Sashe 135
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ki fita kuma ƙarfe goma ne taron, umarni ne na baki ba wai shawara ba ki kasance a gurin" ya bata amsa cikin halin ko in kula ba tareda ya bi ta kan maganganunta ba. Hawayen takaici suka zubo mata ta share ta fice daga ɗakin, tana can ƙuryar ɗakinta ta kira Yar uwarta Maimuna ta gaya mata abinda ake ciki.
"Kije ki zauna a gurin saura kuma ki zama hoto kiyi shirun da kika saba a zartar da abinda ba haka ba dan nasan munafunci yasa aka shiryi wannan zaman ba wai dan Allah bane" Maimuna ta gaya mata. Tana shirya masa abin kari Hajiya Rabi ta shiga Falonta. Suka gaisa take tambayarta zaman da Alhaji ya kirata a waya yanzu yace mata wai ƙarfe goma.
"Nima da Asubar nan ya gaya mun wai akan Ahmad ne, amma ita hamshaƙiyar ai tasan da komai tunda tun jiya naga tana bada umarnin abincin da za'a dafa" Momy ta bata amsa tana murmushin takaici. Hajiya Rabi cikin jimami tace
"Ahmad kuma? Nasan dai ba laifi yayi ba koma menene Allah yasa Alkhairi ne, bari naje na shirya toh" daga haka ta wuce tana ta lissafin to wane irin abu kuma Ahmad yayi ko zeyi da har se an masa taron dangi haka?
Tun tara Iyalan Alhaji Audu suka fara hallara a gidan. Wasu su kaɗai suka zo wasu tareda yayayensu da matansu dan haka gidan ya cika hayaniyar jikoki kota ina tashi takeyi suna ta guje guje. Ƙarfe goma Mazan suka hallara cikin babban falon da ke bangarensa a ƙasa gaba ɗayansu Jafar ne kawai babu a gurin.
Bayan an buɗe taro da Addu'a tareda jawabin maraba daga uban garken, babu ɓata lokaci ya shiga zayyano musu maƙasudin kiransu wannan taro.
Shiru falon ya ɗauka banda ƙarar Ac bakajin komai se salallamin da Hajiya Binta takeyi murya a sama tamkar wadda aka aikowa da mutuwar iyayenta dare ɗaya, yanda takeyi seka rantse da Allah yanzu ta fara jin maganar, tamkar bada ita ta tsarawa Alhajin daya tara su ba domin ta ƙaddamar da wani shiri nata. Can kuma ta zabura ta miƙe tsaye idonta akan Ahmad daya sunkuyar da kai ƙasa, abinda yake ji a zuciyarsa baze misaltu ba, wai duk akanme? A ina aka taɓa haka? Shi yaushe ya cewa Alhajin maganar aurensa ta tashi? Auran da yake ƙoƙarin yakicewa ya haƙura da yarinyar shine aka zo ana masa wannan taron dangin akansa?
"Amadu ashe baka da hankali ban sani ba? Wayonka da nake gani na banza da wofi ne baka san komai ba se neman kuɗi kamar Ɓarawo?" Hajiya Bintan ta faɗa, Momy ta ɗago a karon farko tun zamanta a falon ta kalleta jin kalmar data jiɓanci gudan jinin nata da ita wai Ɓarawo ita kuwa Hajiya bata dakata ba a fusace taci gaba da cewa
"Wallahi tallahi ko sama da ƙasa zata haɗe banga uban daya isa ya ƙulla auran nan ba, yar Bakanike Amadu? Mu zamu haɗa surukuta da Bakanike kuma Sadaka yallah mayu? to idan ita uwarka sallamammiya ce komai aka ce bata musawa ni bazan lamunta ba. Iyakar irin tsiyar da aka ɗakko mana sun isa ba se an haɗo mana da wanda zasu zo suna mana ɗauki ɗaiɗai suna ciyayya ba" Hajiyar ta kai aya tsabar masifa numfashinta har neman sarƙewa yakeyi.
