Sashe 92
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Shin kana da kuɗin da zaka gabatar da duk wannan aikin daka ɗauko?" Alhajin ya tambayeshi, Ahmad ya haɗe yawu kafin yace
"Da akwai tanadin da nakeyi dukda nasan baze isheni nayi koda rabin abinda nake da buri ba a yanzu, amma a hankali ina sha Allah ina saka ran zan samu"
"Ok, to me kake so nayi maka kenan?" Alhajin ya jefa masa tambayar me kama da rainin wayo, jikinsa yayi sanyi dan be hango alamar samun nasara ba amma ya daure yace
"Wannan filin na cikin gari inda ake ajiye manyan Motoci da nake so idan da Hali a bani Aro tunda an dena amfani dashi".
"Aro?" Alhajin ya tambayeshi kamar da mamaki, kansa na ƙasa ya ɗaga masa shi da tabbatarwa seya gyara zama yace
"Se kum me?"
Muryarsa na rawa kamar a tsorace ya sake cewa
"Sannan idan da hali a gina mun, se muyi lissafi a yankemun abinda zan ringa biya duk shekara har na mallakeshi ya zama nawa".
Shiru ya ratsa tsakaninsu fin tsahon minti goma sha biyar har Ahmad ya yanke ƙauna daga samun Amsa me daɗi Alhajin kuwa kallonsa yakeyi yana nanata kalmar Aro da yace ya bashi na guri sannan ya yanka masa abinda ze ringa biya kuɗin hayar daya ambata tun yana yaro kenan ze ringa biyansa, kenan a matsayinsa na Mahaifinsa baze iya roƙarsa ya mallaka masa gurin kyauta ba ko kuma ya gina masa irin yanda sauran Yaransa Yayan Binta sukeyi ko su ɗauki abinsa ma suyi amfani dashi ba tareda saninsa ba?
"Idan ya tambayekan zaka yi masa hakan ne?" Zuciyarsa ta tambayeshi se ya rasa amsar da ze bawa kansa dan haka yaja numfashi yace
"Shikenan, ina fatan kana da Lawyer? Ka haɗa duk wata takadda data kamata ka kaiwa Barr, kuyi magana dashi daga nan ka samu Mr Lee ku tsara yanda construction ɗin ze kasance da abinda za'a kashe daga nan se a tattara lissafin, darajar filin dai shekara goma baya an taya Miliyan dari ban siyar ba, nasan yanzu ya ninka haka sau goma ko fiye da haka tunda kasan inda yake kaima kwaɗayin kyawun location ɗin ne yaja hankalinka dan haka zan bar maka shi a Dari biyu, ka gayawa Barr, sannan ka fara haɗo kuɗin filin tukunna koda rabine sannan zan yarda na fara gina maka".
Wani sanyi ya ratsa zuciyar Ahmad, ya shiga zuba masa godiya, seda ya gama kuma kwakwalwarsa ta shiga aiki na gaske, Miliyan dari biyu da Alhaji ya ambata kuɗin fili seya biya sannan za'a fara gini a ina ze nemota? Tanadinsa ƙarƙaf idan ya haɗa baze fidda kuɗin filin ba, amma ya yarda a ransa Allah zeyi masa ze kawo masa hanyar da ze samu abinda ze cika burinsa.
*ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.*
*NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...*
*LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...*
*A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:*
*- HAIR SALOON*
*-HENNA*
*-SPA*
*-DUKKAN*
*-PEDICURE*
*-MANICURE*
*-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI*
*DOMINSU SUMA*
*-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA*😊
*- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...*
*IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....*
*AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY 💅💯*
*Address 👇👇:*
*KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA*
*TEL:08133379628.*
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*BOOK 2*
*PAGE 3*
Daga gidan gona kai tsaye gidan Anty Manfusa Inda ya ajiyw Momy dan tare suka fito. Yayi masu bayanin yanda sukayi da Alhajin dan Anty Manfusan na cikin waɗanda zasu saka hannun jari idan Allah yayi buɗewar shopping mall ɗin.
"Wato uban nan naku lamarin sa yana matuƙar bani mamaki, yanzu ba'a rufa wata guda ba Yayansu Nihal (Dan Mijinta ne) yake cemun Anyi musu ƙarin kuɗin hayar shaguna a plaza, da aka kawo musu takaddu yaga an canza sunan da yake jiki wai yanzu ta zama ta NAZIRU BECHI, a yanda akace wai siya yayi gurin Alhajin wasu kuma sunce bashi yayi, nima yana faɗa nace wlh ƙaryane bashi yayi saboda rashin tsoron Allah duk girman plazar nan ace ya bawa Naziru shikaɗai shagunan ciki fa sunyi hamsin? nifa da nice a matsayinki wlh da tuni gayyar ta watse dan bazan zauna ana wannnan kutumar ubancin inyi shiru ba"
"To banda abinki Manfusa Naziru ai Ɗansa ne yana da damar mallaka masa duk abinda yayi niyya" Momy ta bata amsa. Manfusa ta harzuƙa tace
"Shi Ahmad ɗin ai Agola kikaje masa dashi shi yasa ze kasa bashi kyaitar fili, tsabar zalunci kuma ya lafta kuɗi har Miliyan ɗari biyu ce masa akayi Ahmad ɗin barawo ne irin sauran Yayansa da ze mallakin waɗannan kuɗin a shekarunsa? Ko kuwa saboda yana rayuwarsa cikin rufin Asiri bai taɓa neman wani abu a hannunsa ba?"
