Sashe 121
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Anty ce ta amsa da Amin fuskarta a washe ta tabbata halin nasa yayi musu na Alkhairi, kyautar Ahmad irin wadda Annabi yace ayi ce, ka bayar da hannun dama ba tareda Hagunka ma ta gani ba, ya miƙe yana sake cewa Anty
"Ina Aboki? Dana dawo da safe banshi ba ina sauri shiyasa ban shigi na dubashi ba"
"Ai bama nan ma da wuri na fita ma kaishi Allura seda muka dawo Momy tace ka shigo amma kun fita da Alhaji, yana ciki rigima yake tayi tunda akayi allurar bari Hasna ta kawo maka shi ko zaka shiga?"
"Bari na leƙashi to ance idan anyi allurar ba'aso ana jagwalgwalasu ko ƙila zafi take masa" ya faɗa yana nufar ɗakinta. Tun daga wajen falon kuwa yake jiyo kukan Abdallah Autan gidan a yanzu me watanni uku kuma shine Ɗa na shida da Antyn ta haifa. Babban Ɗanta Musa da suke kira Mu'allim nada shekara goma sha takwas yanzu, se yan biyu mata Husna da Hasna masu shekaru sha biyar sannan Mariya me goma Zayyad me shekaru takwas sai kuma Abdallah data haifa watanni uku baya.
Fadar tashin hankalin da akasha da Hajiya akan cikin nan bata baki ne dan tabbas Allah ya hakunta zuwan sa badan haka ba iyakar baƙin cikin da takaicin da Anty ta ringa sha na Hajiya da gori da cin mutunci akan tazo tana ta zuba yaya saboda taci gado yar matsiyata yaci ace cikin ya bare kota haifi yaron da lalura se gashi Allah ya bata lafiyayyan Ɗa kuma Namiji abinda ya sake gigita Hajiyar ta ringa abu kamar wadda ta zauce, Allah kaɗai yasan da yanda tasha kan Alhaji haka ya saka Antyn a gaba taje Asibiti aka juyar mata da mahaifa wai da shekarunsa rututu ga manyan yaya abin kunya ne ace har yanzu ana haihuwa a gidansa yana haifar Ƙannen Jikokinsa badan Manyan Yayan Alhaji Babannan da Babangida duk Mazane ba da yanzu ma ya fara aurar da jikoki itama Antyn tace daman ko bece ba ta gama haihuwar.
Karɓan Abdallan yayi daga hannun Mariya dake jijjigashi yana cewa
"Ya haka, me yasa yake kuka kuma?"
"Wlh Yaya Hasna ce ta ja masa ƙafar da akayi masa allura wai zata fi saurin saki shine fa yake ta kukan nan". Ahmad ya harari wadda aka kira da Hasna ta sunkuyar dakai kafin yace
"Banda cin zali ya za'ayi kija masa ƙafa? idan ke kikaji ciwo aka taɓa miki ya kikeji hum?"
"Kayi haƙuri Yaya" ta faɗa tana sadda kai ƙasa, yayi tsaki kafin ya juya da yaron ya fita Husna Usainarta tace
"Wlh Naso Yah Faisal ne ko Yah Salim da kinji a jikinki banza muguwa kawai.
A falon Momy da Ahmad ya shiga ta karɓi Abdallah tana cewa
"Meya samu babana tun ɗazu nake jiyo kukansa kuma dai shi baya kukan banza?"
"Wai Allura akayi masa" ya bata amsa bayan daya sake gaiaheta.
"Wayyo, Babana yau ansha ƙarfe, yi shiru kaji kar suyi mana dariya ace tsohona rago ne, Allah ya taimaka bata saukar masa da zazzabi bama zuwa safiya in sha Allahu ze ware" ta faɗa tana zare masa dogon wandon dake jikinsa ta cire masa Diaper da aka matse masa cinya tana sake cewa
"Da gani wannan aikin Hasna ne uwar raino yau kam ai a ɗaga masa ƙafa da wata Diaper a barshi yaji da sagaggiyar cinya" tana cirewa kuwa ya dena kukan ya shiga wulla ƙafa, Ahmad yayi murmushi yace
"Babu baki, ƙila ma duk abinda ya takurashi kenan yake ta kukan haka su kuma basu sani ba, ina Anty Muna badai ta wuce ba?"
"Ka ganni Amadi sallah nayi kai nake jira ka shigo musha hirar yaushe gamo" Anty Maimunan ta faɗa tana fitowa saga Bedroom ɗin Momy. A nan yaci abincin dare tareda Salim da tunda garin Allah ya waye se sannan ya shiga falon ya zauna da Momyn suka gaisa kuma yana gidan wuni sur sallar Juma'a kawai ya fita ya dawo wai bashida lecture a makaranta shine ya wuni bacci. Har gurin sha daya kafin Ahmad yayi musu sallama ya tafi makwanci ransa cike da mamakin abinda ya samu wayar Fatima yana zaunen ya kira yafi sau goma amma still busy ake gaya masa, abin ya bashi mamaki dan layinta akan tsarin call waiting yake in dai wayace da zasu gaya masa sedai idan a DND ta saka wayar ko kuma a kashe take sharrin Network yake ce masa busy, haka ya kwanta duk yanajin babu daɗi ga kewar muryarta duk ta cikashi danya saba koda ba wata hirar soyayya suke ba amma yana jin daɗin magana da ita a haka bacci yayi awon gaba dashi.
