← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 137

Sashe 50

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah yasa lafiya dai Hajiya keda kanki kika zo gidan nan idan wani abu ne aida se ki aiko a kirani" Lantanar ta sake fada. Cikin muryar qunquni ba tareda ta kalleta ba tace
"Lafiya lau, zaman gidan ne ya isheni shine na fito"
"Ai to barka, kuma ke kikace na taho da wuri yau ai da yanzu ina can na tayaki hirar to ina wuni?" Cewar Lantana sauran matan da se sannan suka iya magana duk suka gaisheta.

"Bari naje Lantana inaga su Shamsiyya sun taso daga Allo yanzu, mace daya ta fada se dayar ma ta miqe tana cewa
"Bari na biki ki lallabemun kan nan nawa, Lantana Allah bamu Alkhairi"

"Duk tafiya zakuyi? To ku gaida gida nagode" Lantana ta fada ta na miqewa ta taka musu. Binta na zaune tana qarewa tsakar gidan Lantanar kallo yanda kasan wani filin baje koli can kwanukan wanke wanke can kayan yara sun cire sun zubar a qasa harda zannuwanta ga abinci da akaci aka zubar ba'a kwashe ba banda tiqar rake da qutsirarrun Kara gurin murhunta kadai abin kallonne.

"Bari na kawo miki ruwa Hajiya" Lantana ta fada Binta ta kalli Randarta ta kalli Lantanar kafin ta zabga tsaki tace
"Kika ce mun Mijinki yana aikin Malanta ko? Yana ina? So nake a karyamun duk asirin da waccen tsinanniyar tayiwa Audu a yau nake so ba se gobe ba ta yanda ze mata korar kare ta tafi gidansu komai dare"

"Tirqashi" Lantana ta fada a zuciyarta a fili kuwa seta gyara zama tace
"To yanzu kin hau saiti kenan Hajiya"
"Da ba a saiti nake ba? Karki gayamun magana Lantana saboda kinga nazo gidanki, ki kiramun shi ayimun aikin da yake gabana ba surutun banza nazo muyi ba"

"Allah ya baki haquri Hajiya nima ba surutu nake miki ba, amma yanzu dai Malam baya nan ya tafi qauye kuma kwana uku zeyi a can, da ace jiya kikazo da zaki tarar dashi amma da akwai Mijin qawar nan tawa da suka fita yanzu shi yana nan a gida Malam me makarantar Allon nan ta kan kwanar shigowa idan kina so yanzu sena rakaki gurinsa duk abinda Malam zeyi miki shima irinsa yakeyi" Lantana ta fada cikin ladabi. Binta tayi shiru na wani lokaci, zata so ace a yau din nan an karya mata duk wani Asiri da Zubaida tayiwa Audu amma kuma bata son terere, shima Mijin Lantanar data zo gurinsa saboda tasan zatayi komai cikin sirri ne Lantanar ba zata fitar mata da sirri ba wannan da take fada kuwa bata da tabbas a kansa dan haka ta nisa tace

"Jibi kikace ze dawo ko?"
"In Allah ya yarda Hajiya"
"Shikenan, bari naje na dawo" ta fada tana miqewa tsaye, Lantana taso ta jata da wata maganar ta zauna ko Allah zesa taji yanda ake ciki dan daga ganin idanun Bintan da kuma kawo kanta da tayi gurin Mijinta da tayi mata Qaryar yana aikin Malanta tun farkon fara aikinta a gidan tasan banza bata kao zomo Kasuwa kuma duk abinda ya koro Kifi daga ruwa ya fada wuta toh tabbas yafi wutar zafi, zata so taji komenene dan ta samu na yamadidi a unguwa kamar yanda ta saba raba zancen Bintan lungu da saqo a unguwar amma yanzu babu fuska dole ta haqura ta rakata zaure tana jaddada cewar Jibi da Malam ya dawo zata sanar mata.

"Ko na biki na tayaki zaman ne Hajiya?" Bata dai sare na ta fada, Binta ta mata Banza tayi gaba. A maimakon ta tafi gida kai tsaye seta bige dabi ta wancan lungun ta bulla wancan seda taji ana kiraye kirayen sallar Magriba kafin ta kama hanyar gidan ranta na quna da tunanin me zataje ta tarar, tana shiga Soro hawaye ya balle mata, wai yau ita Binta ce gidan Audu ya gagareta zama har ta fita tana garari a titi saboda qata Mace? Wlh bata isa ba, taci alwashin seta tozarta Zubaida, yanda ta kori Bara'atu Salin Alin haka itama zata fita ta bar mata gida, Audu da duk abinda ya mallaka nata ne wata mace bata isa tazo ta mata katsalandan a sabgarta ba.

A tsakar gida sukaci karo ya fito da Alama masallaci zeje,
"Kin dawo? Ga Alhaji can an maidoshi bakya nan yana gurin Yar Dagwas" Audun ya fada mata kafin ta bashi amsa ya rabeta ya fice daga gidan dan har an tayar da sallah. Kamar kububuwa ta doshi dakin Zubaidan babu sallama.bare neman iso ta bankada labule ta fada ciki.
"Wane Dan abu ta kazan ne ya baki izinin taba mun yaro? Dana tsarkakakke zaki shafa masa Dattin zina? To bari kiji karki dauka kinga gurin zama a gidan nan, yanda kika shigo da qafa biyu idan bakiyi wasa ba sedai a kwasheki a wilbaro dan sena karairayaki na zubar. Se kinyi nadamar auran mun Miji, sena illataki yanda ko kin koma yawon Karuwancin naki ba zaki samu masu tayawa ba, bani Dana, kuma ki fito ki doramun abincin dare yanzun ba se anjima ma".

