← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 137

Sashe 43

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakyar ta iya nutsuwa dukda ba sosai ba ta shiga kora musu qaryar data tsara ta haddace dangane da Auran da Audu yayi ba tareda saninta ba kuma akan ta masa magana yayi mata dukan kawo wuqa dakyar ta kwaci kanta shine ta gudo. Yanda ta tsara labarin babu wanda ya isa ya qaryata ta musamman ga shaida nan jikinta ya nuna. Mamaki madaukaki ya kama iyayenta musamman Alhaji daya ringa dubanta kamar me son ya tabbatar da dagaske take ko qarya takeyi.

"Wlh bazan koma ba, sedai ya zaba koni ko ita haka kawai bazanje su shafamun cuta ba kuma idan ya zabi zama da ita Dady ka gaya masa ya maido maka da duk wata dukiya daya samu ta dalilinka ai daman saboda ni ne kuma idan ya sakeni dole ya bayar tunda bata ubansa bace" Binta ta fada cikin gunjin kuka. Alhaji Zakariyya ya wuce bangarensa ba tareda yace mata qala ba ya kasa yarda da abinda ta fada, meya hada Audu da matan banza har ya gano matar Aure a cikinsu sannan da gaske Audu ne yayiwa yarsa gudan jininsa wannan dukan babu kara balle ya taci arziqinsa to kodai shaye ya fara toh?

A can falo kuwa da Mama ta gaji da ihu da kururuwar Binta ta daka mata tsawa tace
"Ki rufe mana baki, Audun ai ba mahaukaci bane da ze kamaki da duka haka kawai waye be san halin tsiwarki ba a gidan nan kuma Aure daman kin sani a rubuce take zeyi, ba wata kika tarar a gidan ba dan haka ba zaki fitar da ran kema za'a kawo miki wata ba. Abinda na jiye miki tun farko a Auran Tifical Bahaushe kenan wanda be yi Ilimin Boko ba balle ya waye da yanda rayuwa take, irinsu Audu a kullum tunaninsu be wuci su samu kudi su tara mata da Yaya ba basu damu da jin dadinsu ba balle walwala ko yanda zayuwarsu zata kasance, ke kikace kinji kingani dan haka yanzu babu wani dalili da ze saka kice zaki dawo mana nan, Munira ma Addu'ar Allah ya kawo wanda zero dauke mun ita nakeyi ballantana ki kaso Auranki ki dawo mun".

"Kai Mama ya zakice haka bakiga abinda ya mata ba se kace ba yarki ba, kuma ko auran zeyi ya rasa wa ze auro is Karuwa haba mana wannan ai ba abune me yuwuwa bama" Munira ta fada aiko ta juya kanta tana cewa
"Idan na sake jin bakinki a nan sena gwabjeki shashasha ai kema ba sanin ciwo kanki kikayi ba

"Ya isa haka Firdausi, ke kuma Mamana ki shiga ciki kiyi wanka Munira ki rakata clinic a dubata, ku dauke yaron nan daga qasa sannan wanda ya kawoki tafiya yayi ko yana nan?" Alhaji Zakariyya saya sake fitowa shirin shirin fita ya fada. Se sannan suka lura da Zakariyya dake kwance qasa abinsa yana bacci Direban ne ya shigo mata dashi ya watsar dashi a qasa tareda jakar kayanta. Ta miqe tana dingisawa Munira ta dauki Yaron suka wuce ciki.

KANO
Rai fes Audu yayi bacci babu damuwar komai tattare dashi illah mafarkin Amaryarsa daya kwana yanayi tareda shirya yanda tariyarta zata kasance nan da sati biyu masu zuwa shima saboda ya bata damar yin shirye shirye ne daga bangarenta dan shi a shirye yake fenti kawai ze saka a sakewa dakin can tazo ta zauna. Rashin zuwan Binta dakin be dameshi ba saboda yasan koda taje qarshe rigima zasuyi, da ya dawo daga sallar Asuba har ze shiga ya dubata kuma ya fasa dan yana so ya koma bacci yasan kuma muddin ya shigan bacin rai ze kwaso dan haka ya bari akan sa hade idan gari ya waye sosai.

