Sashe 82
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE 31*
Seda aka kwashi sati daya cikin wani yanayi a gidan, Audu ba magana babu murmushi bare dariya duk kuma wadda tayi kuskuren shiga sabgarsa ta jawa kanta tijara. Basu san me yake faruwa ba se randa zugar Yan Bechi suka zo Bus biyu ranar befita ba kusan kwana biyu ma kenan be fita ba sedai yaransa dake ta zarya a gidan kuma sedai su fita can inda yake ajiye mota suyi magana ko Binta duk iya labenta bata tsinto abinda ake ciki ba har seda yan Bechi sukazo jaje.
Ashe bayan motar Mai kwanaki Babbar Gonarsa da yake noman shinkafa ruwa ya shanyeta. Gonata ba yar ƙarama ba. Shinkafar kuma tayi kyau dan har an saka ranar girbi Dam din dake kusa da inda yake Noman yayi ambaliya gana ɗaya ya shafe gonakin dake kan hanya abindai ya munana ba'a cewa komai.
Binta ta ringa kyarma jin Maƙudan kuɗaɗen da aka ce sun narke daga kan Mai zuwa shinkafar,
"Shikenan, a garin kwashe kwashenka ka kwaso mana me farar ƙafa" ta faɗa hannu biyu aka jiki na tsuma hawaye suna sakko mata. Duk akayi shiru aka zuba mata ido banda Audu dayaja tsaki dan maganar tata ɓacin rai ta ƙara masa ya tuna da wani lokaci can baya sanda suna Yara tun Malam nada rai Goggo Fadi na ce musu yayan me farar ƙafa, a lokacin abinda ya dauka saboda Dada Farace tar duk jikinta abinda take nufi kenan kalar fatar ƙafarta shiyasa be taɓa gayawa Dadan ba se bayan daya girma ya san ma'anar abin sannan ya fahimci zaginsu takeyi shiyasa duk inda yaji an faɗa se ransa ya baci.
Binta ta ringa kuka tana maimaita an Auro musu me farar Ƙafa shikenan zasu tagayyare su shiga wani hali yan jaje suka koma wasu na ganin salonta data saba laƙawa matan da yake aurowa sharrine wasu kuma sun yarda da abinda ta fada dan tun bayan Auran Audun abubuwa suka fara canzawa yanayin bunƙasar Arziƙin tayi ƙasa ba'a dai samu wani ibtila'i babba kamar wadannan ba.
A hankali rayuwar walwala da jin dadin da akeyi a gidan ta fara juyewa zuwa ƙunci da tashin hankali dan zuciyar megidan a kusa take kullum ƙiris yake jira a taɓashi yayi zazzaga ga mata uku kowacce da ciki haihuwa kusa hatta da yanayin cima ta sauya dan samun ƙasa yakeyi ba sama ba. An kwashi watanni cikin wannan hali, Audu nada shirin mallakar rijiyar Mai tasa ta kasansa a kwankin baya domin har ya fara harhaɗa kudade sun gama tsara yanda za'ayi da Alhaji Zakariyya wanda ze siyar masa da daya daga cikin rijiyoyinsa sedai matsalar daya shiga a yanzu da harta girgiza masa jari ta tilasta masa karbo kudaden daya bayar matsayin kafin Alƙalami ya sakasu cikin harkokinsa na Noma da kiwo wanda anan Ibtila'in yafi sauka, Amfanin gonar da ya noma a shekarar sama da kaso hamsin ƙwari sun lalatashi haka dabbobinsa na gidan gona Kaji sedai a shiga basu abinci a tarar da au fululu a ƙasa sun mutu ko a hangi Sa ya Tirƙeƙen Rago yana kakarin mutuwa sedai a danne a yanka.
Abu dai kamar wasa ana saka ran samu sauƙi se ya zamana kullum kamar Tiri ƙaruwa abubuwan sukeyi. Mutane da yawa sukace hannu aka saka masa, Asirine, jifansa akayi ya bazama shine waccen tsangaya ya kai sadaka shine waccen gidansa kuwa kullum cike yake da Gardawa anata saukar Karatun Alƙur'ani idan an gama ayi sadaka amma abin se godiyar Allah kawai.
Ana wannan yanayi Hadiza ta tashi da Naƙuda cikin dare, Audu da Aisha ne suka fita kaita Asibiti dan Bibta cewa tayi Allah ya kasheta babu inda zataje da Aishar ta shiga kiranta Audu kuma tace masa Yara, be kamatu a barsu su kadai a gida ba. Haka kawai sun hau Titi suna tafiya mota ta tsaya, ya fita yayi yaj dube dube ya sake kunnata yana ja inji yayi wata ƙara Baammm mota ta cake kuma ko ba'a fada musu ba sun san Injine ya buga, tamkar Audu ya fasa kuka, ya fita nemo taimako Hadiza dai nan cikin mota ta haihu ta santalo danta Namiji ƙato.
Wani mutum ne ya taimaka musu ya ƙarasa Asibitin dasu se safiya aka sallamosu bayan an tabbatar da ita da Jaririnta duk lafiyarsu ƙalau motar Audu kuma akaje da Janwe aka dauketa.
Binta da taga Hadiza ta dawo gida da Da Namiji ba'a cewa komai, baƙin ciki kamar ta mutu ko zuwa tayi mata barka batayi ba har akayi sunan Aminu Hadizan ta koma gida saboda jikinta dayaƙi mata dadi tun bayan haihuwar Binta faɗi take ta tafi kenan ba zata dawo ba.
