsautsayi abinda ze iya kama wuta ya shiga ciki se kaga gobara ta tashi amma kuma basu hango jan wuta a cikin dakin ba ko kuma hayaqi to ko wani mugun kwaron ne ya cije shi?

Yakubu ne akan gaba, burki yaci yana kallon Dada dake kwance idanuwanta a bude tana kallon rufin dakin hannunta daya na dafe da qirjinta dayan kuma ya saki ya sakko qasa, dukda cewar gawa daya ya taba gani ido muraran wato ta Malam amma baya buqatar a gaya masa cewar Dadan ta rasu. Lokaci daya wani kuka me cike da rauni ya kufce masa, ya durqushe gaban gadon Audu ya tsallake shi ya qarasa shigewa dakin dan be fahimci dalilin tsayuwar Yakubun ba ga Baballiya dabe fasa ihu yana kiran ya shiga uku ba.

Hannun Dadan dake qasa ya daga ya maida kan gadon, sanyi qalau yaji shi, ya shiga jijjigata yana kallon fuskarta tareda kiran sunanta ganin ta zubawa guri daya ido Yakubu dake kuka kamar qaramin yaro, ashe Alhinin rasa mahaifiya ne ya hanashi sakat har seda ya kamo hanya ya dawo sedai an saba haduwar, bashida rabon zasu sake zantawa da ita rai yayi halinsa. Kama hannun Audu dake jijjiga Dadan yayi cikin kuka yace masa
"Bari jijjigata ta rigamu gidan gaskiya"
Ze iya cewa be fahimci abinda Yakubu yake nufi ba dan kwakwalwarsa gaza fassara hausar tayi dan haka ya shiga qoqarin dagata yana cewa Yakubun ya tayashi su fita da ita ya kaita Asibiti Yakubu ya miqe yana janye shi cikin daga sauti yace masa

"Ka dena wahalar da ita Audu na gaya maka ta rasu" kalaman da suka fi duk wasu kalamai daya tabaji a rayuwarsa Muni, Dada ta rasu? Dadar da suka gama hira dazu daman duk wasiyya take masa?
Kalaman Yakubu suka janyo hankalin su Goggo Fadi dake qofar daki take suka fasa kuka kafin kace me maqota sun jiyo aka fara shigowa rayuwa kenan tabbas dan Adam abin tausayi ne yanzun kaine qiftawar ido ana iya cewa babu kai. Duk wanda yaji rasuwar Dadan se yace jiya fa da La'asar sakaliya ya ganta a Mashin Audu ya dauke ta har sun gaisa, a masallaci ana idar da sallah aka bada sanarwar Jana'izar, kafin ko gari ya gama wayewa tangararau har an shiryata tsakanin Yayanta baka iya fidda wanda mutuwar tafi duka. Bilki suma tayi sanda saqon ya risketa Aisha tafita dauriya kuka ta ringayi Audu kansa duk taurin rai irin nasa ya koka hada kai sukayi da Yakubu suka ringa kuka gwanin tausayi.

Bayan an kaita an dawo aka zauna zaman karbar gaisuwa, Goggo Fadi tayi wata zugewa lokaci daya, mutuwar Dadan ta daketa matuwa ta kuma yi nasarar maidata cikin hayyacinta.
"Malam beyi sauri ba, nima zan bishi kuma kema kina tafe komai daren dadewa" kalaman Hafsatun na jiya suka ringa mata yawo a kwakwalwa ashe mutuwa Hafsatu zatayi? Da tasan haka da bata takaleta ba, data nemi yafiyarta akan abubuwan da ita da yayanta suka ringayi mata. Hashimu kansa yaji mutuwar amma da yake Dan Adam ne ana kwana daya ya ci gaba da sabgoginsa be ko sake zama gurin karbar gaisuwar ba ya bar su Audu dasu Aminu da idan ka ganshi zaka dauka mahaifiyarsa ce ta rasu. Su Audu kuwa ba'a magana duk sun sukurkuce bayasu ba baya matansu ba amma ya zasuyi haka aka share zama bayan anyi bakwai Abokanan Audu na Kano sunyi masa kara mota guda suka yi sukaje masa gaisuwa bayan da suka samu labarin rasuwar a bakin masu daukar kaya yan garinsu.

Wannan karon tsakanin Audu da Yakubu rasa wanda ze lallashi wani ya koma bakin nemansa akayi. Seda Dada tayi sati biyar da rasuwa, Yaya Baba ya kirasu cike da Alhini bayan ya sakeyi musu gaisuwar rashin da sukayi kafin yace musu
"Naga dukkanku baku da alamar komawa bakin neman ku musamman kai Yakubu da kuke tsaka da Karatu ka taho ya kamata kuyi haquri ku dauki dangana zamanku bashi ze maido da Goggo ba A yanzu Addu'a kadai take da buqata daga gareku sannan kuci gaba da jajircewa akan abinda take da burin ganin kun cimmasa".