Bugun qofar gidan da ake kamar za'a ballata ne ya tayar dashi. Ya ringa sakin tsaki yana tunanin wanene haka? Jallabiya ya saka ya sakko yana mamakin Ina Binta ta shiga ake irin wannan dukan qofar bataji ba ko itace ta fita qofar ta kulle ta waje. Takaici ya qumeshi ganin Lantana me aiki, ya tsani matar saboda kana ganinta kalar munafukai ne da ita. Ta durqushe a qasa kamar zata kwanta tana gaishe shi ya amsa a dake yana cewa

"Wane irin abu ne haka zakizo kina dukan qofar mutane"
"Kayi haquri yallabai kasan dokar Hajiya qarfe bakwai nake zuwa gidan nan to Nazo tun bakwan na buga ba'a bude ba na tafi shine na dawo na sake bayi bugun da qarfi ne ko bacci take kar nayi laifi tace banzo da wuri ba"

Tsaki yayi ya juya ciki, harya fara hawa sama ya dawo jin tanata qwanqwasa qofar Bintan shiru ba'a bude ba, ta matsa ya isa jikin qofar ya kwankwasa kana ya murda handle din qofar. Fahimta da yayi a kulle take yasa ya zagaya ta window ta da yake a tsakar gidan ya zuge ya leqa ciki, kayana da ya gani barbaje suka fahimtar dashi bata nan, se abin ma ya bashi dariya a fili yace
"Yaji tayi kenan"
"Ki tafi na manta zataje zata fita yau ta fita da wuri ina bacci" ya fadawa Lantana, kamar zata fasa kuka haka ta ja qafa tana waiwayensa, kamar tace masa zata zauna ta jira tunda ko fita Bintan zata yi tana barinta tayi mata jiran gida gashi ta kwaso yunwar safe ta saka rai zatazo taci me kyau kuma ace bata nan.

"Alhaji Mairo tazo ne? Kuma zuwa yaushe Hajiyar zata dawo?" Ta fada tana sunkuyar da kai,
"Idan ta dawo zata saka a kiraki ba yau ba ba gobe ba, kija qofar ki tabbatar kuma ta rufu idan kin fita" ya bata amsa yana juyawa tilas ta fita taja musu qofar gidan. Audu kuwa kasa komawa bacci yayi, tunanin inda Binta ta tafi ya shigayi, qila ba zata wuce gidan Baturiya ba dan bata da yar uwa a Kano bare yace gurinsu zataje Baturiyar itace yanzu babbar Qawarta ko yace Aminiya indai ba gidanta taje ba to Kaduna ta tafi.

Zabura yayi ya miqe yana salati, idan Kaduna ta tafi ya Alhaji zero dauki maganar? Ze goyi bayansa ko kuma ze goyi bayan yarsa ne? Idan Alhaji ya goyi bayan Binta yace ya sakar masa yarsa ya makomarsa zata zama kenan dan dai Alhajin shine abin tunqahonsa, duk abinda yake ganin ya tasarma zama da bazar Alhajin yake rawa.

A gurguje yayi wanka ya shirya, kai tsaye gidan Ali ya fara zuwa suka hade a waje Alin na shirin fita ya kuma tabbatar masa Binta bataje gidan ba dan babu inda zata buya da ze kasa ganinta.
"Dan girman Allah kazo ka rakani Kaduna" ya roqi Alin
"Kai yanzu? Ina babu wannan magana, ai yanda ka tirko rigimarka se ka san ta yanda zaka kasheta. Amma fa ban taba dauka da gaske kaci kai ba Audu se yanzu, duk matan da suke garin nan yayan mutunchi ka rasa wadda ta burgeka se wannan yarinyar? Kodai Asirinsu tayi amfani dashi ta zarge zuciyarka?" Ali ya fada yana tsareshi da ido. Audu yaja tsaki kafin ya shige mota ya daga ba tare da ya bashi amsa ba

