← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 137

Sashe 90

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To wani sa'ilin kuma idan Al'amura sun cukurkuɗe mata ta rasa mafita se Turai tace suje gurin Malam, tun akan Muƙamin Yakubun da Audu yaso yayi mata buyagi yaƙi yarda Turai tace ta kawo kuɗi, har yarjejeniya sukayi akan odan aiki beci ba zata maido mata kuɗinta se gashi tana zaune Audun ya kira Yakubun wannan tasa ta fara amanna da sabgar dukda ko buƙatar ta taso ba ita take zuwa ba, Turai take bawa kuɗi aje a mata abinda ya dace tunda sabgarta ce, ta daɗe dayin amannan da Bin Malamai harda Bokaye zuwa gurinsu takeyi shiyasa har kawo yanzu Ta kanainaye Ali, shekaru an tasamma Hamsin amma se yanda tayi dashi ƙarin Aure da yake da burin yi tunda jajayen sahu ta hana haka yake ta gurgura rayuwa ga kuɗi ya tara mata ita da yayanta suna wadaƙa Yau tana waccen ƙasar gobe tana wannan kayan Alatu kuwa kullum cikin siya takeyi dan ita ba irin Binta bace tana cin kuɗinta Binta kuwa har yau har gobe abin naira goma sabo idan ka ganta dashi to Yaranta suka siya mata shi ko ma ace Jafar dan shine duk abinda ya gani na kwalliyar jiki a gurin hamshaƙan mata ze siyawa Hajiyar abin takaici kuma ba zata saka ba musamman idan taji kuɗin kayan, suturu da sauran kayan Ado da kuɗi kam ta tarasu babu Adadi har tsokanarta Faisal yake yana cewa
"Hajiya idan kika mutu zamu ja kaya da yawa dan wlh inaga kason abinda zamu samu na gadonki se yafi na Alhaji" duk ranar da yayi mata wannan maganar kuwa Ashar da tsinuwa babu wadda baya sha tace sedai ubansa ya mutu tamkar ita ɗin zata zauna gadin duniya ne.

Bayan sun gama waya da Turai ta miƙe tayi sallar Ishar da aka idar tuni, tana zaune a gurin takaicin duniya ya isheta, jibgin kayan snacks da Kaji da akayiwa Abba Tee take tunawa ya zatayi dasu harda irin shinkafar Larabawan nan da ake dafawa da naman Rago yayi ligib aka masa yanzu duk sun tashi a banza ta saka ran ze cakewa Hafsatu kuɗin da zasu maida wanda aka kashe harda riba se gashi wancan Dan is** yaron ya janyo mata Asara. Tsaki ta rafka yanda kasan wata riƙaƙƙiyar tsaka, ita kaɗai taci gaba da bala'i daga zaunen da take tana dannanwa Yakubu Ashar.

Faisal ya shiga kamar an jefoshi, ya kalli Hajiyar ya kalli cikin falon ganin ita kaɗaice zaune kuma tana ta faman sababi yasa ya matsa gabanta yana cewa
"Hajjaju, kinƙi yarda Jayy ya kaiki Asibitin da yace, lamarin nan naki fa kullum ƙara gaba yakeyi gara a tari abin tun beyi nisa ba"

"Dan ubanka Faisal kaima mahaukaciyar kake so kace mun?" Ta faɗa tana miƙewa tsaye, Faisal yayi wata dariyar shaƙiyanci yaja ja da baya dan ya san tana iya kai masa duka yace
"Ni ba haka nake nufi ba, bafa ciwon hauka bane Ciwon damuwa akace kamar yana damunki kuma idan yayi yawa ne yake komawa haukan kinga ba zamu so haka ta kasance ba gara ki daure aje Asibitin nan asan abinda za'ayi dan wlh daga mutum yana zama shi kaɗai yana maganganu kodai wata rana aganshi warwas a ƙasa ya mutu ko kuma aga ya zura da gudu saitinsa ya kwance.." Be dire maganarsa ba ta fashe da kuka tana cewa

"Sedai kaga hauka ko mutuwa a kanka dan iska kawai, fice mun daga ɗaki kafin nayi maka baki"

