← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 137

Sashe 62

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daren ranar Binta ta wuce Saudiyya cikin tashin hankali bayan sun rakaya dasu Turai sunje Asibiti sun ganewa idanunsu Tagwayen da akace Zubaidan ta haifa. Kuka wiwi ta ringayi kamar wadda kanta ya kwance wai ya za'ayi tazo a bayanta ta haifi tagwaye kuma Maza kenan yanzu ta fita kasafi cikin dukiyar Audu kenan. A Saudiyyan haka tayi Ibadar rabin Addu'arta ta Allah ya sa tayita haifar Yan biyu Maza ne bayiwa kanta wata kwakwkwarar Addu'a ba balle Yayan da take roqon a bata haka aka sauke Hajji ta dawo kamar yanda Audun yayi tunani daga ita se Kayan data tafi dasu yar tsarabar data yiwo bata kai kota kashi goma cikin uban kudin data tafi dasu ba.

Bayan dawowarta ta tarar da an kwashe kayan Zubaida wannan ya dan rangwanta mata damuqar data saka kanta a ciki. Daman daga Asibiti Zubaidan gidansu ta wuce kamar yanda Mahaifinta ya buqata Yakubu yayi iyakar roqon da ze iya amma Malam Hassan yace yayi haquri kawai. Ran Yakubun ya sake baci matuqa ya dauka Audun zeyi Nadama ya kuma nemi su sasanta ta koma dakinta amma seyaga akasin haka. Ya dai siyawa Jarirai kayan na Alfarma haka itama Maijegon ya hada da ita da Manya manyan Ragunan suna dana Qauri ranar kwana biyar da Yan Bechi suka zo wanda suma Yakubu ne yaje ya sanar dasu suka kai kayan Barkar.

Da aka kwana biyu har ya koma Ikko ya sake dawowa wata daya bayan haihuwar kenan ya sake tarar Audu da zancen ya suke ciki sun daidaita zata dawo idan ta yada wanka ko kuwa kai tsaye babu boye boye yace masa

"A gaskiya ni bazan iya zuwa nayi bikon wata mace ba, zan bata lokaci harta huce daga fushin da takeyi, idan ta nuna buqatar cigaba da zama a gidana se mu daidaita".

Yakubu ya rasa abin fada ya ringa kallon Audu kawai yana jin kamar ya rufeshi da duka. Ya dade yana ganin marasa hankalin mutane amma Audu leader ne, cikin tsantsar takaici yace

"Abinda ya hanaka ka maido da Bara'atu kenan tunda bata furta da bakinta tana so ta dawo ba ko?"

"Ka gane ashe, ai Allah ya kallo duk wani abu daya kamata ace nayi da ze nunawa Bara'atu ta dawo dakinta nayi. Kana kallo dawainiyar gidansu kaf har abinda be zama dole na ba yi musu nakeyi, duk wata se nayi mata aiken kudi da kayan abinci kuma idan naje Bechi ina zuwa naga Yaran to me kuma ya rage da zanyi ya nuna mata Biko nakeyi? Sena zubarda girmana na roqeta ta dawo bayan Alfarma zanyi mata naci gaba da zama da ita bayan laifin data aikata mun?

Itama Zubaidan ai koda ina da laifi nata yafi yawa a ciki, me yasa bata tsaya tayi mun bayani yanda zan fahimce ta ba amaimakon haka seta ringayin abubuwan da zasu qara tabbatar mun da zargina akanta ni kuma shine ya tunzurani na yanke hukunci. Kuma ai ita har haquri na bata da naje Asibiti tace babu ita babu ni kuma ta hanani taba Yayana shine kake so naje gidansu nace ta dawo salon ta samu damar rainani ko to ni bazan iya wannan aikin zubarda mutunchin ba" Audun ya fada cikin dagawa.

Mamaki, takaici hade da baqin ciki sukayiwa Yakubu rubdugu lokaci daya amma ya rasa kalmar da zeyi amfani da ita gurin zagin Audun dan haka ya kada kai kawai ya wuce ya barshi yana jinsa yana masa magana akan ya tsaya mana ina zashi be ko waiwaya ba. Duniya dai akace tafi bagaruwa iya jima, tabbas yana jiyewa dan uwansa randa muguwar Ta'adarsa zata bibiyi rayuwarsa.

https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 24*

Rayuwa ta miqa, kwanan Binta Talatin da bakwai da dawowa daga Aikin Hajji ta haihu ta sake samun Da Namiji da yaci suna Naziru, yafi babu wai Agwai da baqin Da yanayin da ta nuna kenan domin ta gama sakankancewa da Addu'ar data ringa zagaye Ka'aba tanayi akan Allah ya bata yan Biyu Maza ta karbu to dayan ma babu laifi tunda yanzu sunyi kai daya su ukun gaba daya kowacce tana da Yaya Maza Biyu kenan, amma ba ta sare ba za kuma taci gaba da addu'a Allah badi war haka tayi yan uku ma ba biyu ba kuma duka Mazaje dan babu yanda za'ayi wata mace ya fita kaso a cikin Dukiyar da ubantane silar samunta.

Ko kaza bata zo mata barka ba daga Bechi balle suna haka sukayi bidirinsu da ita da yan uwanta se qawaye da makwafta shi kansa Audun tun bayan abubuwan da suka faru zamansu ya canza salo dan gaba daya ya daura mata laifin itace silar Rabashi da Zubaida ita kuma ta nuna sam ba haka bane ba. Da fari bayan dawowarta ta biyeshi zaman ya zama babu dadi sedai bayan da suka tattauna da Turai da kuma sabuwar mashawarciyar da suka samu wato Basira se abubuwa suka canza daga bangarenta.