Maganar Yaya Baba tasa suka fara shiri jiki a sabule babu wani karsashi sun kasa sabawa da Rashin Dada, tunanin yanda rayuwarsu zata cigaba ba tareda ita ba sukeyi yanzu dawa zasu ringa barin matansu? Tunanin Audu kenan. Da dare ya samu Yakubu a bangarensu yana zaune shiru Balaraba na gefensa itama shiru duk ta fice hayyacinta tamkar Bara'atun sa ga tsohon ciki haihuwa ko wanne lokaci na iya zuwa shigowar Audun yasa ta cicciba ta basu guri.

"Wata shawara nake da ita Yakubu" Audu ya fada bayan daya gyara zamansa. Yakubu ya kalle shi Audu yaci gaba da cewa
"Daman akan Iyalanmu ne, kaga yanzu Babu Dada gaskiya hankalina baze taba kwanciya ace mu barsu a nan ba kaga dai halin da gidan nan yake ciki lokacin da ranta ma yaya balle yanzu da babu idonta"

Yakubu ya jijjiga kai yace
"Hakane, ni kaina ina wannan tunanin ga yanayin da suke ciki gaba daya kowacce na da buqatar kulawa ta musamman, amma kai menene shawararka me kake gani za'ayi?"

"Dama dai tun zuwansu Ma'aruf na gaya mishi ya dauki kudi cikin cinikin da akayi a qarasa ayyukan da suka rage na gidan nan mu koma can kawai gaba daya da zama kaga hankalina zefi kwanciya na kuma tsaya a guri guda amma kai me kake gani?" Audu ya fada. Yakubu ya muskuta yana cewa
"To wannan shawara ce amma kana nufin kenan zamu bar Bechi da zama gaba daya?"

"To me muke dashi a nan da ze sa muci gaba da zama? Karka manta mun rasa uwa da uba dangi kadai suka rage mana kuma zamu ringa kawo musu ziyara lokaci lokaci musamman kaga Bara'atu iyayenta suna nan baze dauki lokaci me tsayi ba zamu ringa leqowa muna ganin dangin mu" Audu ya sake fada.

"To gida kuma fa haka zamu barshi ya lalace?" Yakubun ya sake fadaz cike da qosawa Audu yace
"Nidai na rigada na yanke shawara bazan iya cigaba da zama a gidan nan ba idan na kalli dakin Dada gani nake kamar zata fito daga ciki zuciyata bazata iya ci gaba da dauka ba" yayi maganar a raunane sukayi shiru baki daya kafin can Yakubun ya sake cewa

"Ina ganin zan kama daki a Ikko da zamu iya zama da Balaraba zuwa na qarasa karatuna kafin muga abinda Allah zeyi"

"Wannan shawara ce me kyau, amma kuma a halin da take ciki baze yuwu ka dauketa ba dole sedai a jira har seta haihu kuma kaga lokaci yana qara tafiya kamata yayi ka fara yin gaba kaje ka shirya duk abinda ya kamata idan ta sauka ta yada wanka se kazo ka dauke ta ku tafi ko ba haka ba?" Shawarar Audu.

Yakubu yayi na'am da maganar tasa dan haka suka shiga shiri, sun sanar da matayensu abinda ake ciki haka yan uwansu da suke uba daya, Goggo Fadi ta fasa musu kuka sanda suka gaya mata shirin nasu tana cewa wai me yasa zasu ce zasu bar gidan kenan ita basu dauketa uwa ba ba zata iya kula musu da matansu ba? Daga Yakubun har Audu babu wanda ya kula maganganunta dan gani sukeyi ihu ne kawai bayan hari basu yarda wai har zuciya Goggo Fadin tayi tuba na gaske ba. A satin suka shirya tafi, sun tsara da gida ya kammala Audu ze kwashi Bara'atu da Balaraba duk su koma Kano da zarar Balaraban ta haihu kuma zata koma Wailari tayi wanka inda daga can zata bi Audu, da akwai Yayanta da yake zama a Ikkon shima Shanu yake kaiwa daga baya kuma yayi zamansa can matansa biyu ya kai daya can sunzo ganin gida zasu jima dan haka suka bari akana idan Yaya Iron ya tashi komawa zata bisu su tafi tare.
Chapter 18 · 0% Book details