Sashe 105
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaban Momy ya wuce ya zauna dab da Ƙafafunta yana kallon Step sisters ɗinsa fuska ɗauke da murmushi.
"Barka da dawowa Sheikh Jafar" Momy ta faɗa cikin raha.
"Mun same ku lafiya Momy?" Ya mayar mata ta amsa da
"Lafiya lau, ya ka baro abokanan sana'arka da gurinsu Yaya Muhammadu?"
"Duk suna lafiya suna gaisheku"
"Madallah sannu da zuwa" ta sake faɗa kafin ta miƙe ta shiga kitchen, bata jima ba ta fito me aikinta Amira na biye da ita da babban Try ta ajiye a gaban Jay kafin ta gaishe shi ta koma.
Ya miƙawa Nu'ayma Babyn Khadija hannu ta tafi kamar zata faɗi dan tafiyar tata batayi kwari ba, Khadija, Maimuna da Aslamiyya suka haɗa baki gurin yi masa sannu da zuwa ya amsa musu kafin yace da Khadija
"Yaya Khadija ya yara? Ina Alhaji?"
"Yana Islamiyya se sun tashi idan an ɗauko shi zasu biyo ta nan mu wuce".
"Kasha ruwa, ga mutuminka nan Coconut Juice" Momy ta faɗa ganin yana ta wasa da Nu'ayma be taɓa abinda aka ajiye masa ba.
"Yah Jay sha kaji dan Allah ni nayi fa" Maimuna ta faɗa cikin zumuɗi ta sauka ƙasan ta tsiyaya masa a Cup ta bude kwanon da aka zuba kayan maƙwalashe tana cewa
"Har small chops ɗin ma ni nayi fa"
"Kice kin zama Chef babu labari? Me ya samu wayarki na dena ganinki Online?" Ya faɗa yana karɓan Cup ɗin da ta zuba masa Lemon, seta kalli Momy, Momyn tace
"Kya kalleni? Ki gaya masa abinda kikayi Ahmad ya kwace wayar mana"
"Ai base ta faɗa ba ma Momy tunda kikace Yah Ahmad ne nasan tayi abu mara kyau ne, Any Juice ɗin yayi daɗi sosai, and this too" ya nuna Chocolate cake dake hannunsa.
"Thank u, shine Yah Aslamiyya yace ba zakaci ba wai beyi daɗi ba"
"Zanci mana har Token zan baki ma for the good job".
Gwalo tayiwa Aslamiyya Momy da Khadija na musu dariya Faɗan sako da sako sukeyi kamar kaji.
A cikin zuciyar Jafar kuwa abinda ya sabaji a duk sanda yake cikin ɗakin Yauma yaki, ina ma ace shima ɗan ɗakin ne? Duk sanda ya zo Nigeria irin wannan tarbat yake samu a gurin Momy. Ita zatayi masa maraba ta bashi abinci Hajiya kuwa se Hayagaga ta cikashi da tambayoyi da ƙorafe ƙorafe, ruwa seya tambaya kafin zata tuna ya kamata a bashi babu ruwanta da duba daga wani guri me nisa yazo yana da buƙatar hutu da kulawa Aa matsalolinta kawai sune a gabanta.
"Bari naje nayi sallah an kira La'asar" ya faɗa yana miƙewa tsaye, Momy tace
"Tam, zasu Miƙo maka abinci Gas ne yayi mana tsiya amma an gama ƙarashene kawai"
"Nagode, Yah Khadija kafin ki tafi kimun magana" daga haka ya fice daga falon. Seda ya leƙa Hajiya Rabi, a mutunce suka gaisa se sannan Yaranta suka samu sukunin yi masa sannu da zuwa suma, ya kama hannun Zayyad suka fita tare zuwa masallaci.