Basirar ta qara tunasar da ita cewar muddin fa tana son biyan buqata seta kwantar da kai. Tilas ta maida kanta banza a gurin Audun, tunda har ta fahimci shi mutum ne me matuqar son girma da son a nuna ya isa to tayi amfani da wannan damar gurin kaishi matsayin da Allah be kaishi ba. Ta ringa nuna masa nan duniya babu yashi, duk kuma abinda ze fada karta kuskura ta musa masa ta barshi akan komai yayi daidai ne baya kuskure.

"Hajiya sufa Maza kamar qananan yara suke wlh, fahimtarsu kawai zakiyi me suke so menene basa so shikenan ku zauna lafiya. Kuma a yanzu abinda ya kamata ki mayar da kai gurin yi shine ta yanda zaki kafa kanki da Yayanki a gurinsa yanda zakiyiwa duk wata mace da zata shigo rayuwarku Zarra" Basirar ta fada taba durqusar da kai irin na shahararrun munafukai. Binta ta hura hanci tace

"Ai ba se kin fada ba, haihuwa dai an haifesu amma naci alwashin muddin ina raye yaya nane zasu zama kan gaba a komai na dukiyar Audu, baze tuna yana da wasu yaya ba bayan nawa, duk wanda yaci Arziqin Audu to ni naso"

"Ina yinki qawata fada da cikawa wannan aikinki ne" Turai ta fada tana bata hannu suka tafa. Haka suka yita qulle qulle da shiri na yanda za'ayi yanzu da nan gaba. A haka har lokacin haihuwar tata yazo bayan anyi suna da kwanaki Turai taje ta sameta da zancen rashin zuwan yan Bechi.

"Ni se nake gani ko dai babu dadi yaci ace kina sabga dasu, saboda dangin Miji ba qananan Munafukai bane, kinga idan suka kafawa mutum qahon zuqa Allah ne kadai ze kubutar dasu. Kina kallo dai yanda nake zaune da nawa duk sharrin mutum be isa yace na masa mugun abu a fili ba kuma na sani sun sani basa qaunata nima bana qaunarsu amma tunda ban bada qofar da zasu wulaqantani ba kinga qalau muke zaune dan haka kema dole ki gyarota dasu, ki jasu a jiki musamman ma naki da suke Fuqara'u Ahalin tsiya. Kamar kajine kina watsa musu tsaba na tabbata zasu biki ko wannan ma ze qara miki fada idan kika kame yan uwansa kinga koda ace kin samu tangarda dashi ba fata ba yan uwansa zasu zame miki makamin da zaki gyara komai" cewar Turai.

Binta ta numfasa tace
"Turai baki san yan uwan Audu ba musamman yan dakinsu. Yanda yake da wannan kafaffiyar zuciyarfa iwa ta mutanen farko haka suke. Bana tsammatar kudi ze saka su soni kina kallo ko shi din da yake musu shine jigon komai nasu akan Wannan shegiyar Bara'atun duk suka masa tawaye, yanzu an kuma na biyu sun nuna sunfi qaunar Karuwa akaina shiyasa duk suka qi zuwar mun Barka amma ai na samu labarin su sukazo suka kaikayan suna suna gidansu Zubaidan.

Tsinanniyar Bilkin nan tun ranar sunan Dady na farko bata qara tako qafarta gidan nan ba gara Aishar tazo jinya kwanaki can Mazan kuwa tunda suka zo fadar Baqin labarin Auran Karuwa basu dawo ba hatta Baballiya tunda aka Auro ni sau daya ya tako qafarsa gidan nan sedai fa idan naje can Kaduna na ganshi ya samu guri ya baje kamar gidan ubansa yanzu nan Yakubu ne kadai yake zuwa idan cin mutuncibsa ya tashi kuma daman duk ciki Audun ma shi yake shakka shi kadai ne yake tsayawa ya gaya masa magana son ransa kuma ya shanye baze iya mayar masa ba a yanda ya tsaneni kuwa ko duniya da abin cikinta zan bashi baze qaunaceni ba haka Annamimiyar matarsa ni ko kamanninta bazan iya tunawa bama yanzu. Kai na tsani Yakubun nan iyajar raina wlh" ta qarasa tana cizon yatsa tsanar da tace tanawa Yakubu ta nuna qarara akan fuskarta.

"Dukda haka dai ance se an tsaga ake ganin jini, daurewa zakiyi ki cusa kanki cikinsu ko basa qaunarki ta hakane fa zaki ringa sanin wasu abubuwa da suka shafi shi kansa Audun, hatta da dukiyar tasa kince duk abinda ya samu acan yake narkata, filaye gonaki duk ya tattara acan to idan kika qwafe a nan kin bar musu komai can ta yaya zaki san me kuke dashi? Irin hakane kina zaune kina lissafin dokin Rano se anzo ranar kasafi kiji abinda ba haka ba ita Bara'atun da take cikinsu tsaya mata zasuyi taja rabo me tsoka ga wannan itama tunda sun nuna tafi musu ke duk mara musu baya zasuyi a barki da lissafi. Amma idan kika shige su ta yanda ba za'a layance miki komai ba kin sani shima kuma ki matseshi ta yanda duk abinda yayi ko zeyi seya gaya miki"

"Yana ma gayamun in dai ya siyi abu ze fada mun tunda wannan matsiyaciyar ta fita ne dai kinga yanda abubuwan suka koma"
Chapter 62 · 0% Book details