Sashe 127
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A maimakon ta sassauta se maganganunsa suka sake ƙukar da ita, ta tsani Namiji da bashida ra'ayin kansa se abinda mace tace yayi wannan yana daga abinda bata so da Ahmad yanda yake mata wani lako lako kamar ita ce Namijin shine macen, to tun yanzu baya iya taɓuka komai daga abu ya haɗa m
Su ya fara kamar zeyi kuka yana lallaɓata idan sunyi auren kenan baze ringa tsawatar mata ba idan tayi masa laifi. Haɗuwarta da Jay tasa ta ƙara fahimtar banbancin Namiji da muna Maza, duk yanda yake nuna So ta yake riritata idan tayi masa abinda be gamshe shi ba murɗewa yakeyi ita ce zatayi ta lallashinsa da ban baki kafin ya sakko kamar dai yanzu daya yi fushi saboda bata maida hankali akan Exam ɗinta ba ta tabbata da Ahmad ne tsayawa zeyi yana lallashinta akan tayi kaza ko kartayi.
"Dan Allah Fatima ki tausaya mun. Na sani bakya sona Alfarma kike mun ina roƙon da ki daure kici gaba, ki dubi kalar jarabawar da nake ciki ta Sonki ki tausaya mun. Wlh Fatima da zan iya da tuni na cireki daga raina na rabu dake, koda baki taba buɗe baki kin gaya mun ba nida kaina nasan bakya sona kina kulani ne kawai saboda wulaƙnta ɗan Adam ba tarbiyyarki bace kuma na gode da hakan. Bazan gaji da roƙonki na akan ki bani dama, ki bude mun zuciyarki ko yaya ne in Allah ya yarda ba zakiyi nadamar tarayya dani ba" Ahmad ya sake faɗa a sanyaye.
Zuciyarta tayi rauni da jin abinda ya ke cewa, wato shi da kansa yasan bata sonsa amma ya gaza haƙura da ita tashi jarabawar Sonta ita kuma tata Son Jay Allah kenan.
Ajiyar zuciya ta sauke na shaking tace
"Nifa Ahmad ba haka bane ba, na gaya maka exam mukeyi ina buƙatar isashshen lokaci saboda nayi karatu shiyasa duk wani waya da wani chat na ajiye su amma mun kusa gamawa nan da Three days In sha Allah".
Yayi murmushi da jin abinda tace shima yace
"Ranar Thursday kenan zaku gama?" Ta yatsina fuska kamar yana kallonta tace eh, se ya sake cewa a sanyaye
"To yaushe zaki dawo Kano?"
"Paper safe ce, in har na gama komai kafin 12 ma zan taho a ranar in Allah ya yarda"
"To nazo na ɗakko ki?" Ya faɗa da sigar roƙo kamar wani me magana da ogarsa a gurin aiki, bata san sanda tsaki ya subuce mata ba tace
"Zan dawo da kaina, kasan Baffa ya hana ai ka ringa barin aikinka kana tahowa hidimata".
"Dan Allah Fatima karkice Aa kar kuma ki jingina maganar nan da Baffa sedai idan bakya sone kawai sena haƙura" ya sake faɗa gwanin ban haushi kuma ban tausayi kamar ze mata kuka, babu yanda ta iya haka ta yarda akan yazo ya ɗauketa, ita kanta zata ji daɗin hakan saboda hutun Session ne zata tafi da duka kayanta.
Ya ringa zabga mata godiya kamar wanda tayiwa kyauta daga ƙarshe sukayi sallama bayan ya sake roƙarta akan dan Allah ko sau ɗaya ne a rana idan ya kirani ta ringa amsawa gaisawa kaiwai zasuyi baze ja mata lokaci ba tace Toh.
"Allah sarki Ahmad, wlh yana bani tausayi na daɗe banga soyayya me zafi irin wadda yakeyi miki ba Afeeyah,dan Allah ki tausayawa mutumin nan yaci Albarkacin so wlh na tabbatar ba zaki yi nadamar auransa ba saboda yana sonki" Badar ta faɗa, Afeeyah ta hararaeta tace
"Kyaji da fuska biyunki anjima idan Jay ya kira waya jikinki na rawa zakiyita karaɗi kina bashi assurance na ze sameni ke ga campaign coordinator kuma se na gaya masa abinda kike cewa yanzu"
"Amma Thruth to be told Afeeya wlh Ahmad yafi sonki, ki gani fa shekara biyu yana binki kina jansa a ƙasa na tabbata Jay baze ɗauki haka ba Mace ta ringa wasa dashi kamar wani Toy, da yanzu ya daɗe da sallama ki" Badar ta sake faɗa. Afeeyah ta tashi zaune daga kwanciyar da take tace
"To ai banbancinsu kenan shi yasan mutunchin kansa baze zauna a ringa wulaƙantashi akan abinda yafi ƙarfi ba shi kuwa Ahmad kamar mara zuciya ke nifa ba zan auri Mijin da zan ringa juyawa ba ga yan uwansa basa sona naje ana wulaƙantani baze iya tsayawa ya kwatar mun yanci ba".
Badar tayi kasaƙe tana kallonta amma ta haɗiye abinda tayi niyyar cewa ta canza maganar da wata tace
"Yawwa, nikam kinsan Familyn Jay ne?" kai ta girgiza mata tana cewa
"Aa, me yasa kika tambayeni?"