"Idan kina Ƙaunar Allah Binta ki zauna, mene haka? Waike bakya kunyar idon mutane ki ringa abu kamar wata zararriya?" Turai ta faɗa tana tare Ƙofar uwar ɗakin Hajiya dake shirin fita ta raba hali, Jafar na fita tacewa Aidah, Jikarta Babbar Yar Nazira ta bishi taga inda zashi ilai kuwa tace mata ya shiga ɗakin Momy ta zabura zata fita Turai ta hanata shine ta turata ɗaki suketa tata burza tun dazun lokacin daya ɗauka a ɗakin be fito ba shi ya saka Harzuƙata, ta window taga fitowarsa da shigarsa Gurin Hajiya Rabi shine ta zabura zata tareshi ta tsigaleshi taji tsakanin Aisha da Rabi ko da akwai wadda ta tayata ɗaukar cikinsa ko ɗawainiyar rainonsa ne bata sani ba dayafi mutuntasu da girmama su akanta?
"Turai kirabu dani, ni ban iya haɗiye baƙin ciki ba sena Amayar dashi, ke ni fita ki sallami kowa ma ta wuce gidanta zaman me kuma za'a mun tunda wanda ake taron danshi ya watsa mun ƙasa a ido, sallami kowa dan Allah na samu sararin huce fushina yanda ya kamata" Hajiya ta faɗa a fusace tana fuzgewa daga riƙon da Turai tayi mata.
"Kamar ya in sallamesu ni na tara miki su ko yaya? Sannan Ai kya jira su gana cin abinci ko ba'ace su tafi ba kowa kama gabanta zatayi tunda ba yinin Biki bane balle ace se rana ta faɗi idan kuma zaki fita ki korasu daman ba baƙon abu bane a gurinki ai siyar da hali" Turai ta mayar mata itama a fusace kowa ta kalli Bango tana hura hanci.
Jafar kuwa daƙyar ya ƙwato ya fito daga Masallaci, ɗakinsu shida Ahmad ya wuce. Ya saki murmushi ganin yanda aka canza tsarin ɗakin daga zuwansa na last year ya canza musu Gado da Labulaye da Carpet harda penti aka sake sabo ga kyawawan Food warmers da Jug a ajiye yasan aiken Momy ne. Seda ya sakawa Ƙofa Key kafin shiga wanka. A cikin kayan Ahmad ya nemi marasa nauyi Three quater Kaki da Armless shirt ya saka ya dirarwa Abincin.
Tuwo ne da Miyar Agusi, taji Wasulla na ruwa dana ƙasa wato Momyn kamar tana shiga zuciyarsa duk zuwa seta tareshi da abinda yake da burin ci idan yazo gida. Sosai yaci tuwon ya sha Juice ta ture kayan gefe ya kishingiɗa jikin gado yana jin jikinsa ya cika da yawa, shida abinci me nauyi kamar tuwo se yazo Nigeria shina baya ci da yawa saboda Diet ɗinsa. Wayar Ahmad ya kira,
"Ina Get" Ahmad ya faɗa bayan daya amsa wayar dan idan be ɗaga ba Jay kira zeyi tayi baze barshi ba. Ragowar Abincin daya rage Ahmad yaci suna hira Salim ma ya shigo se Lawal da Mu'allim da suka shiga suka gaida shi suma suka kuma gaya masa mutane na jiransa a ƙofar gida.
"Ka ce musu na fita" Inji Jafar. Ahnad na siɗe hannu yace
"Sun fika sanin whereabouts ɗinka ai, garama ka tashi kaje kafin Alhaji ya dawo ya tarar da taro a Ƙofar gidansa ya dirar maka daga dawowa"
"Yana nan da halinsa kenan be canza ba? Is high time da muma ya kamata mu mallaki gidan kanmu haka a dena zuba mana Iko, small thing ze fara badai a gidana za'ayi this ba? A gidana kuke mun that?" Jafar ya faɗa yana mimicking muryar Alhaji Audu. Ahmad dasu Salim sukayi dariya, dole ya fita ya sallami Fans ɗakyar kafin ya koma ciki Matan da Hajiya ta tara nata fitowa kowa na kama gabanta ya ɗauke kai kamar be gansu ba yanajin Yannatan na kiran sunansa amma ya share. Shi ko ƙawar hira be hango a cikinsu ba balle Alaƙar da iyayensu suke son ƙullawa dashi.
