← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 137

Sashe 41

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Watanni uku bayan dawowar Zubaida gida, a hankali tun tana sharewa harta yarda ta sakarwa Audu fuska soyayya me sanyi ta qullu tsakaninsu, dukda tana matuqar jin kunyarsa kasancewar yasan komai na rayuwarta ta baya, ta kanga kamar wata rana ze goranta mata bama shi ba babban damuwarta yan uwansa take zaton ya zasu dauketa idan har sukaji ita din wacece a baya gashi yace mata yana da mata ire iren wadannan tunanin yake sare mata guiwa taji kamar ma Auranta da Audun baze yuwu ba. Watanninsu hudu tare Malam Hassan yace ya turo magabatansa saboda yana so ya hada da Auran Surayya ayi gaba daya, su uku suka rage cikin yaya shiga da mahaifiyarsu ta haifa ukun sun rasu suma bayan rasuwar Mahaifiyar tasu se Surayya da Ibrahim Wanda yake bin Zubaida ne suka rage masa be kuma sake Aure ba tun rasuwar Habiba shekara bakwai kenan.

Babu damuwar komai Kai tsaye Audu ya tafi Bechi ya samu Yaya Baba ya gaya masa cewar zasuje nema masa Aure nan da sati daya, mamaki ya kama Yaya Baba saboda Yakubu yaje Bechi ba'afi sati daya da tafiyarsa ba kuma beyi musu zancen Auran Audu ba dukda yaga alamar kamar Audun ma be san yaje din ba, tun rabuwar Auransa da Bara'atu abubuwa sukayi zafi tsakaninsa da Yakubu.

Yakubun Yayi fushi me tsanani shi kuma Izza da ganin yanzu ya isa ya hanashi ya neme shi su sulhunta. Yaya Baba bashida ta cewa dan haka ya amsa masa da Toh, ya kuma sanarwa da sauran yan uwansu abinda ake ciki take Hashimu yace ba zashi ba. Aminu ya samu Audu ya tambayeshi Yakubu yasan da magabar kuwa yace masa Aa.
"Wannan abinda kukeyi sam be kamata ba, kaine qarami dan haka ka nemeshi ku sasanta. Me yasa kakeyin tufka kana warwara? Kayi nasarar hade kanmu sannan kuma ka koma ka bata da Yayanka da kuke ciki daya akan Mace wannan wane irin abu ne?"

"To ni Aminu menene laifina a ciki, Shi ya fiya damuwa ne kawai idan ba haka ba menene nayin fushi akan na rabu da Bara'atu nifa nake zaune da ita ni nasan matsalarta amma shi ne da fushi dan na saketa?"

"Saboda yafika hango abinda yake daidai ne shi yasa kai kanka kuma da zakayi duba na tsanaki zaka gane abinda ake qoqarin fahimtar da kai. Da ace zaka ji shawara da ka haqura da sabon Auran nan ka maida Bara'atu dakinta" Aminu ya sake fada. Audu yayi shiru kafin ya kalle shi yace
"To kai ka aureta mana ko kuma shi din ya aureta tunda kun fini sanin darajarta".

https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE17*

Badan Audu yaso ba sedan Yaya Baba dayace muddin ba sanarwa da Yakubu ba bazasuje masa neman Aure ba tilas ya kirashi ta wayar Landilayin wadda ya hada a gidansa shima kuma Yakubun suna da ita a Ofishin da yake aiki dan haka ya kirashi.

"Allah ya sanya Alkhairi yasa ayi a sa'a" abinda Yakubun ya fada masa kenan bayan daya shaida masa zancen Auran se kuma yaji babu dadi dan haka yace masa
"Amma zaka zo ko? Saboda ina tunanin a daura Auran kawai idan an kai kudin"
"Ina da Ayyuka da yawa a gabana bana jin zan samu halarta sedai daga baya nazo naga Amarya amma a ina ka samo matar?" Yakubu ya tambayeshi, Audu yayi shiru kamar mara gaskiya kafin yace

"Amm yar nan cikin gari ce unguwar Alkantara, yarinyar nada hankali da nutsuwa sosai se ka ganta ma"

"Amma da zan baka shawara ka dauka da nace kayi haquri ka maido da Bara'atu kodan darajar yayanta ka dubi rayuwar da zasuyi a Bechi babu wadataccen Ilimin Islamiyy ada Boko"

"To ya kake so nayi da wannan din bayan na sanarwa da Iyayenta zan turo so kake na zama qaramin mutum?" Audu ya fada a dake dan ya gaji da maganar ya maido Bara'atu da suka dameshi da ita, Yakubu yayi murmushi yace

"Bance ka fasa ba kana iya hadasu su ukun ai Alhamdulillahi Allah ya hore maka abinda zaka iya riqe su nidai yaranka nake dubawa saboda zuwan nan da nayi na gansu banji dadin yanda suka koma ba gashi sun fara tasawa"

"Naga muma a Bechin nan aka haifemu muka girma, yanzu kai bada shekarunka ba harda Aure ka kammala sakandire ka tafi Jami'a? Suma idan sun girma sun kai munzalin da zasu iya wahaltawa kansu se su dawo nan gidan su zauna yanzu dai ba wannan maganar mukeyi ba ka daure dan Allah kazo kasan dai nan duniya bani da kamarka" Audu ya fada. Yakubu yayi dariyar takaici yace

"Zanyi maka Addu'a daga nan kuma da ace abinda ka fada da gaske be baka da kamata da baka qi karbar shawarata ba muddin ba cutar da kai nayi niyya ba, yanzu ina aiki ne zamu sake magana idan na samu lokaci" daga haka ya ajiye waya ya bar Audu sororo da waya a hannu seda ya kashe ma sannan ya tuna dayar maganar da yake so ya masa ta jin dalilin daya saka ya dauki Baballiya ya tafi da shi Lagos zeyi hutu ba tareda su. Sanar masa ba seda sukayi magana da Alhaji Zakariyya yake gaya masa dan a gidan Baballiyan yake zama idan sun samu hutu yanzu haka yana ma yana shekararsa ta qarshe shirye shiryen fita sukeyi.

