← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 137

Sashe 47

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ce mata yayi ta maimaita duk abinda ta fada cewar Audu ya mata, tana kuka ta shiga shiryosu harma da abinda dazun bata fada ba na cewar daman Audun ya dade yana yawon ta zubar dinsa har kwanaki yake tafiya yayi acan in ya dawo kuma tayi magana ya zageta koya hada mata da duka qarshema tace idan ta fita har gidan yake kawo mata shidai kasa cewa komai yayi saboda mamaki, maganganunta kuma babu yanda za'ayi ace qarya takeyi tunda tabbas yana yawace yawaceb har yaje ya kwanan amma ai ba abinda take fada yakeyi ba sedai kuma waye ze bada shaidar hakan?

Shidai Alhaji na jinta yana kuma kallon Audu daya kasa rufe bakinsa seda tayi shiru kafin ya kalleta yace

"Kinaji ko Mamana, duk wani Aure da kika gani tattare yake da qalubale muddin kuma ba ma'aurata sun bude cikinsu ba bazaka taba sani ba dan haka kowa haquri yakeyi kamar yanda kika faro haqurin kici gaba dayi kuma tunda ya auro yarinyar da take dauke masa hankali a wajen ai magana ta qare se ayi fatan kuma Allah ya hada kanku ya bada zaman lafiya. Kaikuma abinda nake so na gaya maka shine ka tabbatar kayi na farko kuma kayi na qarshe da zaka dora hannu da sunan duka a jikin Mamana, zan manta da duk wata alaqa dake tsakaninmu na maka ka a Kotu domin bana hada kowa da yayana, ban daki yar kowa ba dan haka babu hujjar da zata saka wani ya dakar mun yata. Idan tayi maka laifin da ba zau iya sasantawa a tsakaninku ba ka kawo mun qararta nizan hukuntata amma bazan lamunchi duka ba ina fatan ka gane?"

Kunya, nauyi da takaici suka rufe Audu gaba daya ya rasa ma abinda zeyi, Alhaji yaci gaba da cewa
"Idan Allah ya kaimu gobe yanda kikazo da sassafen nan ki tattara ku koma aje aci gaba da haquri kuma na kashe maganar nan, Aure kuma dakayi Allah ya sanya Alkhairi ya baka ladan Jihadi"

"Wlh bazan koma ba, babu yanda za'ayi nayi zamab kishi da Karuwa Dady kawai kace masa ya saketa idan ba haka ba bazan koma gidan ba" ta fada cikin kuka tana bubbuga qafa.

https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 18*

Ki bude kunnenki dakyau kiji abinda zan fada, dukiya da kike tutiya akanta ta Abdullahi ce, duk abinda nayi masa kyautace halak malak dan haka ko ki bishi ki koma, ko ki dage ya sake ki zabi ya rage naki amma ki sani sisin kwabo baze maidamun ba dan ya rabu dake ko wani abu saboda dama badan ya aureki na bashi ba, tashi ki bani guri karki qara mun ciwon kan da yake damuna" Alhaji ya dakatar da Binta dake ihun kuka.

Sanin halin mahaifin nata kaifi dayane yasa ta tashi ta koma ciki tana cigaba da kukan ta labartawa Mama yanda sukayi.
"Ahto seki shirya ki koma daman duk tsuntsun daya ja ruwa ai shi ruwa ze doka, ke kika zabe shi dan haka dole ki jure duk wasu tazgado dake tareda zama dashi kishiya kuma naga wata kika tarar kowa da halinta zata zauna ai ba kuma kanki ze ajiyeta ba" abinda Mama ta sake gaya mata kenan haka tana ji tana gani suka kama hanya da farar Asuba ba tareda ta hadu da sauran yan uwanta ba wadanda su ta saka ran zasu bata shawarar yanda zata yida wannan Al'amari, da Munira suka sake tattaunawa da dare ta qara masa karatun yanda zatayi ta hana Amaryar shigo mata gida dan basu hasko ma ta shigo balle ta zauna.

Haka suka sha tafiyar bata ko kula Audu sedai shine yake tankata lokaci lokaci daya gaji da yanda ta shareshi yayi shiru har sukazo Kano, yana Ajiyeta ya fita itama bata zauna ba jakarta kadai ta shigar daki ta fice gidan Turai.
"Wlh Turai ko a jikinsu, babu fa wanda ya daga maganar Asalin matar daya aura din kamar ma basu fahimta ba haka suka share zancen har a gabansa Dady yana wani jaddadamun duk kudin daya bashi ba Aro bane kyautace kuma ba saboda ni ya masa ba, wlh da na shirya rabuwa dashi amma wannan dalilin yasa na fasa. Babu yar iskar dazan tafi na barwa gida tazo ta wataya da kudin ubana".

Duk da yanayin jimamin da suke ciki seda Turai tayi dariyar maganar Bintan ta kuwa sake harzuqa tace
"Au ga mahaukaciya ko ina magana dariya ma kike mun"
"Ba haka bane, ke dince da abin dariya waini in tambayeki Binta tsakaninki da Allah Audu kike so ko kuma Dukiyarsa?" Turai ta fada tana kallonta.

