← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 137

Sashe 52

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke! A gaban nawa ma rashin kunya zaki mata? To bari kiji daga yau koda wasa karki sake kullemun qofa tunda dai gida nawane ba na wani ba, sannan dukanku matana ne babu wadda nayiwa shamaki daga shiga dakin wata a cikinku, yanzu kalli ciwon da kikaji mata ji yanda hannun ya kumbura fisabilillahi hakan da kikayi yayi kyau?" Audu fada yana zare mata ido, Zubaida sadda kai qasa saboda kukan dake shirin bada ita tace

"Amma dai tsakani da Allah ba haka ya kamata kayi ba, seka tambayeni abinda ya hadamu tunda dai kaji daga bangarenta"

"Ke zaki tsara mun abinda zanyi a cikin gidana? To banyi hakan ba nace banga damar yin hakan ba koda abinda zakiyi?" Ya hayayyaqo mata seta fashe da kuka saboda takaici tama rasa abinda zata kuma ce masa

"Tashi kije" ya bata umarni yana wani dauke kai dan kukan nata ya tabashi amma shi a dole ta masa laifi shiyasa ya dauke kai. Cikin kuka guiwoyinta a sanyaye ta wuce dakinta. Zubaidan na fita itama Binta ta fashe masa da kuka tana cewa
"Yanzu shikenan ta jimun ciwo taci bulus iyakar abinda zaka ce mata kenan sannan saboda makirci ta fita tana kuka kamar ita aka zalunta?"

"To ya kike so nayi, so kike na rufeta da duka ko kuma na riqe hannunta ki rama abinda tayi miki? Ina kinji dai tace kuskurene?" Audun yayi kanta a fusace, yanda yayin yasa tayi shiru bata kuma cewa komai ba wato tuggunta be samu shiga ba so tayi ya rufe Zubaidan da fadan koma ya falla mata mari koya rufeta ma da duka amma dai ko banza hakan ma babu laifi tunda ya sakata kuka a gabanta da haka zata cigaba da nunawa Zubaidan ita din ba kowa bace a gurinsa Audu, kuma duk yanda ta dama haka za'a sha. Qarawa kukanta volum tayi babu ko dadin sauraro Audu yaja tsaki yace ta tashi suje gurin wani wanzami dake qasansu a duba hannun.

"Wlh ba zani ba idan ba zaka kaini Asibiti ba sedai na zauna da hannun haka kuma gobe karka saka ran zaka fito ka tarar dani a gidan nan Kaduna zan wuce" ta fada cikin kuka. Wannan tasa ya kaita Asibitin suka bata magu gunan rage radadi bayan an mata allurar kashe kwayoyin cuta sannan suka dawo gida lokacin goma harta gota, seda taci abinci tasha magani kafin ya wuce dakin Zubaida.

Tana zaune a falo ta kunna Tv amma hankalinta baya ga abinda ake nunawar tayi nisa cikin tunanin da tunda ta baro dakin Binta takeyinsa. Se taga kamar shari'ar ta Audu ba haka ya kamata ya gudanar da ita ba, tambayarta ya kamata yayi abinda ya hadata da Binta har wannan tsautsayin ya faru bawai ya dora mata laifin matsewa matarsa hannu haka nan ba kuma da yake maganar kowa tana iya shigar dakin yar uwarta babu shamaki a ina ake haka fusabilillahi?

Yanda ya shiga fuska a daure haka tayi masa sannu da zuwa jiki babu karsashi guiwoyinta suka sake sanyi da Al'amarin Audun, to fushin na menene kuma? Ba an gama magana ta wuce ba? Ya gama uzurirrikansa data bashi abinci yace ya qoshi, bata sake tsinkewa da lamarin ba seda ya juya mata baya da sukaje kwanciya a ranta tace lallai abin babbane.

"Kayi haquri in dai akan abinda ya faru jiya ne kake fushi wlh ba ina sane na matse mata hannu ba ita ta biyo ni tana zagina tace zata dokeni ni kuma tsoron haka yasa na shigo na tura qofar bansan ta saka hannunta a ciki ba" Zubaidan ta fada hawaye na saukar mata sanda Audu ke shirin fita da safe ba tareda ya ko kalli kayan karin data jera masa ba.

"Oh, bayan abinda kikayi shine kina da bakin sake magana harda sharri zaki mata a yaushe ta zageki harta biyoki zata dokeki?" Ya fada yana dakatawa daga fitar dayayi niyya. Hawaye suka balle mata na takaici, wato sharri tayi mata? Ita Bintan Allah kadai yasan abinda ta fada masa wato natane gaskiya se ita data fadi ainihin abinda ya faru shine zece ta mata sharri?

Muryarta na rawar kuka tace
"Akan me zan mata sharri? Sannan ai kaima zaka iya bada shaida akai dan ba shibe karo na farko data zageni ba ko tayi yunqurin dukana a gabanka ma anyi shekaran jiya ba kai ka kwaceni daga hannunta ba?" Ta fada tana tsare shi da ido. Yayi jummm alamar ya gasgata abinda ta fada din amma saboda qi fadi da rashin son gaskiya irin nasa se ya murje yace

"Rashin kunya zakiyi mun har kina tsareni da ido kamar wani sa'anki? To bari kiji muddin kina neman zaman lafiya a gidan nan dole ki zauna lafiya dani da kuma matata. Mu bamu saba fadace fadace da kuka iya har ana fidda jini ba a gidan nan dan haka ki san a inda kike" daga nan yasa kai ya fita ya barta tsaye kamar ya dasata tana juya kalamansa.

