← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 137

Sashe 32

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko a jikin Bara'atu daman me zata saka suyi mata ita? Gaisuwa kuma babu dole a ciki ita a zauna lafiya babu ruwan kowa da kowa yafi mata. Lantana me share share itace Mara mutunchi a masu aikin ta kuma lura tafi fada a gurin Bintan sama da Mairo me mata girki wadda Bintan ta santa ta taba zuwa gidanta kitso sau daya can qasan layinsu take Lantanar ce bata san a inda ta kwasota ba. Matar sam batayiba, a suffa ma Astagfirulla kalar munafukai ne da ita kuma haka take a zahiri. Ita take zuba gishiri akan ciwon zaman su da Bintan. Yanzu da cikinta yayi nauyi ta kusa haihuwa tadan rage hayaniya da hayagagar da take mata shiyasa har take dan samun damar fita tsakar gida tasha iska.

Randa Lantana ta kunno Bintan kuwa ruwa ba zata barta ta hadiye da dadinrai ba, masifa zagi cin mutunchi da gori babu wanda bata mata, tun ba da Hadiza qanwarta tazo, ita take binta an mata aure shekara biyu baya zaman yaqi dadi suka rabu da Mijin nan ma babansu ya tasata gaba shine ta gudo gurin Bara'atun ta kwana biyu tareda Addu'ar ko Allah ze fito mata da Miji a Kano tayi aure ta huta da Fadan Babansu. Nan fa Binta ta samu nayi, gori da yana fita a jiki da bazasu samu sararin shan iska ba, sauqi daya da bata samu goyon bayan Audu ba da tace ya kori Hadizan, da haka zasu tattaro su cika masa gida to da yake har sannan ba a koma daidai ba tun abinda ya faru a Bechi dukda da fatar baki be mata magana ko fada akan abinda tayin ba kawai ya dan dauke mata wuta ne yanda yake rawar jiki yana mata abubuwa ya rage wannan ma na bala'in mata ciwo tadai barine zuwa ta haihu dan ta kanta take yanzun shiyasa ma take sararawa Bara'atun amma da zarar ta haihu zata qaddamar da shirin da tilas ta bar gidan da kareren qanwar tata data kwaso.

Kwanci tashi cikin Binta ya shiga watan haihuwa, lamari fa ya zarce nada dan kankat Audu ya tattara ya koma gurinta da kwana dukda daman kusan hakan ake, a girki hudu idan zatayi kwanaki takwas kenan da qyar ya kwana uku tareda ita dasun kwanta Binta zata doko qofa wai bata da lafiya daga qarshe ma tsakaninsa da Bara'atu sedai idan yana da buqatarta yaje da Rana ko da daren kafin lokacin kwanciya yayi daman saman sa Binta tace Turakarta ce ita kadai, daga qarshe dakin tsakar gidan aka gyarawa Abdullahi daya fara zama saurayi su Babangida kuma tare take kwana dasu a dakinta se dayan ya zama dakin Audun to a hakan ma ita bata damu ba tunda dai babu wata fitina ko a haka za'a cigaba da rakawa zata iya haqura.

Ranar da Binta ta haihu cikin dare naquda ta tasar mata, Audu baya nan ranar ya tafi Calaba dakko Mai a ranar dai suke saka ran dawowarsa amma har aka kwanta bacci shiru. Guraren sha biyu Ciwon gaske ya tasarwa Bintan, tun tana daurewa har abu yaci tura ta shiga kuka kamar yarinya. Abdullahi ne ya tashi fitsari ya fita tsakar gidan ya ringa jiyo kamar kuka daga dakin Bintan saboda darene guri yayi shiru kuma window dakin a tsakar gidan yake dan haka ya tafi da gudu ya bugawa Bara'atu qofa tana bacci taji bugun ta farka a gigice ta fito ya sanar mata da abinda yaji

Tunanin naquda take ne ya fara zuwar mata dan haka ta juya ta tafi dakko zani da Hajib idan yaso ta fita ta kirawo Baba Uwani maqociyarsu. Tana zuwa qofar dakin sukaci karo da Audu, bata gama mamakin sanda ya dawo ba tsaqarsa ta katseta.
"Ki kamata muje mota" ya fada rai a matuqar hade, jiki na rawa ta kama Bintan da tasan Azaba ce tasa ta yarda ta riqeta. Haka sukaje Asibitin murtala, kamar ana jira suna isa ko minti biyar ba'ayi ba Binta ta haihu ta samu Da Namiji. Yanda Audu ya ringa murna seka dauka haihuwar fari aka masa. A can suka qarasa kwana hardashi seda safe suka dawo gida Bara'atu ta ringa godewa Allah da zuwan Hadiza, shaf ta manta da batun Yara a gida seda sukaje Asibitin. Da ace Hadizan bata nan bata san ya zatayi ba qila sedai ta tako da qafa ta dawo dan ba zata barsu a gida suka kadai da daddare ba.