Ta zabga tsaki kafin tace
"Duka gaba daya, kinga Audu yayi mun daidai da tsarin Mijin da nake burin na Aura cikas dinsa daya rashin wayewar Boko amma abinda yaja hankalina harna yarda na Aureshi saboda yanda Dady ya ke labarinsa na san gobensa zatayi kyau zeyi Arziqi. Turai ina son kudi ina so kuma na auri me Kudi, dukda nayi samari masu kudi yayan masu kudi abinda yasa na zabi Audu a cikinsu saboda shi be waye ba, zan iya masa wayo na samu abinda nake da buqata a gurinsa sannan na hana kowa rabar sa ya zamani ni kadai zan moreshi se yayana, ba qaramin takaici naji ba dana samu labarin yana da mata harda yaya kuma tun sannan na daura Aniyar seta fita ta barmun gidan, bayan nayi nasara sannan ga Arziqi nan yana qara habaka se kuma na bari wata tazo ta tayani ci? Wlh baze yuwu ba dole koda tsiya koda Arziqi matar nan ta koma inda ta fito babu yanda za'ayi na zauna da kishiya a gidan Audu".

"Yanzu dai plan A ya ruguje se mu tafi ga shiri na biyu, kuma ina so ki kwantar da hankalinki qawata shi yaqi akace fan zambo ne, yanda kikayi da Bara'atu haka zakiyi da wannan ma koda ace ta shigo cikin gidan, yanzu abinda zakiyi, lambo lambo zaki masa ki nuna masa kinyi nadamar abinda kikayi ki bashi haquri kisan duk yanda zakiyi yabyarda dake ta haka ne zaki yi komai ba tareda ya zargeki ba, kamar dai lokacin Bara'atu ai kinga kin nuna masa kina sonta harta fita be taba sanin irin gallazawar da kika ringa mata ba" Turai ta fada

"Turai! Wannan fa ba Bara'atu bace, kefa kika ce mun kilaki ce ta ina zan iya goga kishi da yar Bariki Turai?" Bintan ta fada cikin yanayin dake nuna tabbas ta tsorata da Amaryar da Audun yayiwo mata. Turai tayi murmushi tace
"Dadi na dake Damusar takardace, ga tsoro ga ban tsoro, yanzu har akawai wata kisisina da matar bariki ta iya waddda mu bamu iyata ba? Meye a cikin barikin ne da har zata naki tsoro? Kinga fa yaqin nan dole se kin dage idan ba haka ba kina zaune zata shigo kuma ta kwace Mijin"

"Allah ya rufa asiri, wlh ko zan mutu bazan bari naga wannan rana ba" Binta ta fada tana fashewa da kuka Turai tayi dariya tace
"Bama zaki mutu ba sedai ita me shirin yi mana kutse ta mutu, yanzu dai kamar yanda na gaya miki kije ki lallabashi ku daidaita, da an kwana biyu kic zaki Bechi ki gaishe su a can zaki kwarkwance komai ki gaya musu wacece ita son samu ki fara sanar da Yayansa na Lagos nasan ko beji maganar na qauyen ba shi baze qijin ta tasa ba" da wannan shawara suka rufe ta koma gida ta yi matuqar qoqarin danne zuciya tayi duk abinda Turai tace.

Kuka wiwi ta ringayi tana bashi haquri da rantsuwar ba zata sake ba yanzun ma sharrin shaidan ne tayi iyayinta har seda ya sakko shima ya bata haqurin yanda Al'amuran suka kasance a qaryarsa wai besan za'ayi haka ba.
"Amma banji dadin yanda kika kwanceni a gaban Dady ba, na dauka ko abinda kika fada gaskiya ne ke me rufamun Asirice a ko ina" ya fada in relevant to zancen yawonsa data gayawa Dady. Kanta na qasa tana share hawayen kissa tace

"Kayi haquri, wlh bansan abinda ya shiga kaina ba kan yafemun Mijina kaji dan Allah"

"Ya wuce, Allah ya yafe mana gaba daya sannan in Allah ya yarda nan da kwana Goma Zata tare, ina so ki lissafa duk abinda kike da buqata da wanda za'ayi amfanin yinin Biki a can Bechi"

Wani abu ya caki ranta amma ta shanye tace
"Shikenan zan lissafa, yaushe zamu tafi Beechin toh?"

Da mamaki ya kalleta jin yau anyi zancen zuwa Bechi salin Alin ba ta fadi mara dadi ba, ransa ya qarayin fari yana qara gasgata da gaske tayi nadama dan haka yace mata se saura kwana uku zasu tafi da anyi yini yau washe gari au dawo gaba daya da Amarya ta amsa da Allah ya nuna mana a Ranta tana ayyana Bura'ubar da zata tafka a Bechi idan sunje.

Haka ko akayi, tana kallo aka ringa fenti aka shigo da sababbin kayan gado da kujeru aka saka a tsohon dakin Bara'atu baqin ciki kamar ya murqusheta ta mutu wato cikin dukiyarsu yayiwa Tsinanniyar Amaryar kayan daki, takaicin kanta ya sake rufeta datayi wautar cewa ya barshi bata buqatar komai duk a salon wanke kanta gurinsa. Ranar Laraba suka tafi Bechi ita da Direba daya hadata dashi tareda kayayyakin amfanin girkin da ba za'a samu a can ba, Juma'a za'a kai Amarya can ayi yini su Kwana Asabar su juyo.
Chapter 47 · 0% Book details