← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 137

Sashe 77

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AUDU
Tattara yaran yayi ya maidasu Bechi bayan da Binta ta bar gidan harda Zakariyya da bata tafi dashi ba, rayuwa ta masa quncin da be taba zaton ze tsince kansa a makamancinsa ba, komai ya sukurkuce masa, duk ya gigice ya fita a hayyacinsa shi kadai yake rayuwa a gidan abinci sedai ya siya ko yaje gidajen Abokanansa yaci. Be bi takan Binta ba balle yasan me take ciki dukda har yanzun be yanke hukunce dangane da cigaban zama da ita ba ko akasin haka cikin wannan yanayi ya share watanni biyu, Yakubu yazo Kano ya tarar dashi gashi nan shi ba me hankali ba shi ba zararre ba, dukda cewar yana da fushinsa a zuciya amma akace Jini ba wasa ba ya tausayawa Audun.

Shi ya ringa tausarsa ya nuna masa cewar kuskure dai ya rigada ya aikata a rayuwarsa yanzu abinda ya rage masa shine ya gyara sannan rabuwa sa Binta ba shine mafita ba a yanzu tunda dai ya fahimci wacece ita ya kuma san tuggu da makircin da take shirya masa a gida seya hankalta ya kuma san me yakeyi, sannan ya bashi shawara da ya hade kan gidansa, yaje ya maido da Zubaida ta raini Yayanta a gidan ubansu yasan kuma ita zata iya riqe Marayun Bara'atu ta hada da nata saboda zancen yace ze maidasu Bechi ma be taso ba ya kuma jaddada masa ya tashi ya koma makaranta ya nemi ilili na boko dana Muhammadiyya saboda Ilimi shine gishirin rayuwaz daga shi har Bintan Jahilci shine jigon abinda yake qara ingizasu ga shirmen da suke aikatawa a rayuwarsu.

Karo na farko da Yakubun ya dangantashi da Jahilci kuma ya amsa beji Haushi ba ya kuma tabbatar masa da ze bazama neman Ilimi ze kuma gyara mu'amalarsa, zancen Zubaida kuwa daman ya dade yana saqa hakan a zuciyarsa tun ma kafin Bara'atu ta sake fita daga gidansa dan haka ya roqr Yakubun dayayi masa Jagora suje dan yana kunyar Idon Mahaifinta ya sani be kyautawa Tsohon ba. Yakubu beqi ba suka shirya sukaje, ko a fuska Malam Hassan be nuna musu komai ba ya ringa Maraba dasu ga Yan Biyu sunyi girma sosai sunyi wayo idan ka gansu zaka dauka sun shekara uku ko sama kamanninsu daya sak sedai banbancin halayya inji Malam Hassan ya nuna Hussaini yana cewa

"Kaga wannan kaiya biyo sak, rigima a cikin Hussaini harda ta bayarwa sadaka shi kuwa takwarana yanda kasan wannan dan uwan naka salihin bawa babu ruwansa haka Tagwai din zeyita cin zalinsa yayi shiru na zakaji bakinsa ba". Audu ya sunkuyar da kai dan ji yayi kamar zaginsa Malam Hassan yake a fakaice Yakubu kuma yayi murmushi yana cewa
"Dama hakane ai duk tagwaye se an samu wannan banbancin dabi'ar daya me sanyi daya me zafi"

"Wannan gaskiya ne dan nima nawa Hussainin Allah ya jaddada rahma a gareshi haka muka sha fama tun quruciya har zuwa girma shekarun mu Arba'in da biyar Allah yayi masa rasuwa sedai shi be bar baya ba yaya hudu ya haifa duk kuma sun rigashi mutuwa" Inji Malam Hassan.
"Allah ya jaddada rahma a gareshi" Audu da Yakubu suka hada baki gurin fadi. Shiru sukayi nadan lokaci kafin Yakubu ya numfashi ya amayarwa da Malam Hassan abinda yake tafe dasu.

"Wai, ashe baka sani ba? Ai yau kwana Ashirin da tara kenan da Zubaida ta daura aure kwana goma sha biyu kuma da tarewarta, nan qasan mu babu nisa take Yaron Aminina Malam Bala ta Aura wannan da kuka taba gaisawa a nan har nake ce maka Daga qasar waje ya dawo yayo karatun Likitanci" Malam Hassan ya fada yana duban Audu Audun kuma ya kalli Yakubu kamar dashi ake maganar,

"Tooo ai babu labari Baba, da yake muma din an samu Rashi ne uwargidansa ce ta rasu a Makka sunje aikin Hajji ba'a dawo da ita ba wannan ya tayar masa da hankali har yasa ya dauki lokaci haka be leqo Yaran ba. Ashe kuma haka ubangiji ya qaddaro babu rabon komawarsu da itaz to masha Allahu munyi murna Allah ya sa hakan shine mafi Alkhairi a rayuwarsu baki daya" inji Yakubu.