Bayan Magriba suka shirya shida Ahmad sukaje gidan Late Brigadier General Baballiya Bechi yayiwa Matarsa da yaransa Ta'aziyya, daga can Ahmad yace su biya gidan Baba Alƙali sukayi rashin Sa'a baya nan yana Abuja se washe gari ze dawo inji Mama Balaraba, dukda basu tarar dashi ba amma suka zauna har kusan 11 suna can dan idan sukaje gidan nan basa iya fita da wuri daman musamman da suka tarar da Fadlan ya fara caccakar Jay akan Premier League wai suna kwan gaba kwan baya, se sunyi sama se su diro ƙasa sun kasa yin abin kirki. Drama Jay da Fadlan daman bata ƙarewa tunawa da dokar Alhaji Audu ta hana kaiwa dare a waje yasa suka tafi a 11 ɗin.
"So we go cross fence today" Jay ya faɗa sanda suka tarar da Kantamemen Get ɗin gidan a garƙame, Ahmad yace
"Da rabon kayi kwanan Cell kuwa, gidan Alhajin Bechin zaka haura? To sauka nayi tacan farkon Layi karma yace tare muke" suka fashe da dariya suna tuna wani lokaci zamanin yarinta Jafar da yarbanzar ƙiriniya Hajiya bata nan ta kukke ɗakinta ya shiga ta window wai ze ɗakko Uniform ɗin Islamiyya ya shiga amma fitowa ta gagara a zatonsa bata saka key ba a Ƙofar ze buɗe ta ciki ashe ta murza Key abinta haka ya zauna
ɗaki har Magriba akayi sa'a Alhajin ya riga Hajiya dawowa akace ga Jafar can ya haura ɗaki ya kasa fitowa Alhaji ya tubure se an kirawo yan sanda kafin a buɗe ƙofa se su tuhumi Jafar dalilin daya saka ya haura masa gida dakyar fa Aka bashi baki ya ɗauko spare key ya buɗe shi amma yaci duka a gurinsa ranar.
Horn Ahmad ya danna, Issa ya leƙo ganin motar Ahnad ya buɗe Ƙofar,
"Da alama Alhaji baya gari" Ahmad ya faɗa bayan da ya ajiye mota. Issa yace
"Aa, mun faɗa masa kunje gidan Alhaji Soja kuma kunayin dare acan shine yace idan kune a buɗe, idan ba ku bane kowaye ya kwana ga waje, kuma Alhajji Yaƙubu bayaga gida? Ko bashi a Kano baki ɗayane?" Ya tambayesu.
"Ohna manta ko banga Yah Yakub ba, ko baya nan?" Jafar ya faɗa Ahmad yace
"I'm not sure da safe dai mun haɗu, ta yuwu yayi tafiya ko kuma Gidansa ze kwana kasan Yah Yakub ya zama jan wuya Alhaji ya saka masa ido kawai"
"Kodai Hajiya ta tsaya masa ba?" Inji Jafar daga nan suka wuce ɗaki, yana so yaje gurin Hajiyar amma yasan tashin hankali ze siyo da se ta hana kowa bacci a tsanake gara ya bari ayishi ido na ganin Ido.
Ƙofar falon Alhaji da suka gani a buɗe tasa suka fahimci yana ƙasan dan haka suka shiga sedai suna saka kai duk su biyun sukayi dana sanin shiga a lokacin, Hajiya na zaune da akama su take jira, Jay ya juya ze koma Ahmad ya rufa masa baya ta tashi da hanzari ƙiris ya rage ta hantsila tana cewa
"Gasu nan, ka gani ko ya janyeshi sunfita ze fara koya masa yawon Iskancinda yakeyi, wlh tallahi kayi mun tsakani da Aisha da zuri'arta ta fita a sabgata idan ba haka ba ta bari na waiwaya kanta wlh na lahira se ya fita jin daɗi.