"Hakan ma da yayi nagode Anty dan wlh idan a gurin wani ne darajar filin nan ta zarce haka ko a haya za'a bani a gine dai a shekara Miliyan Hamsin sen bayar da ita wlh kinfa san location kafin ni nasan manyan Organization da suka nema ya hanasu har Gwamnati seda taso ta kwace gurin Baba Alƙali ne ya tsaya masa Allah ya taimaka aka bar masa in sha Allahu in har muka samu abinda muke so shekara biyar tayi yawa zamu mallakeshi ya zama namu kawai dai kuyi ta tayamu da Addu'a" Ahmad ya yayyafawa wutar masifar data fara ruwa, dole tayi shiru tunda uwa da Ɗan da take haƙilo akansu abinma.be damesu ba.
A hanyar komawa gida Momy take ce masa
"Nifa ubana ina tsoron mutanen gidanku akan maganar gurin nan, ban manta ba Yayanku Zakariyya ya taɓa nemar ya bashi ya gina Hotel yaƙi, baka tsoron idan sunji suyi maka lamɓo se ka saka kuɗinka su zugashi ya kwace?"
"Momy, dan Allah ki kyautata zato akan abin nan ki cire duk wani wasi wasi daga ranki. Nida ke duk mun sani Alhaji kaifi ɗayane, idan da beyi niyyar bani ba koda ace duniya zata taru akansa wlh baze bayar ba haka nan yanzu daya ce ze bada bana tsammanin da akwai abinda ze canza masa ra'ayi akan hakan, ki kwantar da hankalinki"
"Ai shikenan, Allah yasa tabbatar da Alkhairi"
"Amin Momy, abinda ya kamata ki faɗa kenan" daga nan suka shiga wasu hirarrakin harya sauketa gida ya juya yana so yaje yaga Barr Ansaruddeen Kalam, Childhood friend ɗinsa ne kuma shiya Aminta dashi da zama Lawyersa, a gidan Barr yayi Magriba da isha suna tattauna yanda za'ayi da takardun daya kamata su haɗa kafin su zauna da Lawyer Alhajin.
Cikin hukuncin Allah yarjejeniya ta ƙullu tsakanin Alhaji Audu Bechi da Ahmad Bechi, kowanne bangare ya gamsu da tsarin da akayi har kuma BECHI CONSTRUCTIONS sun aza harsashin gini bisa Jagorancin Mr Lee, Injiniyan da yake shugabantar bangaren gine gine da ƙere ƙere na BECHI GROUP OF COMPANIES kujerar da Hajiya Binta take hari domin kuwa tuni ta matsantawa Faisal tafiya bangaren Engineering ɗin yanzu haka yana shekara ta biyu ne a Civil Engineering, burinta daya gama kuma a tunɓuke Mr Lee ya koma ƙasarsu Faisal Bechi ya maye gurbinsa.
Ubangiji ya sirrinta Al'amarin ta yanda har gini yakai Linta Hajiya da Yayanta basu san abinda ake ciki ba, koda yake Yakubu Bechi ya sani saboda buƙatar fitar da kuɗin da aka kai kan Teburinsa dan tuni ya maye gurbin Aminu Bechi.
Yakubun be fiya shiga sabgar da bata shafeshi ba, a barshi dai da son kansa dan haka muddin Abu ba wai ya shafi personal Interest nasa bane baze ce komai a kai yanzun ma haka ce ta faru yayi shiru ya saka hannu kawai kamar yanda aka buƙata be kuma tattauna maganar da kowa ba.
Yanda akayi Labari ya isarwa Hajiya Binta kuwa hanya ce ta bida ita ta gurin da filin yake zataje gaisuwar Lantana wadda Allah yayiwa Rasuwa, Hajiyar bata yada Lantana ba a wannan bangaren kam tayi Alƙawari dan Lantanar tsautsayi ta gamu dashi a shegen yawonta mota ta kaɗeta shikenan ta gamu da Ƙafa, shekararta goma a zaune kafin Ajali ya sauka Bintan na leƙata lokaci lokaci duk kuma sanda ta wuce seta kalli wannan fili tana wassafa burinta akansa. A Zoo road yake, zuciyar Kasuwanci, kanta takeyiwa tanadi zata gina plaza ta zuba shaguna wanda ko iyakarsu me kadararta tasan ba ƙananan kuɗaɗe zata ringa shaƙa duk shekara ba.
Jiki na rawa ta samu Alhaji Zakariyya da zancen waya tada gini a wannan filin?
"Badai siyar dashi yayi bamu sani ba? Ka nema ya hanaka ina fakonsa shine ze siyar? To duk wanda ya siya ma kuwa ya siyi Asara dan ciniki be yuwu ba" Inji Hajiya Binta. Alhaji Zakariyya da har ya fita shiga ruɗu domin a halin da ake ciki a yanzun ya karɓi kuɗi a hannun Lebanese da suke son gurin zasu gina Hotel dan bashi zeyi ginin ba kuma ya musu Alƙawarin kafin watan da ake ciki ya ƙare zasu fara aikinsu se kuma yake Jin wata magana daban.