Sashe 108
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kwana na uku ina yawo cikin makarantar nan, na kasa samunki a waya, idan na canza layi na kira ki da kinji muryata seki kashe daga ƙarshe kindena Amsa duk wata number dana kira da ita why Fatima? So kikeyi zuciyata ta buga na mutu kowa ya huta? Dame kike so naji? Da Matsalarki koda rigimar Jafar? Wlh ko ki tsaya muyi magana yanzu ko kuma ba biki har cikin Hostel, Bet me I'm fuc***g serious zaki sha mamakina yau".
Kuka Fatima ta fasashe masa da shi kawai ta zauna tareda kwantar da kanta akan Table ta shiga rera shi. Ahmad ya zauna ya harɗe hannaye yana kallonta ba tareda ya hanata ba. Badar kuwa saya karɓi order ta tafiya tayi Hostel.
Seda Fatima tayi kuka me isarta Ahmad na zaune ya na kallonta kafin ta tsagaita ta fara zazzage masa abinda yake ranta wanda Jafar Bechi yaci ace ta gayawa sanda yake zaginta amma ta huce akan Ahmad ɗin.
"Kiyi haƙuri dan Allah kuma ki manta duk wani abu daya faɗa shima cikin fushine and he regretted everything he said, zan haɗaku a waya ze baki haƙuri komai ya wuce" Ahmad ya faɗa kamar zeyi mata kuka.
"Ni na haƙura sannan kaima na haƙura dakai, Brother ka ya gaya mun what i need to know about your Family, na sani daman ba zasu soni ba saboda ni Talaka ce amma ka sani ka kuma gaya masa tabbas mahaifina Talaka ne amma ba Matsiyaci bane domin yana da wadatar zuciya kuma sana'ar sa da yake zagi Halal yake nema Haram ba sannan ba yawon Maula yake gurin wasu mutane ba balle ya samu damar zaginsa ya Ƙasƙantar dashi. Nasan mutunchin Iyayena dan gaka bazan bari wani ya taka darajarsu ba, ko beyi rantsuwar bazan Aureka ba na rigada na yankewa kaina wannan shawarar sannan ka gaya masa Maita daya dangantamu da ita, nasan ko nayi shari'a dashi a duniya ba za'a bi mun haƙƙina ba saboda shi ɗan masu kuɗi ne amma zamuyi shari'a a Katun da ba'a bada cin hanci" ta faɗa sababbin hawaye na sauko mata.
Duk yanda Ahmad ya zata abin ze zo masa da sauƙi ya zarce haka, taurin kaine da ita kamar mutanen farko ta riƙe maganganun Jafar Bechi se maimaitasu takeyi.
"Amma Fatima ko Allah daya halicce mu baya kama wani mutum akan laifin da wani daban ya aikata muddin ba sunyi tarayya a cikin aikata laifin ba. In har akan Abinda Jafar yayi miki ne na baki haƙuri kuma in har zakiyi mun Adalci kin san bani na sakashi ba, ki faɗi kanki tsaye cewar bakya sona, ba kya Ƙaunata kawai dan rajin kanki ba saboda abinda Jafar yayi miki ba. Na dade da fahimtar haka, amma na kasa cire rai dake bansan me yasa zuciyata ta kasa haƙura dake ba, ina Addu'a akan Allah ya zaɓa mun mafi Alkhairi a kullum kuma ji nakeyi tamkar ana Ƙaramin sonki, duk yanda nakeji akanki wlh zan jure kuma zan roƙi Allah ya yayemun muddin kika furta da bakinki bakya Sona ba kuma zaki aureni ba nayi miki Alƙawarin daga nan gurin ba zaki sake gani na ba zan kuma fita daga rayuwarki koda Sonki ze zama Ajalina zan haƙura dake Fatima".
*************
A YEAR LATER
Gudu gudu sauri sauri take tafiya saboda ta kusa makaraz fata takeyi Allah dai ya rufa mun asiri ta samu ta shiga Ajin nan kafin Dr Abolude ya rufe, ba rasa ajinsa ba wannan banzan halin nasa na marking note se kace a primary ko secondary school shine abinda yake bawa kowa haushi dashi balle ita yau da rubutun ya zamar mata biyu, ga nata gana Badar dole taje da wuri ta samu sit a gaba, layin wanka ne ya bata mata lokaci saboda Monday ce kusan kowa na block dinsu nada Ajin safe.
Qiris ya rage ta hantsila daidai Basket ball court saboda wani mutum da tun fitowarta daga Amina Hall ya zura mata ido kamar me shirin ganin yayan hanjinta, taja tsaki ta dauki Jakarta data zame ta fadi a ranta tana mitar wannan kallo haka taci gaba da zabga sauri a karo na biyu ta sake yin gaba tana shirin gangarawa daidai Senate building saboda mutumin dazu data gani tsaye gabanta kamar Aljani. Batasan sanda ya biyota ba harya tare mata hanya, zuciya ta harziqomata amma bata tankashi ba ta sake rabeshi ta wuce a kato na biyu se ji tayi daga bayanta ance
"Sihh, jimana yammata". Raita ya ninka da baci, a duniya idan akwai abinda ta tsana be wuce irin wannan kiran wulaqancin da maza sukeyiwa yammata ba, se kace wata mota ko Mashin a ringa maka wani Sihh wasu tantiranma har fito suke kamar masu kiran kare. Taci gaba da tafiyarta kamar zata tashi sama ga haushin mutumin ga na bata mata lokaci da yake tayi dan ta tabbata yanzun kam ta makara sedai ta maqale a bakin window idan batayi sa'a ba. Karo na uku ya sako fadowa gabanta, wannan baƙar ɗabi'a ta mutumin da abin takaici take baya ko tunanin zata iya faɗuwa tunda batasan da shi ba ya ringa diro mata kawai kamar wani jifa.