Ita da suwa suka saba fadace fadacen da zubar da jini?
"A bariki mana yake nufi" zuciyarta ta bata amsa, dabas ta zauna dafe da kunci hawaye suka shiga mata tsere, wato abinda yake nufi kenan, a fakaice yana gaya mata cewar nan ba irin gidan daya dakkota bane kenan da suka saba Fada kamar Kaji suna jiwa junansu rauni Yau Audu da kansa yae goranta mata wani al'amari daya shude a rayuwarta kenan.

Wannan abu yasa gaba daya jiki ta yayi sanyi, sararin data samu ta fara baje kolin sharholiyarta duk karsashin ya barta shima kuma be bi takanta ba yana ta tattalin Binta da hannu ya saka a gaba har ya saukar mata da zazzabi me zafin gaske seda ta kwana uku a kwance kullum kuma is Zubaidan ta shiga ta dubata safe da dare idan yana nan zata amsa cikin sakin fuska idan baya nan kuwa har Lantana samun damar yaba mata magana take suce mata mayya wai ta kama mata hannu to kurwarta kur. Ita Binta ko abinda take mata ma sam be dameta ba irin na Audun, qiri qiri yaba ganin gaskiya amma ya take yabi qarya shin wane irin mutum ne shi haka?

Ya za'ayi rayuwa ta yuwu a haka ace duk abinda aka gayawa mutum walau shine gaskiya walau qaryane se ya hau ya zauna kuma idan ya gano gaskiyar daga baya girkan kai da izza su hana shi karbar kuskurensa ai ko baze furta da baki ya karbi gyara ba se ya nuna hakan a aikace amma shi babu daya daga ciki da yakeyi sedai ya dora fushi wannan ai ba daidai bane. Data lura da gaske fushi yake da ita kuma bashi da alamar sakkowa dan har ranakun girkinta da suka zagayo bacci ke shigar dashi dakinta safiya nayi ze fice dole ta sauke nata fushin ta sake samunsa ranar ta tattara duk wata wayo da dabarar da take dasu ta wanke kanta a gurinsa ta hanyar karban laifin da bata aikata cikin sani ba ta kuma tabbatar masa da ba za'a sake ba har da kukanta tace kuma ya rakata a gabansa ta baiwa Bintan haquri sukaje ta bata haqurin ganin idonsa yasa Binta tace ta haqura ai ita komai ya dade da wucewa a gurinta daman wannan tasa ya sakko daga fushin da yake suka koma zamansu lafiya abinda yayi mugun batawa Binta rai.

A zaman tsamar da sukayi ba qaramin qara samun kan Audun tayi ba, a wayo da dabara take dada kwarkwarashi shi kuma dake kan keke ne ya hau daram ya zauna. Shiryawarsu da Zubaidan se ya zama silar warewar nata shirin musamman da taga kamar Zubaidan ta ganota duk irin tuggun data hada mata a gurin Audun ta dena musawa zata amsa laifinta ta durqusa har qasa ta bashi haquri tana hawayen munafunci a cewar Bintan shi kuma me son girma kansa ya sake fasuwa shikenan kome ta shirya ya wargaje.

Tun daga wannan kuma Zubaidan ta hankaltu duk laifin da Binta ta dora mata zata amsa ta bashi haquri tunda ta fahimci abinda yake so kenan babu ruwansa da jin ainihin magana yanda take hakan kuwa da takeyi ya sama musu zaman lafiya se a dade ba'aji kansu ba idan ba kuma Bintan ta shammaceta ta tunzuro shi ta yanda harta gaza kare kanta ba.

A haka aka kwashi watanni biyar da Auro Zubaida a kuma wannan yanayi ta fara laulayi wanda yazo mata da zafin gaske ga Amai ga Zazzabi lalurori dai iri iri ba qaramin Jiki take ji ba, wannan cikin ya sake gigita Binta, wato Zubaida zama tazoyi ma kenan tunda gashi har tayi ciki ita tana me haka ta faru yama za'ayi Mata suyita haihuwa a gidan Audu Bara'atu tayi biyu ita tana da daya kamar rai kuma a auro wata a bayanta tazo ta goga da ita wannan baze yuwu ba ta shiga takalar masifa kala kala fatanta Zubaida ta tanka mata ta samu dalilin lakada mata na jaki ta yanda cikin zebi rariya tun be gama samun gurin zama dakyau ba sedai bata samu hakan ba, Zubaida da ko a baya bata biye mata ba balle yanzun da take ta kanta.

Abin ya hadewa Binta biyu dan Audun shima yanzu duk ya maida hankali kan Zubaidan sosai wannan yasa ta kasa jurewa ta fiddo haukarta fili take baje musu ita watarana ya tanka mata wata rana kuma ya qyaleta a haka abinda ya sassuta lamarin ganewar da tayi itama tana da shigar ciki saboda batan wata da tayi amma tayi shiru bata gayawa Audu ba sannan kuma cikin Zubaida yayi watanni uku a lissafinsu na daga sanda ta fara laulayi kenan ita kuma nata yana wata daya.
Chapter 52 · 0% Book details