"Allah huci zuciyarki ni ban faɗa dan kiyi kuka ba, ɗaki kuma sedai kiyi haƙuri amma yau a nan zan kwana bazan shiga can ba akwai tamu da Salim" yana gama faɗa mata ya shige kitchen da lafcecen takalmin Salim daya sace. Abincin daya gani a gyare ya ɗebi iyakar abinda ze isheshi ya shaƙo plate ya fito har sannan Hajiya na kuka da faɗe faɗen maganganu marasa daɗi akan Yakubu daya fara jangwalota da kuma Faisal ɗin daya ɗora nasa wanda kuma be kyautu ace uwace take danganta Yaranta da irin kalamanba. Kan kujera ya haye abinsa bayan ya kunna Tv ya ƙure volume abinda ya fito da Hafsatu ya hau cin abincinsa ya gama ya gyara zama yana kallo, duk Tijarar da Hajiyar take zuba masa be tanka ba harta gaji dan kanta ta wuce ɗaki ta barshi anan bacci ya kwasheshi dan ko giyar wake yasha bazeje ɗakinsu ya tarar da Salim ba tsaf seya masa dukan mutuwar da yace ze masa.

Washe gari da safe zuwan Alhaji Zakatiyya ne ya wankewa Hajiya Binta baƙin cikin data kwana dashi jiyan, dukda sun fara maganar a waya tunjiya amma da yazo yayi mata bayani dalla dalla na yanda komai ya faru se ranta ya sakeyin fari ƙal.

"Ai ni wani tunani nakeyi, anya wannan shegen yaron ma ze bamu haɗin kai idan ya hau kujerar? Jiyan nan fa kar kaga tijarar daya mun a gidan nan ya zubar mun da mutunchi a gaban maƙiya" nan ta bashi labarin yanda sukayi da Yakubu jiya, Zakariyya ya jijjiga kai yace
"Haba kema Hajiya wani sa'ilin se ki ringa abunda be kamata ba, yanzu saboda Allah wannan tarbiyyace? Ko yar wani kikaga zatayi abinda be kamata ba ai hanawa zakiyi amma kike ingiza yarki ta aikata wannan ba daidai bane sam wlh kuma koni da ace na tarar da yaron sena ballashi wlh itaka kuma se naci uwarta dama ana yawan kawo mun zancen bataji na zata hassadace kawai akeyi mata ashe da gaskene to dan ubanta kawai zamu nemo koma waye mu aurar da ita mu huta kafin ta janyo mana abin kunya a gari".

Baki sake Binta ta ringa kallonsa har ya kai aya kamar zatace wani abu kuma seta haɗiye ta bar maganar tace
"Ai shikenan, zancen ya wuce, yanzu dai a aikamun da kasona a akawun kai a kawomun kash kawai na ringa ganinsu inajin ɗuminsu kusa dani"

"Miliyan dari ukun za'a kawo miki cash Hajiya?" Zakariyya faɗa cikin mamaki, ta harareshi tace
"Bangane dari uku ba? Wai nawane kuɗinma da kake kiran wata dari uku za'a bani?" Cikin ɗaga murya tayi maganar yayi saurin yi mata alama da tayi shiru saboda motsin taɓa ƙofa dayaji, Yakubu Bechine ya shiga fuskar nan a turɓune kamar ta Audu, Binta ta lafta tsaki tace

"Dallah rabu dani yaji mana, nama zata wani barene ze shigo"
"Barka da safiya Hajiya, Zakariyya Sannu" ya gaishe su daga tsayen da yake. Hajiyar ta harareshi bata amsa ba dan a cike dashi akan abinda yayi jiya Alhaji Zakariyya kuwa wani banbarakwai yaji daya kirashi Zakariyya gatsal kamar wani sa'ansa, yanzun shigowarsa ya haɗu da Ahmad ze fita shi kuma, seda ya kusa kaiwa ƙasa kafin ya gaishe shi kuma da Yaya ya kirashi ya amsa masa a wani wulaƙance yana shan ƙamshi kamar wanda yazo masa maula kuma yaron ko a jikinsa ya wuce abinsa har yana masa fatan fitowa lafiya daga gidan se yanzu Yakubu ƙaninsa ciki ɗaya ze masa wannan gaisuwar se kace wasu Abokanai? Koda yake ai Yakubun ma ya mutuntashi tunda Faisal da ido kawai ya kalleshi sanda ya shigo ita kanta Hajiyar be tsammaci ya gaisheta ba ya fita dan da ganinsa lokacin ya tashi ma daga barci.