Zubaida na tsaye da goyon Zakariyya wanda yake ta rigima tunda wata yarinya ta kawo shi daga gidan da Binta take kaishi raino yana ganin Audu ze fita kuma ya saka kuka wannan yasa ta goyashi harya rufe ido da alama daman rigimar bacci ce hargagin uwarsa ya tadashi. Kwanto mata danta tayi ta direshi kan Kujera, Binta ta fizgeshi ya saka kuka saboda yanda taja hannunsa ko tsoron yaji ciwo batayi ba ta fara jansa tana cewa
"Kinji abinda nace ai karki bari na maimaita miki"

"Bana tsammanin yace miki ya miki bayanin ni wacece a gidan nan, to idan beyi miki ba ni yanzu bari na gaya miki. Yanda kike matar aure da aka auro da sadaki nima haka nake, matsayinmu daya na yar aiki ko me dafa abinci aka kawo miki ba dan haka ke baki da qarfin ikon da zaki sakani na dafa miki abinci a gidan nan kici, idan kinga haka ta faru to Mijina ne ya bani umarni wannan kuwa zanyi saboda shidin shugaba nane, kuma neman Aljanna ya kawoni gidansa bazan tsallake umarninsa ba muddin be sabawa shari'a ba" Zubaidan ta bata amsa kafin ta angizo daurin dankwalinta gaban goshi tace

"Karuwa kuma bakiga komai ba daga cikin halinta, ki saka ido ki gani, tsakanin nidake za'aga wadda zaman gidan nan ze gagara" tana gama fada ta wuce cikin daki tana kada jiki tabar Binta tsaye baki a sake, seda ta bugo qofa kafin Bintan ta farga ta fara dura mata Ashar tana cewa idan ta isa ta fito ta gani seta sauke mata rainin da take taqama dashi yau, ta gama hayagagarta taja Zakariyya suka wuce daki tana cigaba da bala'i kamar tsohuwar karya.

Zubaida kuwa Alwala ta daura tanayi tana kuka, a duk sanda aka kirata da Karuwa takanci ciwon abin yanda bata taba tsammata ba. A sanda take cikin rayuwar Alfahari take da sunan amma yanzu tana jn muninsa fiye da misali. Yanzu haka za'a ringa alaqanta yayanta da wannan mummunan sunan?
Bayan ta idar da sallah bata tashi ba har akayi Isha'i ta dora shafa'i da wutri tayi addu'a kana ta nade abin sallar ta tashi. A gurguje tayi wanka ta shirya, cikin irin dinkunan da Kilallu irin tane a wancam zamanin ta saka riga da siket daya matuqar kamata ta baza qamshi ta ko ina sannan ta kafa dauri a gaban goshi.

Audu ya gaya mata kartayi girki ze shigo musu da abinda zasuci dan haka ta dora ruwan shayi baqi ta zuba kayan qamashi sannan ta dauki Kankanar data hada tun yamma tashanye ta koma falo ta zauna bayan ta kunna waqar Aliko makaho tana bi hankali kwance tana gyada kai.
"Baki a washe kamar wawa Audu ringa binta da kallo sanda ta karbi ledojin Kaji da kayan Marmarin daya shigo dasu,
"Aa kaga yar dagwas, irin wannan Ado haka gaskiya kinci sunan naki na yar dagwas" ya fada yana washe mata haqora. Ta dan bata rai irin na shagwaba dukda tace

"Nace maka bana so ka canza mun wani sunan amma banda wannan" har ranta ta tsani sunan a yanzu amma bata so ta nuna masa hakan cikin fushi ko fada, ya zauna yana sake ce mata
"Barni kinji, dadi sunan yake mun. Je ki kawo faranti muci Naman nan tun da zafinsa".

Ta wuce Madafa tana juya mazaunanta da basufi rabin na Binta ba amma da yake ta iya sarrafasu bala'in dauke masa hankali take idan tana tafiya. A da gani yake ba Macen data kai Binta iya gwalangwaso da kisisina wannan abin ya qara dakusar da Bara'atu a idonsa yaji sam ta dena birgeshi saboda bata ko kamo qafar Bintan ba babu abinda ta iya se wanda ya koya mata amma yanzu daya auro Macen gaske se yaga ashe duk wani sanaben Binta sharar fage ne, wato jiya yaje cloud 9, yaga abinda ya dauka a gurin Hurul'ayni matan Aljanna kadai ze samu yanzu ita kanta Bintan ganinta yake kamar shi dan yanzu ne ya tabbatar ya auri Mace.

Yana can lissafin ta dawo, yanda take duqawa ta ajiye kayan ma abin birgewa ne sannan ta kalle shi tayi masa wani farrr da ido se yaji kamar ze suma dan dadi.
"Ina na Maman Zakariyya? Kona kirata muci tare?" Ta fada tana bude ledojin.

Ya sauka qasa ya zauna yana cewa
"Ai tana da Kaji a firinji, kema gobe za'a kawo miki saboda ajiyar Danyan Nama da sauran kayan amfani" ya bata amsa yana daukar kofin data tsiyaya masa baqin shayi a ciki kurba seta shagwabe fuska tace

"Haba dai, ya za'ayi muna gida daya ka siyo abu muci mu kadai banda ita da yaronmu? Aa gaskiya bari na dibar mata dan wannan ai ya mana yawa Kaji biyu Manya ina zamu kaisu" taja faranti ta fara dibar Naman, wata qaramar Leda da taji dumi ta bude taga Tsirene a ciki ta aika masa hararar qasa tace
"Harda tsirema duk a wane cikin zamu zuba mu kadai?"

*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*

*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓
Chapter 50 · 0% Book details