Alhaji Audu dake kishingiɗe akan kujera ya nisa yace "Duk wannan a ganina ba wani abun azo ana tayar da jijiyar wuya akai bane, magana ce ta aure kuma shi ma'auri yace yaji ya gani sannan ni da kaina nayi binciken iyayenta kuma ban samu wani abun ƙi da ze saka a hana shi auranta ba, ni kiram da nayi muku na taraku ne dan muyi shawara akan yanda za'abi gurin neman auran, suwa za'a wakilta suje".
Momy da Anty Amarya suka kalleshi kamar yanda da yawan yayayensa dake zaune duk suka kalleshin. Harara Hajiya Binta ta maka masa kamar wani ɗanta tace
"Lallai Alhaji, ya kake nema ka canza magana koda yake kwanakin nan ka zama me fuska biyu daman"
Mamaki kamar ya shaƙesu jin abinda Hajiyar ta faɗa masa, kunne, baki da hanci duk suka zuba suna jiran suga matakin da ze ɗauka amma sukaji muƙus ko tari Alhajin beyi ba sema Hajiya data ci gaba da sababinta tana cewa
"Da zakace bakaga wani aibu da ze hanashi auranta ba ai kuwa ita keda babban aibu, Talaka yar talaka jikar talaka kuma Mayya".
"Amma Hajiya talauci fa ba fasiƙanci bane, sannan baya cikin sharuɗɗan da suke hana aure. Kuma maita da kike jifanta da ita kin san cewar fa ba ƙaramin abu bane idan sukaji zasu iya yin ƙararki akan hakan tunda baki da wata tartibiyar hujja data tabbatar da abinda kike jifansu dashi" tsautsayi ya saka Hajiya Rabi magana tamkar kuwa Hajiya Binta na jiranta daman tace
"Babu shakka Rabi dole kice talauci baya cikin abinda ze hana aure saboda kinji zaki samu ƙarin yar uwa ko Ahalul fuƙara'u za'a ƙara yawaita? Koda yake ma a hakan ita ai ta fiki tunda nata uban ance yana da tsayayyar sa'ar da yake samun abun kaiwa bakin salati ba irin naki tsohon ba da se an bi gidaje anyi yawon maula kafin a tattara a kaiwa Iyali ya isa be isa ba a yayyafa aci shi kansa Alhajin daya kwaso wa kansa ƙaya gashi nan kullum cikin nadama da dana sanin auranki yake, jiya farar safiya gari ko gama haske beyi ba me dattin hula ya buga mana gida wai katangarku ta faɗi, daka fita ka bashi kuɗin ina dawowa kayi kana mitar daka saba duk sanda yazo maka maula irin rayuwar da kake so shima Amadun ka jefa shi a ciki kenan ya ƙare yana nema dangin Sadaka Yalla su dabaibayeshi su cinye sannan subi ɗan naman jikin nasa ma da ba auki ne dashi ba su lashe ni daman kwanakin nan zugewar nan da yakeyi ina ganin har sun fara lasar sane wlh sun zarge kurwa tab" Hajiya Binta ta faɗa tana tsaida idonta akan Alhajin.
Baƙin cikin maganganunta suka sanya Anty Amarya barin falon babu shiri saboda kukan daya taso mata, shekaru kusan Ashirin kenan babu ranar Allah da zata fito ta koma ba tareda ta goranta mata talauchin da ba ita ko iyayenta suka siyawa kansu ba, dukda tabbas Mahaifinta shi yake ƙara zubar mata da mutunchi saboda ya kasa wadata da dan Abinda Allah ya hore mata take taimakonsu dashi haka shima Alhajin ta sani iyakar Ƙoƙari yanayi cikin su ukun ita kaɗaice duk watan duniya seya saukewa iyayenta buhunhunan Abinci da kuɗin cefane duk a son Baban nata ya dena banzar ɗabi'arsa ta yawon maula gidajen Masu kuɗi, ya dai rage amma fa kullum yana tafe gidan Alhaji Audu, sabulun wanka omon wanke wanke ko yana da kuɗin da ze siya se yazo ya roqa an bashi.