*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*

*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓

*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*

*Muna da magunguna iri iri*

*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*

*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*

*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*

*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,

*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*

*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*

*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*

*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*

*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*

Haka suka tattara suka tashi guiwoyi a sage, har sun shiga Mota Audu ya kalleshi yace
"Mu koma mu tafi da yaran"
"Idan ka dakko su ina zaka kaisu? Ko kuwa kai zaka haqura da fita nema ka zauna rainon Yara? Koda zaka karbe su ba yanzu ba ka fara bari ka nutsu kasan alqiblar daka kama sannan se kayi batun dakko Yara, yanzu dai gashi yayanka shida Audu Aure uku, ina fatan ya zama na qarshe saboda Aure Aure bashi da dadi, sau da yawa yana kawo rarrabuwar kawuna Ahali musamman a gida irin naka da Shugaban gidan be zama tsayayye ba, kaje ka zauna kayi shawara ka yankewa kanka hukuncin abinda ya kamata kayi a yanzu, kaga dai Bara'atu ta tafi inda babu dawowa, Zubaida Tayi Aure nasan kuma sedai wata qaddara ta ubangiji ce zata fiddota daga gidan auranta Binta kadai ta rage maka uwar Yaya da kake da damar cigaba da zama da ita dan haka ka maidota ta riqe Yayanta kana iya nemo wata Macen daka yarda da tarbiyyarta da zata mayewa wadannan Iyayen da basu tare dasu domin na tabbatar Bintan dana sani bazata riqa maka Yaro ko guda daya tsakani da Allah ba.

BAYAN WATANNI UKU
Watanni uku suka shude wata biyar kenan tun bayan rasuwar Bara'atu da kuma barin Binta gidan Audu, be waiwayeta ba be kuma je Kadunan ba kamar yanda Suma Iyayenta basu nemi da yaje ba. Mahaifinta yace duk hukuncin da Audun ya yanke akanta dai dai ne kuma shi baze shiga cikin maganar su balle Alfarmarsa tasa ya yanke hukuncin da bashi yaso a zuciyarsa ba. Wannan zama ya quntata Binta matuqa da gaske, babu walwala ko Yancin da take dashi a baya ta zama kamar wata mujiya kowa kyararta yakeyi tsakanin Iyayen abinda yake qara rura wutar Bala'i a zuciyarta kenan ta sake cin Alwashi kala kala akan komawarta gidan Audu.
Wulaqancin daya mata baze tafi a banza ba wlh seya gane kurensa.

A bangaren Audu kuwa bayan dogon tunani da shawarwari daga yan uwa da Abokanan Arziqi ya yanke shawarar sake Aure, duk wanda ya masa maganar Binta fa se yace yana sane lokaci ze nuna abinda ya kamata yayi da ita da yawa sun dauka ya saketa ne ma ganin an tasarma rabin shekara babu labarinta a gidab. Wannan karon mata biyu ya rakito a lokaci daya, Hadiza data kasance Bazawara auranta biyu na farko Mijin ya rasu sena biyun kuma rabuwa sukayi tana da yarinya daya dashi yar Ƙofar dawanau ce amma tana yawan zuwa Goron dutse gidan Yayarta a nan suka hadu da Audun kamar da wasa yayiwa Mijin Yayarta magana wanda suke gaisuwar mutunci dashi babu bata lokaci ya shige masa gaba magana taje gaban Manya.

Ta biyun kuma Aisha, yace ga Sarkin Ƙaraye Maimartaba Alhaji Ahmadu Isah na biyu. Ita din Ƙanwace ga Abokin kasuwancin sa Najibullahi Amadu wanda suka hadu sanadin Noman Rani da Audu yakeyi a gonakinsa da suke Kusalla wani Ƙauye dake ƙarqashin Ƙaramar hukumar ta Ƙaraye Gonakin Audun sunyi iyaka dana Najibullahin wannan tasa suke haɗuwa idan sunje zagayen Gona daga haka kuma zumumci ya Ƙullu harta kai Audun yana zuwa gidan Najibu duk sanda ya shiga qaraye a nan kuma yaga Aisha kamar da wasa yacewa Najibun tayi masa dukda yarinya ce ƙarama shekarunta basu haura sha hudu ba tana cikin ta sha biyar sannan ganinta yana tuna masa da Bara'atu lokacin daya aureta banbancin ita Aisha tana da dan girman Jiki kadan tafi Bara'atu cika ido a lokacin da take da shekarunta.

Najibu ya tabbatar masa in har da gaske yake shi ze shige masa gaba akan maganar wannan tasa daya yanke shawarar Ƙarin Auran ya tuntubeshi, babu bata lokaci kuma ya gabatar dashi ga Maimartaba. Shaidar daya samu daga Najibu da sauran Mutanen garin da suke masa aiki tasa har Sarki ya Aminta dashi ya kuma ce yaje ya nemi yardar Aisha dan shi bayayiwa Yaransa Auran dole.
Chapter 77 · 0% Book details