Duk yanda Audu yayi da Yakubu akan yazo Auransa qi yayi dole ya haqura badan yaso ba kuma har ransa yaji rashin jin dadin hakan saboda bashi da tamkar Yakubu sannan ya rasa abinda yasa Yakubu ya dauki wannan fushin dashi. Yanzu kenan yana so ya nuna Bara'atu ta fishi a gurinsa kenan?
Haka nan ya tura su Yaya Baba da wasu Abokanansa sukaje masa neman Auran wanda ba'a tashi daga gurin ba seda aka daura shi. Yana gida ranar be fita ba yana tsammatar dawowarsu Binta natayi masa gwalgwaso ta aje wannan ta kawar da wancan surutu kuwa har kunnensa ya gaji ga babu halin yace tayi shiru ko ta fita ta barshi ya huta.

Lantana ce ta kwankwasa musu qofar saman, rawar kan matar ya zarce misali seda Binta ta taka mata burki sannan ta dena zirgillin shigar mata turakar Miji. Bintan ce ta bude qofar ta leqa fuska a hade tana cewa
"Meye? Wai sau nawa zanja kunnenki akan tako benen nan ballantana kiyi tunanin shiga dakin nan? Ke wace irin daqiqiyar mace ce ne Lantana?"

"Kiyi haquri Hajia, baqi kukayi shine nace bari nazo na sanar miki" Lantana ta fada cikin qasqantar da kai amma a ranta zagin Binta takeyi.

Binta ta yatsina fuska tace "Baqi kuma daga ina? Ni yau babu wanda babu wanda nayi da ita zatazo"
"Ai Hajiya Maza ne ba mata ba kuma kamar yan Uwan Alhaji ne dan naga wasu suna yanayi dashi"

Tsaki me qarfi Binta taja, ta tsani wannan zaryar maukar da yan uwan Audu suke musu. Ba'a rufa sati se wani yazo daga Bechi badan ta taka burki bama har kwana suke so su ringayi amma duk zatayi maganinsu dan ba zata dauki wannan abun ba suzo su dabaibayeshi su cinye musu dukiya to bada ita ba. Ciki ta juya ba tareda tacewa Lantana komai ba, Audu na kwance kan kujera tace

"Kayi baqi"
Da gaggawa ya miqe kamar wani mara gaskiya, be ko tambayeta su waye ba ya shige daki ya zuro rigar wandon jikinsa ya sauka qasan seta bishi da sauri dan se anyi komai a gabanta. Haka take duk sanda yan uwansa suka zo seta kasa ta tsare komai zasu fada ko ya basu seta gani idan akayi dace kuwa saqo ya biyo ta hannunta daman se abinda mutum ya gani. Qannensa Mata dai da suke ciki daya tun fitar Bara'atu babu wadda ta sake taka qafarta gidan se yan dakin Goggo Maryo ne suke zaryar zuwa ko gajiya basayi da wulaqancin Binta dan Mazan sun fisu kamewa da wadatar zuci muddin sukaje to dole ce ta saka ko kuma maganar Gonarsa wadda Aminu da Yaya Baba ne suke kula masa dasu yanzu.

Bayan Audu ya sauka qasa a tsakar gida ya tarar da Baqin nasa a tsaitsaye.
"Bismilla muje can falon" ya fada yana musu jagora zuwa falon da Bara'atu ta fita can ya gyara ya saka kujeru yake sauke baqinsa amma haka Binta zata bisu har can din. Suna zama tana shiga ko gyale bata yafo ba ta dirirce ganin harda Yaya Baba ko babu komai shidin babbane a cikinsu yanayin rayuwa yasa take ganin kamar ma ze girmin Dadynta dan wahala tasa tsufa ya masa sammako banda yanzu da Al'amura suka fara daidaitar musu ya dawo hayyacinsa dalilin Alkhairan da yake samu daga kula da Gonar da yakewa Audu amma da kam anji jiki ga tarin iyali ga Abinda suka Dogara dashi na Noma Hashimu ya ringa Ha'intarsu yana Azurta kansa su da wahala amma shine cikin walwala da jin dadi wannan ya saka suka yada makaman yaqinsu suka rungumi su Audun hannu bibbiyu gashi kuwa suna sharbar romon damakaradiyya har ya sauke farali a dalilin hakan.

"Au kune sannunku da zuwa ina wuninku?" ta fada tana jada baya tareda sunne kai, suka amsa mata a tare, ta tsaya daga qofa bata fita ba bata shoga ciki sosai ba Audu ya kalleta yace
"Kawo musu ruwa mana"
"Ayyo toh, bari a kawo" ta fada ta juya tana dannan masa Ashar a ranta. Mairo ta kwalawa kira ta gaya mata ta kawo ruwa tayi sauri ta koma bakin qofar ta labe.
"Munje kuma Babanta ya sanar mana da daman kun gama magana shiyasa bamuyi gardama ba dayace a Daura auran, to Alhamdulillahi anyi komai kamar yanda shari'a ta koyar yanzu ya rage kuma ka saka ranar da matarka zata tare, Allah ya sanya Alkhairi ya sa Abokiyar arziqi ce" Yaya Baba ya fada.
Chapter 41 · 0% Book details