Tayi ajiyar zuciya zata yi magana kenan Ummi tayi sallama ta shigo, ciki ciki ta amsa fuska a ɗaure Badar ce ta tambayeta ya Exam ita kuwa ta zari Bucket ta fita dan tun daga ranar da Islam tace mata tana faɗar maganganu akansu ta washsheta, bata son munafukin mutum, idan ta yarda dakai kayi breaking trust ɗinta shikenan kuma.
A gurguje tayi wanka ta shirya dan har Badar ta shirya zata fita Library tace ta jirata suje tare. Maganar da suka fara ɗazu na rantaso take taji dalilin daya saka Badar ta tambayeta ko tasan Familyn Jay dan yanayin da tayi maganar ya nuna akwai wata a ƙasa. A Frizlers sukayi Lunch, tana kallon Badar dake ƙarasa cin abinta tace
"Ɗazu kina tambayata akan Familyn Jay?" tasha ruwa ta goge bakinta kafin tace
"Oh yah nace kin san wani abu akansu kuwa?"
"Nace miki ai ban sani ba, wani abu ne ya faru kuma?" Ta tambayeta tana yatsina fuska, Badar ta gyara zama tace
Ranar Monday da naje office din Yah Sani (Abokin Yayantane ta ne da yake Lecturing anan) kinsan na gaya miki na taɓa ganinsa sunyi hoto da Jay sanda yaje Masters Uk hoton na office ɗinsa shine ina zuwa da na gani maganarku ta faɗo mun a rai nave masa two weeks ago Jay yazo school ɗin nan, he was suprised yace mun wai ya akayi na sani, then i told him about your encounter kinga mamakin da yayi kuwa? Ashe Mamansa da Maman Jay cousins ne shima suna bala'in shiri sosai gurinsa ma yazo nan Zaria kwanan sa ɗaya ya wuce babu wanda ya san yazo dan da daddare ya shigo kuma a gidansa ya sauka da safen daya fito ma be san inda yaje ba kuma harya tafi babu wanda yace masa ya ganshi then he asked me wai waye Dad dinki a Nigeria da har Jay yace yana sonki?"
"Ban gane ba?" Afeeyah ta katseta fuskar ta na nuna alamar confusion, Badar taci gaba da cewa
"Nima abinda nace masa kenan, to cut the story short Afeeyah abinda na fahimta Mamarsa yar Jari hujja ce, Yah Sani ya gaya mun Jay personally bashi da matsala, and tunda yace yana sonki dagaske yake yi amma inda matslar take mawuyacin abune Mahaifiyarsa ta yarda ya aureki saboda a duniya idan da akwai abinda ta tsana be wuce Talaka ba. Yaranta auran Jari take musu kuma babu wanda ta ɗora buri akansa Irin Jay saboda tafi sonsa duk cikinsu matsayin da yakai yasa ta tattara duk wani burinta na duniya akan matar da ze auro, ita a sonta cikin turawa ko larabawa zeyi aure ai kinsan Shahida Anchau ko?" Ta jefo mata tambaya, ruɗu da tashin hankalin da ta shiga yasa dakyar ta ɗaga mata kanta da yayi nauyi Badar taci gaba da cewa
"To Mamansu babu yanda batayi akan a haɗa auransu da Shahida ba kinga dai Abbansu kafin ya rasu yayi kuɗi kamar me kuma har yanzu Mamansu kanta tana da kuɗi amma wai Maman Jay taƙi, ba Shahida kaɗai ba yace a Familynsu babu daga gidan da ba'ayi masa tayin aure ba amma taƙi bari ya karɓa. Ki ga dai Familyn ANCHAU duk Kaduna babu wanda be sansu ba saboda tsofaffin kuɗine, arziƙinsu tun duniya na kwance har jikokinsu ba lallai suyi talauchi ba amma Mahaifiyar Jay ta raina su tace bataga yar da ta dace da shi a ciki ba. Ni wlh mantawa nayi ma tunranar ban gaya miki ba se yau abin ya faɗo mun a rai nace masa ma zamuje tare ya faɗa miki da kansa kafin ki ce hassada nake miki ko ƙarya na shirya saboda na rabaki dashi".
Ƙasa Afeeyah tayi da kanta tanajin wani abu nayi mata yawo tsakanin ƙirjinta da maƙoshi yaƙi wucewa yayi ƙasa kuma yaƙi haurowa ya fito. Wato kallon yar masu ƙumbar susa Jay yayi mata saboda ya ganta fara ƙal kalar madara ya shaƙi ƙamshin designer turare a jikinta ga Hijabin Crep yard da Ummu-Maheer tayi mata ze tsammaci irin yan Turkey ɗinnan ne ko Egyptian shiyasa yake sonta?
Kenan wannan ne dalilin da ya saka yake yawan kawo mata labaran ƙasashen duniya idan ta nuna bata sani ba yace wasa takeyi masa? Bata manta ba ranar nan suna maganar kallon Ball da tace masa Badar na kalla a waya yace me yasa ita bazata kalla ba tace masa kawai, se yace ta roƙi Dadynta wannan Holiday ɗin suje Muje London ta kalli wasan sa Live har take ce masa ita Baffa ne da ita ba Dady ba kuma wace London ita da ko Aiport bata taɓa zuwa ba ya ringa dariya yana cewa ta raina masa hankali kenan kallon yar Masu kuɗi yake mata irin wadda Mahaifiyarsa take da burin ya aura lallai kuwa an yanka ta tashi.