"Dan Allah ki saya" ya faɗa yana kallonta se a sannan ita ma ta kalleshi fuskarta babu alamar rahama amma can ƙasan ranta seda ƙirjinta ya buga saboda se yanzu ta kalleshi da kyau. Wani zabgegen mutum me ƙirar ƙarfi jiki a murɗe dan a yanzu da yake tsaye gabanta shigarsa ta nuna motsa jiki yakeyi, rigace Armless jikinsa da wandonta wanda da kaɗan ya zarce guiwa kayan suka qara bayyana surar ƙarfinsa, bata tantance fuskarsa ba dan bata kalleta sau biyu ba, yanda ya kankane mata hanya yasa ta raina kanta da tsahon da take taƙama dashi dan wata yar firit ta ganta a gabansa.
"Afuwan, Assalamu alaikum" ya sake faɗa da sautinsa daya sa ta gaza tantance wane yare ne shi, sake daga kanta tayi ta sake kallon fuskarsa, a zubi za'a kirashi Bahaushe ko kuma Hausa Fulani amma a zubin jiki dai yafi kama da Irin zabga zabgan Igbiran nan ko Inyamurai haka fatar jikinsa da take da haske dukda ba fari bane amma a goge take tar yanda kasan ya hada jini da fararan fata.
Tsaki ta zabga data kalli sumar kansa da tasha gyara irin na Yan Ball din nan itako yana daga irin abinda ta tsana dan duk girman mutum idan ta ganshi da irin Askunan nan kallon wanda be san kansa take masa ba. Tuna abinda yake gabanta yasa ta kauce ya sake tareta yana cewa
"Nayi sallama kin bini da tsaki ki amsa mana Ammata" ya faɗa da wata cukurkudaddiyar hausa yanda kasan wani Yare yake.
Tsakin ta sake masa tayi baya a tsiwace tace
"Ka matsa Malam ni ina da abinyi"
"Zan masa amma se kin mun abu uku, firstly ki amsa sallamata dan wannan dolene a musulunci kinsani then you tell me your name, lastly you give me your digits" ya ƙarasa yana irgawa da yatsunsa. Harara ta galla masa amma yanda ya bake hanyar tasan ko tureshi tace zatayi ko gezau bayi zeyi ba kuma duk inda tayi binta yake wannan yasa ta amsa masa sallamar a ƙufule tana cewa
"Se ka matsamun na wuce Malam tunda na amsa maka sallamar ai"
"Ai baki cika sauran sharuddan ba" ya sake faɗa se tayi saurin tareshi da cewa
"Nayi wanda zan iya"
"Baki isa ba, na miki rangwame cikin biyu you choose one, either you tell me ur name or you give me your contact, barshima, bari sunan, bani number kawai" ya faɗa yana miƙa mata wata tsadaddiyar waya da bata taɓa ganin irinta ba. Ta harareshi taa harari wayar tana cewa
"Ashema kai zaka zabarmun abinda zanyi? To sunana Afeeya, dan girman Allah ka matsa ka bani hanya dan ka rigada ka makarar dani"
"Kince Allah wuce Afeeyah, suna me kyau kamar yanda kike da kyau" ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi ya harɗe hannaye a Ƙirji yana jifanta da wani kallo.
Tuni tayi masa nisa, a jikinta taji har sannan yana biye da ita bata waiga ba har ta shiga Department dinsu ta sauke numfashi ganin yan Ajinsu a waje suna hirarraki alamar Malamin bezo ba, ba tareda ta tsaya ba ta shige ciki abunta dan zuciyarta wani bugu take kamar wadda tayi tseren gudu.
Ta wutsiyar ido ta kalli window inda taji alamar idanun mutum akainta, yana nan tsaye kuwa ya harɗe hannayensa a
Ƙirji damatsansa sun ƙara fitowa kamar an aje duwatsu se tayi sauri maida kainta kan desk tana jin yanda zuciyarta take tsere, bata dade da zama ba Malamin ya ƙaraso, ya ringa zabga dictation suna rubutawa ajin awa biyu ne amma tsabar mugunta ya roqi next Lecturer da ze shigar musu ya ara masa lokacinsa tun takwas da wasu mintina bamu muka samu kanmu a hannun Dr Abolude be barsu ba se sha biyun rana zuwa sannan hannun kowa ya sage nata kam har sun kumbura gefen inda take riƙe da biro sunja ruwa daman haka yake mata duk sanda tayi dogon rubutu tofa se tayi jinyar hannu abinka da Jiki duk Madara inji Qawayenta.
Taimakon da Allah yayi musu da yace ba lokacin ze karbi note din ba Class rep ya hada ranar Wednesday ya kai masa kuma shine CA dinsu, tayi hamdala a fili dan rubutun nasu rabi da rabi tayi, idan tayi nata se ta kama na Badar duk a tsoron kar a tashi karɓa ta rasa gara ko yayane dai ta rubuta mata wani abu.
A mugun gajiye ta wuce Geography mosque dan Azahar ta kawo kai gara ta tsaya tayi sallah kafin ta koma Hostel ta ɗan kwanta zuwa La'asar suna da wani Ajin. Seda tayi alwala ta shiga cikin masallacin tayi Nafila raka'a biyu kafinta nemi guri saitin fanka ta kishingiɗa tana jin kamar tayi bacci saboda gajiya ga bashin na daren jiya da batayi dakyau ba. Wayarta ta shiga Vibrating ta janyota daga cikin jaka, gaba ɗaya ta sha'afa da ita.