Hajiya ta bita da Harara taja tsaki ganin Mu'allim yabi bayan mahaifiyar tasa bayan daya bi Hajiyar da wani kallon Tsana idanunsa sun tara ƙwallar baƙin ciki
"Umma ta gaida Ashsha, dama banga tsegumin daya kawo ku ba Alhalin baku da abin faɗi" Hajiyar ta faɗa tana buga cinya kamar wata yarinya.
Alhaji Babangida ne yayi gyaran murya, daga jin yanda yake magana kasan a tunzure yake yace
"Amma Hajiya Binta ni banga ta inda zancen Auran Ahmad ko wadda yake son aure ya shafeki ba tun da dai ba ɗanki bane. Ita mahaifiyarsa batayi ƙorafi ko nuna rashin amincewarta akan abun ba se ke meye naki a ciki? Sannan koda ace mahaifin yarinyar nan yafi kowa talauci a duniya wannan ba hujjar ace ba za'a auri yarsa ba tunda talauci ba fasadi bane"
"Nima abinda na gani kenan Yaya, duk ma ba wannan ba a gidan wa aka taɓa titsiyewa akan matar da yake son aure? Ina har yar rawar Tiktok aka auro mana gashi nan ta fitini kowa tana koyawa yaranmu shaiɗanci amma waya ɗaga kai yace wani abu kan hakan kodan saboda shi shafaffe ne da mai shiyasa ba'aga aibun abinda yayi ba se Ahmad da an san idan aka ce kar yayi ze haƙ
Lura ai biyayya kuma ba hauka bace" Dr Hassan ya faɗa cikin ƙunar rai.
Hajiya ta harari Alhaji Babangida, koda ta girme shi amma shakkarsa takeyi ta san ko shi Alhajin yana bashi darajar kasancewarsa Ɗa na fari a gidan, maganar Hassan ce tasa tayi kasaƙe tana kallonsa. Naziru ya zaburo masa yana cewa
"Ka kira sunana kai tsaye ka dena wani kwane kwane, kuma na auri yar Tiktok ɗin koda abinda zakayi akai?"
"Yi shiru da bakinka Naziru barni dashi" Hajiya ta gyara zamanta taci gaba da cewa
"Yanzu kai Hassan tsabar baka da kunya ana maganar matar aure me Asali da tushe daga babban gida har ka saka baki? Koda yake kana da hujjar bin bayan Al'amarin, tunda uwarku ta auru a matsayinta na Tubabbiyar Karuwa ai dole kace wannan ma ba......"
Tsawar da Hussaini ya daka mata me kama da saukar Aradu ta saka sauran maganganun bakinta maƙalewa. Cikin yanayin da yake nuna ƙololuwar ɓacin ransa dan hatta da jijiyoyin kansa daya sha askin Skin sun fito ruɗu ruɗu haka idonsa ya rikiɗa yayi jajir ya nuna ta yana cewa
"Akul Binta, duk abinda kike ji dashi ya tsaya kan waɗanda kika raina karki yi kuskuren sako mahaifiyarmu a shirginki domin yanzu ba da bace idan kuma ba haka ba...."
"Idan ba haka ba me zakayi?" Alhaji Zakariyya ya diro gabansa kamar wanda aka harbo da kwari da baka yana huci, Hajiya da tsoron Hussainin ya cikata jikinta har ɓari yake ta ja hannunsa Zakariyyah tana cewa
"Barshi Ubana kasan ɗan hau ne"
"Ki ƙyaleni Hajiya ku kuke nuna kuna tsoronsa a gidan nan idan zafin kai da ƙwaya yake ji dasu shi ƙaramin ƙwarone kansa baze ɗauki ko rabin chajin da nakeyi ba an faɗa ance Yayan Tubabbiyar Karuwa kayi abinda zak...."