"Tambayarka nake nawane kuɗin?" ta sake nanata masa seya sauke ajiyar zuciya yace
"To nidai abinda yace mun kenan kuma baze yuwu a saka kuɗin lokaci ɗaya ba saboda kinga yanzu EFCC ta tsaurara da binciken shige da ficen kuɗaɗe a Account ɗin mutane kar mu jefa kanmu a matsala gara a ringa sakawa da goma da biyar har ayi balancing"

"Zezo ya sameni kuwa, a gidan ubanwa kasafin ya zama dari uku? Nida nake lissafin kusan dari bakwai shine zaku cemun wata dari uku? Nifa shiyasa naƙi jinin haɗa sabgar kuɗi da Naziru dan macuci ne, tsayin lokaci kullum yace ana juya kuɗin za'a turo ina nan galahanga kenan kuna can kuna sharafinku se yanzu zaku ɗan yafutamun abinda kuka ga dama shiyasa naji ance ka siyawa Matarka motar Miliyan Ashirin shi kuma yana rabon kujerun Umarah ko ni dana hada pulan ɗin ban san komai ba kun ninkeni a baibai" murya a sama take maganar babu ɗar ko shakkar wani ya jita Zakariyya kuwa daga inda yake zaune har zufa ta fara keto masa ta tsoron kar wannan fallasar ta Hajiya ta janyo musu tonon Asiri tun ba'aje ko ina ba, muakutawa yayi cikin rage sauti yace mata

"Yanzu dai kiyi haƙuri na gaya miki yace ze zo kuyi magana tafiyar gaggawa yayi zuwa Legos amma Litinin ze dawo ba jimawa zeyi acan ba"

"Ai ko bezo ba ni zanje har gida na sameshi, yo hauka akeyi mu damfari ubanku sannan ku zagayo nima ku cuceni" ta sake sakin wata maganar

"Dan Allah Hajiya kiyi ƙasa da muryarki kar a jiyo me muke ciki" Alhaji Zakariyya ya sake faɗa,
Yakubu daya haɗo shayi yana daga kan Dining yana jiyosu ya kuma fahimci tsaf inda suka dosa a maganar tasu, daman ya zargi saka hannun yan uwan nasa a manaƙisar da akayiwa Aminun amma be kawo dagaske an ɗebi kuɗin ba ya zata lissafi kawai suka ƙara masa. Kwankwaɗe shayinsa yayi ya taso yana cewa

"A fitar dani ko wallahi na fasa ƙwai"
"Dan uwarka ka yanka Kaza ƙarewar fasa ƙwai, kai baka san a cike nake dakai ba ko? Ka bari mu haɗe seka gane baka da wayo wlh"

Be kalleta ba, Alhaji Zakariyyan yake kallo yace
"Ko a tabbatar dani AG ko wlh na fasa tayi wari kowa ya rasa dan naji ƙishin ƙishin idan Aminu ya tafi wani bare ake shirin kawowa".

Zabura Binta tayi da jin wata sabuwar lukutar Masifar kuma dake shirin danno kai, wani kuma? Wa za'a kawo? Kodai Ahmad ne? Kenan maganar da akeyiwa Alhaji tuni akanta kenan yace ya sameshi yau a gidan gona? Lallai bataga ta zama ba wai an saci zanin mahaukaciya. Wayarta ta raruma, Jafar zata kira tunda dashi aka ƙulla komai, ta kira sau uku bata shiga su Yakubu duk suka tsaya suna kallonta ganin yanda ta ruɗe se kokawa take da waya

"Wai wa zaki kira? Badai Alhaji ba?" Yakubu ya tambayeta, seta miƙa masa wayarta tana cewa
"Kunno mun Jafar na gaza samunsa yasan komai akan maganar nan dashi ake ƙullata".
Chapter 90 · 0% Book details