Yau dinma Musbahu yaje ya dauka suka tafi Kaduna, seda ya isa qofar gidan kuma ya fara tunanin me zece musu idan ya shiga? Seda sukayi sallar La'asar da Magriba da suka riskesu a hanya kafin ya saka kai cikin gidan. Ko ina tarwai da haske, Tun daga Get suka fara gaisawa da ma'aikatan gidan harya isa qofar falo. Ta ciki Munira ta hangoshi, ta kwasa da gudu tayi daki ta fadawa Binta da tunda tayi wanka taci abinci take rama baccin da batayi jiya ba.
"Wlh ko me za'ayi karki koma ai raini nema kamar ke ace a miki kishiya bayan duk fafutukar da daukar hakkin da mukayi muka fitar da waccen shine za'a dakko miki alaqaqai to babu wannan maganar" Muniran ta qara zugata.

Tun daga yanda Alhaji ya amsa masa gaisuwarsa yaji guiwoyinsa sun qarayin sanyi dama Mama tana musu iso a tsayw suka gaisa ta shige ciki, yau ko Kayan Alatun da ake tarbarshi dasu be samu ba Ruwa da Lemo ma Alhajin ne yayi magana aka kawo musu.
"Bansan ta taho ba Alhaji, na dawo daga sallar Asuba kawai na tarar bata nan" Audu ya fada bayan dogon shirun da sukayi kowanne kamar ya rasa abin fada.

Alhaji ya nisa yana kallonsa yace
"Me ya hadaku da har yasa ta baro gidan ba tareda saninka ba?".
Be boye masa komai ba ya bashi labarin Auran da yayi wanda yake ganin shiya tunzurata ta baro gidan, ya rufe da qaryar cewa
"Bansan cewa zasu daura Auran ba saboda tambaya kawai akaje".

Shiru Alhaji ya sakeyi yana kallonsa kafin yace
"Menene gaskiyar maganara data fada na cewar Yarinyar Karuwa ce?" Seda ya daga kai ya kalli Alhajin saboda kalmar daya fada din se yaga kamar tayi girma musamman ana maganar matarsa ne ina laifin yace tsohuwa, wannan ya tunzuro zuciyarsa ta raya masa ci masa mutunchi Alhajin ya tashi yi amma ya danne dan ko ya masa qarya bashida amfani tunda har magana ta fito amma a ina Binta taji wannan batun?

"Kayi shiru" Alhaji ya katseshi, kansa na qasa yace
"Gaskiya ne, amma ban aureta ba seda na maidata gaban iyayenta tayi Istibra'i kamar yanda shari'a ta tanadar"

"To akan me ka daki Mamana har kaji mata ciwuka a jiki?" Alhajin ya fadi ainihin abinda yafi damunsa a duk cikin maganar, se Audu ya daga kai da sauri ya kalleshi jin abinda ya fada.

"Wlh Mari daya nayi mata, shima kuma cin kwalata tayi a gaban yan uwana da sukazo fadamun an daura aure ta labe harta tsinci maganar shine ta shaqemun wuya nace ta sakeni taqi ni kuma zuciya tasa na mareta bayan nan ko yatsa ban nuna mata ba wlh" ya fada cikin kare kai. Alhaji bece komai ba yaja Intercom ya kira cikin gida kan Binta tazo, ba'a dauki lokaci ba ta fito tana jan qafa fuskar nan kamar dafaffen Kunu ta zauna kusada qafar Alhajin tana hararar Audu wanda ke kallonta yana mamakin abinda ya karceta a fuska kamar sunyi dambe da Mage.
Chapter 43 · 0% Book details