Haihuwar Hadiza ta sake zuwar musu da sabon sauyin dayafi na farko dan Asara ce take afkuwa kan Asara duk abinda Audun ya taba seya lalace Binta ta samu nayi ta ringa kwakwazo ai damab ta faɗa ya auro me Farar Ƙafa beji ba. Yakubu ya samu Audu yake tambayarsa
"Anya kuwa Audu kana fitar da zakka yanda take idan munyi lissafi?"
Cikin tsananin damuwa Audu yake ce masa
"Allah shine shaidata dukda bani da cikakken sani akan kasafin Zakka shiyasa ma bana fitarwa da kaina nake baka, kuma wlh Duk idan muka fitarda lissafin shekara yanda kace a fitar din nan haka nake cirewa da hannuna nake rabawa dan karma na bawa wani yayi ha'inci ya rage sannan ka san muna fitarda sadaka daban itama haka ake hadawa a rabar nidai na yarda wannan jarabawa ce kawai daga ubangiji ina kuma roƙon daya bani ikon cinyewa"
"Hakane, na godewa Allah daya sa ka yarda cewa duk wani tsanani daga shine haka kuma sauƙi ma daga gareshi ne. Kaci gaba da Addu'a muma muna tayaka karka kuskura ka bari wata maganar banza tayi tasiri a ranka ace maka wani ya maka Asiri ko wani abu, ka ƙaddara Allahn daya baka Arziƙin shine ya jarabceka akansa".
Kwanan Hadiza Ashirin da bakwai da haihuwa Aisha ma ta haihu ta samu Mace. A gida ta haihu daga ita se Bilki da kuma Unguwar zoman da aka kira dan Audu baya nan kuma babu mota balle a kaita Asibiti kuma Allah ya bata da sauƙi ta samu yarta Kyakykyawa me kama da ita. Binta na daki tana fama da kanta dan itama ta kusa Lantana ta kwaza mata zancen haihuwar, tayi wata dariya harda buga ƙafa tana cewa
"Ita kuma da ƙafar hagu ta shigo kowa na farawa da Magaji shine zata haifo mace? Koda yake na godewa Allah, Allah yasa in ma zata cigaba da haihuwar tayita jera irinta" Lantana ta tayata sukayita izgilanci akan Ikon Allah.
Da Audu ya dawo ya tarar da haihuwar, farin cikin jin Mace aka haifa ya wanke masa kaso hamsin na damuwar da yake kwana yana tashi a cikinta. Ya fita ya samo mota suka tafi Asibiti, su kadai yasa aka maido shi kuma ya tafi bakin Asibitin Nasarawa inda suke da zuwa Binta siyayyar Haihuwa dan rigar da aka sanyawa Jinjirar bashi ya siya ba be kuma san inda Aisha ta sameta ba halin daya shiga yasa duk ya manta da wai ana da buƙatar wasu abubuwan na haihuwa Hadiza ma se bayan data haihun ya basu kudi suka siyo abinda ya sawwaƙa tunda ta san yanda Al'amuran suke wannan kuwa cewa yayi a hada masa kayan barka na Alfarma, aka ware masa wanda ze tafi dasu lokacin ragowar yace a hade masa su ze turo wanda ze ɗauka ya wuce da sauran.
Binta data tsammaci Audu bazeyi murnar samun ƙaruwar Ɗiya mace ba se taga akasin haka, murna sosai ya ringayi, kwanan Aisha uku da haihuwa ta tafi wanka gida wanda daƙyar Audun ya bari gida ya rage Shida Binta se yara. Binta ta shiga zullumi, tunda Aisha ta haihu walwalar Audu ta ƙaru haka bashida wata hira seta yar jaririyar me suna Amina taci sunan Mahaifiyar Najibullahi yayiwa kara, basuyi sati biyu da tafiya ba ya kwashi yaran duka ya kaisu su gano Laila kamar yanda suke kiran yarinyar wannan ya ɗaga mata hankali ta kuma shiga zullumin to kodai itama ta haifi Mace ne saboda bata so ace wani Ɗa yafi nata shiga zuciyar Audu, amma da ta zauna tayi dogon Nazari seta watsar da waccen shawara, ita tana lissafine ne da abinda za'a mutu a bar mata, Yara Maza sune masu Gado duk wannan soyayyar da yakewa Lailan a banza tunda baze ɗauketa ya ɗora akan dukiyarsa ba da wannan ta watsar da tunanin haihuwar Mace taci gaba da lissafin zazzago Yara Maza.
Tsiranta da Aisha kwana goma sha tara ta haihu a Asibiti ta samu ya mace kyakykyawa da ita tamkar Laila dan yarinyar na fadowa Nurse din data karbeta ta dagata tana cewa
"Masha Allahu zankadi kin samu kyakykyawar yarinya da gani da Mahaifinta tayi kama dan ta fiki kyau" Nurse din ta gaya mata magana dan Binta ta gallabesu se dai idan bataje Awo ba amma tabbas se tayi faɗa da wata daga cikinsu.
Zabura Binta tayi ta fizgi ƙafar Yar kamar wadda ta fizgi leda ko wani abu mara rai, tawara ƙafafun tana so ta tabbatar dagaske Mace ta haifa ko kuwa tsokanarta sukeyi data tabbatar din kuwa seta saki yar Nurses da basu gama dawowa daga mamakin fincikar da tayiwa ƙafar yarinyar ba suka dulmiya cikin na sakinta da tayi ba taredadamuwar zata faɗi a ƙasa ba. Kuka ta fashe dashi bayan data koma ta kwanta. Nurse ɗin data cafe yar ta kalleta cikin ɓacin rai tace
"Amma kedai anyi yar ku*****ba, banda ke mahaukaciya ce dabba ki fizgi ƙafar Jinjira haka bakya ko tsoron ki ji mata ciwo sannan ki saketa a ƙasa? Wlh badan mu muka karɓi haihuwarki ba da nace sato yarinyar nan kikayi"