Sashe 56
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AUDU
Tunda suka baro Kano abin duniya ya taru yayi masa yawa haka nan maganganun Binta suka samu matsuguni a zuciyarsa dukda ba kaitsaue tayi magana dashi ba amma se ya ringajin kamar saqo ta bashi, girman Cikin Zubaidan ya jefashi a kokwanton da sam be taba shiga ba se yanzu da Binta ta soko wannan maganar sannan tambayar da yayi mata akan Cikin datace masa ta zubar a baya da shirun datayi ya sake jefashi cikin rudani wannan tasa bayan sun Isa Bechi yabkasa zama har seda ya nemi qarin bayani akan Kwantar da ciki da tayarwa da yaji a zancen Binta.
"Falalu ya fara tara da zancen a gurin zaman makoki da suka hadu a maimakon ya bashi amsa se kawai yayi dariya yace me ya hadashi da shirmen Mata a bakinsu yake jin wani Kwantaccen ciki amma shi be yarda da akwai shi ba. Shaidan ya rigada ya samu abinda yake so yayi kane kane a zuciyarsa haka nan ya jefa masa wasi wasi kala kala, sam ya kasa nutsuwa shiyasa daya fita salkar Magriba kai tsaye ya wuce gidan Bilki dukda ba shiri suke a yanzu ba tun bayan abubuwan da suka faru amma da yake buqatarsa ce yau ta tashi se gashi a gidanta. Tasna Yazo Bechi dan tun rana Labari ya isar mata ta bar gidan raauwar babu dadewa su kuma suka shigo daman kuma Audu na shiga Bechi labari ze karade ko ina kafin Alkhairin kyautar sa ya isa gida gida wannan lazim duk zuwa zeyi rabon abinda ya samu wa jama'ar gari musamman a baya zamanin da suke tare da Bara'atu sunfi zuwa garin sosai yanzun yakan jima beje ba amma duk in ya shiga dai zeyi Alkhaiti daidai yanda hali ya bayar.
A dakin Bilki ya zauna ya rafka tagumi yana sauraronta bayan da yayi mata tambaya akan gaskiyar ana iya kwantar da ciki tsayin wani lokaci sannan a tayar dashi sanda ake so?
"To zancen gaskiya anayi dukda dai ban tabayi ba kuma ban taba ganin wadda taje akayi mata ba amma na samu labarin mutane da yawa da hakan ta faru dasu, kaga babu nisa nan gidan Malam Ado ai kasan Ila Abokin Baballiya ta shima ba'a jima ba anyi irin wannan dambaruwar gidansa yayi Aure matar watanta shida ta haihu. Yar Umarawa ce ya aurota daman dai tun lokacin bikin aketa surutai akan yarinyar kamar magana ta dakko shine iyayenta suka tada auranta babu shiri, hatta dakin da ya sakata fa ubanta ne ya bashi kudi ya qarasa ginashi saboda yace be shirya Aure ba basu karbi Lefe ba kuma karka so kaga uban kayan garar da aka hadota dashi bana tsammacin sun qare har yanzu.
To a yanda Zainabu dai take cemun (kishiyarta) kasan Qanwarsa ce yayan Maza suke wai Amaryar watanta biyar sega Ciki ya fito qato kamar zata haihu gobe, kuma sunce sudai lokaci daya sukaga wannan abun mamaki da fara laulayinta da girman cikin befi watanni ba tofa ciki nayin qato daman akwai qanwarta da aka hadota da ita ta shirya ta tafi can garinsu satinta daya sega Babarta tazo ganinta wai ya akayi ya akayi ta tattarata suka tafi gida wai bata da lafiya za'a nema mata magani ba'a rufa wata ba akace ta haihu, su Zainabu sunje sun gano yar ance musu bakwaini ce to tace Aradun Allah wannan ya idan ka kalli idonta ma zakace ta shekara a ciki kuma qatuwa da ita tabarakallah in taqaita maka zance dai anyi wata uku da haihuwar yanzu Auran yake da wata tara tana can gidansu har yanzu bata dawo ba".
Wannan labari na Bilki ya sake bashi tabbacin maganar da Binta ta fada ana haka kenan, amma wace hujja ze kama ta cewar Zubaida ta shigo gidansa da ciki? Sannan wane tabbaci yake dashi akan kwantar da ciki tayi ta shigo masa dashi gida? Dole ya tsananta bincike ya gano koma menene amma yanda al'amarin ya kasance lokaci daya ciki yayita girma kamar na Aljanu ya bashi mamaki shi kansa. Be gayawa Bilki dalilin tambayar ba duk nacin data yi masa ya tattara ya tafi amma ya kasa komaqa cikin gidan can wani guri ya samu ya zauna yana ta lissafin ya zeyi idan ta tabbata da ciki Zubaida ta shigo masa ba nasa bane ba?
Seda yaga dare ya farayi ya koma gidan ya rigada ya cusawa ransa wani abu na daban shi yasa ya kasa koda kwana daki daya da ita ya bude dakin da Binta take sauka ya kwana a ciki. Har mamakin kansa ya ringayi yanda ko sau daya be taba tunano rayuwarta ta baya yaji ya qyamaceta ba ko ya kasa mu'amalantarta amma yanzu yaji ta fita a ransa akan abinda be gama tabbatarwa ba. Haka suka dawo Kano nan kuma zamansu ya dauki sabon zama ya fita a sabgarta tsakaninsa da ita ya ajiye mata kudin cefane idan ya kwana a dakinta kenan in tayi abinci bayaci gaba daya ya birkice saboda rashin nutsuwa daya sakawa ransa.