Kan jiki kan qarfi ta ringa hidima da Bintan da Jaririnta kyara da hantara kuwa babu wanda bata gani. Abinda yafi damunta yanda Audu ya shareta, ko magana ta masa a ciki yake amsawa hidima yake tayi da Matarsa da Jaririnsa kayan fitar suna ma ana saura kwana biyu Abdullahi ya shiga da qatuwar leda ta zazzage taga kayansu ne shida su Babangida ko dan kunne babu nata a ciki. Suna duba kayan ya shigo fuskar nan kamar hadari ya wuce dakinsa ta tashi ta bishi. Seda ta kai masa abincin dare ya gama ci kafin tayi masa godiyar kayansu Babangida da ya bayar ta qara da cewa

"Dan girman Allah idan wani laifi nayi maka kayi haquribka sanar dani na gaji da wannan zaman gabar da mukeyi" ta tattara qarfin hali ta fada wanda Sadiya maqociyarta kuma qawarta guda dayace ta bata wannan shawarar ta cewa ta dena shiru, duk idan taga canji a gurinsa ta tuntubeshi suyi magana tunda tasan halin Binta baze wuce ta qulla mata wani abun a gurinsa bane koda ace baze yarda da ita ba in har ya gaya mata laifinta ta kare kanta shikenan ai ba makaho bane kuma ba kurma ba qin Allah ne ya saka idan an gaya masa abu yake hawa ya zauna ba tareda yayi bincike akai ba.

Seda ya mula kafin ya fara magana yana cewa
"Wato badan Allah ya kawoni ba so kikayi ki bar Binta ta mutu ba zaki fita ki taimaka mata ba? Koda yake dama tasha fadamun kince se kinyi Ajalinta da ita da abinda yake cikinta ba zata haifeshi ba. Wlh mamakinki nake Bara'atu, yaushe kika zama haka? Ko kuwa dama hakan kike kin lullubeni ne baki fito da ainihin kalarki ba is yanzu?"

"Ni ya kamata nayi maka wannan tambayar yaushe ka zama haka Audu? A zatona kaine mutum na farko da zaka fara bayarda shaida akaina amma kuma se zaton nawa ya zama ba gaskiya ba, koda ace ba zaka shaideni ba Audu yaci ace kasan me zanyi da wanda bazan aikata ba. A Bechi tace na nufeta da wuqa ka yarda yanzu kuma tace ni nace zan kasheta da dan cikinta shima ka yarda wane mugun abu na aikata maka daya janyo irin wannan rashin yardar a tsakaninmu har takai ayi mun qazafin zanyi kisan kai kuma ka hau ka zauna? Nayi tsammanin ko Qadangarenta tace nace zan kashe zaka qaryata balle ran mutum ba dYa ba harda na Jaririn dabe iso duniya bama" Bara'atu ta fada cikinmatuqar qarfin hali hawaye masu dumi suna sakko mata.

https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR*
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*HALIN KISHI*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*FREE PAGE 14 (LAST FREE PAGE)*

Hawayen ta suka qara gudu lokacin daya miqe ya fice daga dakin bayan daya antaya mata tsaki me qarfi. Ta dade zaune a gurin tana kuka, meta tsarewa Binta? Ita data shigo ta tarar batayi kishi ta tayar da hankalinta ba se itace zata yita hada mata tuggu da makirci a gurin Miji shi kuma sam babu bincike ya ringa zama kan magana da an gaya masa? Tana tsaka da wannan kukan Hadiza ta kwankwasa mata qofa, seda ta gyara fuskarta ta fita Hadizan ta gane tayi kuka amna tayi shiru bata tambayeta dalili ba kuka kuma ta gaya mata ta daura aure dashi tunda ba zata tashi tsaye akan wannan Kishiyar tata makira ba se ta zauna tayi musu kuka har hawayenta ya qare.

"Yace kije ga naman qauri can an kawo a gyara, banda rainin wayo ke zakiyi mata suyar qaurin ma ina yan uwanta sunzo? Dama ace zaman mutunchi kukeyi da sauqi amma keda bola banbanci kadan ne a gidan nan sann.."
"Ya isa Hadiza, muje ki kama min" Bara'atu ta katseta daga mitar data kwaso.

"Allah ya sauwaqe kedai da zaki iya bismillah" Hadizan ta fada tana zama akan kujera, tasan ba zatayi ba tunda ta fada dan haka ta fita rai babu dadi zuwa gurin gyaran Qaurin. Ta tarar da Mairo na hura ta dora yan ciki lantana kuma tana ware nama da qashi da alama hadosu masu gyaran naman sukayi.

"Barka da Rana Hajiya" Mairo ta gaisheta, fuska babu walwala sosai dalilin quncin zuciya ta amsa mata, Lantana kuwa ko kallon arziqi bata mata ba sema tahau waqar Habaici daga Mairon har Bara'atun babu wanda ya tanka mata daga qarshe ta nemi guri ta zauna dan Mairo tace ta bari zasuyi tana kallon Lantana nata jan qwafa da alama zataje tayi abinda ta saba na hadin masifa.

Suna kaskon qarshe yan uwan Binta biyu suka zo gurin ta gane Babbar ita tana dan zuwa dalilin akwai yan uwan Mijinta a nan Kanon me bi matan dai sau daya ta taba ganinta se yau na biyu. Dazu da suka sauka har ta fita zataje ta gaishe su suka hadu da Binta a tsakar gida tace ko barandarta ta taka seta mata rashin mutunchi shiyasa ta fasa dan hakan yanzun ta gaishe su suka amsa kadaran kadahan. Robar da aka zuba Nama suka dauke suna barwa Lantana sallahun idan ankwashe sauran a kai musu.
Chapter 32 · 0% Book details