A bangaren Zubaida kuwa gaba daya ta maida hankalinta gurin Ibada ne da kuma kula da lafiyarta data abinda yake cikinta tayi matuqar qoqari gurin ganinbata bari damuwar Audu tayi tasiri a ranta ba haka duk iskancin da Binta zata mata bata daga kai ta kalleta yanda kuma be sake mata tambayar da yayi mata randa sukaje Bechi be itama bata daga maganar ba a haka suka kwashi tsayin sati biyu cikin wannan hali. Da safiyar ranar Asabar tana zaune daga bakin qofarta ta cire saiqoyin data jiqa ta shanya su kafin ta gama shanye ruwan daya jiqun seta maidasu, tana zaune kan Tabarmar data shimfida da yar Radionta a gefe tana sauraro ita kadaice a gidan tun safe Audu da Binta suka fita kamar yanda taji a bakin Bintan tana bawa qawarta da taje gidan labari Audun ya biya mata Aikin Hajji fitar da sukayin tana kyautata zaton duk cikin shirye shiryen tafiyar ne dan abin ya matso a kwanakin kusan kullum se sun fita.
Taja Qaton kofin robar dake cike da ruwan magani ta kurba ta ajiye ta saka hannu biyu tana shafa cikinta da taga kamar yayi qasa sosai kuma ya dan rage girma, sam bata ji shigowa ko sallamarasu ba saboda ta nitsa cikin tunani se maganar Binta taji akanta tana cewa
"Ahaf, ka gani ba? Wasu jiqe jiqen aka qara kawo mata bana gaya maka wannan tsohuwar Matar Babanta ce take mata safara ba kullum tana tafe gidan nan yau ta kawo wannan gobe ta kawo wancan gashi nan kuwa cikin ya fara komawa za'a sake danne shi qila ace mana anyi bari se wata shekarar a haife shi tunda mun ramfo wannan wayon ko?" Bintan tayi maganar tana zuba mata ido fuska a washe irin duniya ta mata dadi babu abinda yake damunta duk da cewar bata tsammaci za'aja lokaci ba wannan Bam din data dana be tashi ba amma kamar yanda Turai ta gaya mata tabi komai a hankali dai kar suyi gaggawa to tana zuba ido taga yanda wasar zata kaya.
Audu bece komai ba ya wuce samansa, jiki a sanyaye Zubaida ta miqe ta shiga tattara abubuwanta Binta natsaye tana zubda mata habaici,
"Ke kin dauka zaki kawo mana shege wato kici bulus bamu gane ba? To qaryarki tasha qarya wlh tun wuri ma ki nemo farkan daya dibga miki ciki ki nana masa abinsa badai a gidan nanba kar muke kallonki"
"Wlh Binta ki tsoraci gamuwarki da Allah" Zubaidan ta fada hawaye na sakko mata, Binta tayi shewa tace
"Nan da sati i yanzu ina gaban Ka'aba yarinya in shafata in roqi Allah yayi gaggawar tona miki asiri ki tattara ya naki ki barmin gida gayyar tsiya gayyar na'ayya"
"Allah baya bacci" Zubaidan ta sake fada daga haka ta shige dakinta. Tana zaune Audu ya shiga ya zauna akan Kujera yana fuskantar ta, irin zaman da yayi yass gabanta ya shiga faduwa, cikin kaushin murya yace
"Zan sake tambayarki bana buqatar qarya ko wani alaye ki fada mun gaskiyar magana Cikin da kikace kin zubar dagaske kike ko kuwa kwantar dashi kikayi?"
Kuka ta fashe dashi ba tareda ta sgirya ba tace
"Yanzu ka dauki maganar da take fada dagaske kenan? A ina ka taba ganin an kwantar da ciki? Idan ma anayi tayaya ciki ze kwanta tsayin sama da shekara daya a Jikina ace baka lura ba wai me yasa akai baka amfani da kwakwalwarka se abinda matarka ta kitsa maka ba tareda bincike ba ka hau kai kawai ka zauna?"
"Nine bana amfani da kwakwalwata?" Ya fada yana nuna kansa, a duk maganganun babu abinda ya tsinta se wannan, ta miqe cikin kuka tace
"Kwarai, kwakwalwarka hotoce Audu domin bata aiki se abinda wani ya kitsa maka dashi kake tunani. Ya za'ayi ka kasa tantance gaskiya da qarya? Se yaushe idonka ze bude ka gane tuggu da makircin da matarka take shirayawa a cikin gidan nan? Ta laqawa uwargidanka sharrin Kisa shine zata shegantaka maka Da ko Ya ka hau kai ka zauna?
To wlh na gaji bazan iya wannan rayuwar ba, ba zan zauna da mutumin da besan daidai ko abinda ya kamata yayi a matsayinsa na Namiji ba, bazan cigaba da zama ace Kishiya ita zata tsara mun irin zaman quncin da zanyi a cikin gidan aurena ba.
Ka fito fili ka fadi abinda yake ranka ka fadi cewar kana kokwanton cikin jikina karka sake sakayawa ko ka titsiyeni da tambayar abinda ya shafi rayuwata ta baya, ka fadi kai tsaye Matarka ta kitsa maka cewar cikin jikina ba naka bane kuma ka hau ka zauna babu abinda zance maka kuma banida amsar da zan baka a yanzu se dai nace maka mu jira lokaci, ubangijin daya wanzar da samuqar cikin ze qarware duk wani qulli da ake qoqarin laqaba masa amma kafin nan ka sani bazan iya cigaba da zama da kai ha Audu gidanmu zan tafi zanje na qarasa rainon cikina a can har Allah ya saukeni lafiya abinda na haifa ya raba gardamar zargin da kake neman laqabamun" tana gama fadar haka ta shige daki tana Kuka ta hau hada kaya.