FATIMA
Ƙarfe ɗaya harda mintuna suka gama Ajin ranar dan Lecturan nacewa yayi akan se yayi covering abinda ya rage mana sannan yayi fixing musu test ranar Monday saboda Next week ake saka ran fara First Semester exam. Sanda suka fita har an fara tafiya Masallaci, tayi murmushi tana kallon yanda Mazan Makarantar suke tafiya a sahu cikin shiga me kyau a fili tace
"Allah mun gode maka da kayi mu musulmai, dan Allah Badar kalle su, ina son Juma'a a school ɗin nan ranar ne wanda ma baka taba zaton musulmi bane zaki ganshi da Kaftan ya tafi masallaci".
Haka suka ringa hira suna ratsa mutane har suka isa Hostel. A gurguje suka yi Alwala, cikim postgraduate Hostel suka fita zuwa masallacin yau basu samu ciki ba saboda sun makara dan haka a waje sukayi sallar kafin suka koma ɗaki.
Ta kira yan gidansu suka gaisa a wayar Baffa dan har sannan ba'a gyara wayar Ummansu ba, yaran Anty Sauda na gidan ta ɓata lokaci sosai suna magana dasu harda Autar Goggonsu Faɗima da taje gidan hutun makaranta. Tana gama wayar kiran JAY ya shiga, tayi ƙaramin tsaki kafin ta sauka daga kan gado saboda hayaniyar mutanen ɗakin sunyi baƙi Jama'ar Sururat kunsan mutanen Yarabawa badai ɗaga murya ba idan suna magana.
Guri ta samu me kyau ta zauna kafin ta duba wayar yayi mata two missed calls, kusan Minti goma tana jira ya sake kira dan tace ita ba Asararriya bace da zata kira layin waje da Katin Ahmad, harta fidda ran ze kira se ga wayar ta shiga Ringing bata ko tsaya dubawa ba saboda yanda zuciyarta take azalzalarta da son jin wannan muryar tasa ta kai wayar kunnenta sedai Muryar Ahmad tayi mata sallama ba wadda tayi tsammanin ji ba.
A taƙaice sukayi magana dan rabta babu daɗi dalilin ta tsammaci JAY ne, ya gaya mata yana Haɗeja ya kai Alhajinsu Biki dalilin tafiyarsa da sassafe kenan maganar batayi tsaho ba sukayi sallama yana kashewa kiran da take ta zaman jira ya sake shigowa.
Ajiyar zuciya ta sauke me ƙarfi har ranta taji daɗin da ta kasa tantance na menene amma dukda haka seda taja aji wayar na dabda katsewa kafin ta daga
"Hello Baby" ya faɗa da muryarsa me tsinka daskararren jini kota daskarar da tsinkakken to itama dai daskarar da nata jinin yayi dan hatta bakinta ji tayi ya mata nauyi ta gaza furta komai seda ya sake cewa
"I'm sorry, Assalamu alaikum".
A hankali taja numfashi kafin ta amsa masa daga nan ta sakeyin shiru.
Jay dake tsaye gaban Mirror cikin katafaren Bedroom ɗinsa yana taje Quater Million Sajen dake kan fuskarsa yayi ƙaramin murmushi kafin yace
"How are you my love?", zare ido tayi kamar tana gabanshi kafin cikin tsiwa nace
"when did i become your love? Don't call me that again"
"The first time i set my eyes on you, i know you are my lost but found true love" Jay ya faɗa yana ɗaura agogo, fita zeyi, kiran da ya mata bata ɗauka ba shine ya shiga wanka yanzu ya fito yana shiryawa ya sake kiranta.
Baki ta tura amma kalamansa sun mata daɗi, wato da confidence yake komai nasa babu wani ɗari ɗarin irin na Ahmad shi gaba gaɗi yake faɗar abinda yake a zuciyarsa.
"Hey sweet, are you there?"
"Uhm" ta iya furtawa kawai dan ta rasa bakin magana. Ta kasa gane kanta da wannan stranger ɗin, bala'in jin daɗin magana dashi take kusan zata iyacewa a class hankalinta duk yana kan wayar da sukayi da Asuba, bata sanshi ba bata san waye shiba ba amma har cikin ranta ji take kamar sun shekara dubu tare.
"I'm going out, dama na kira ne naji muryarki nayi miki barka da Juma'a, i might be late out though, will you wait for me ba zakiyi bacci ba har na dawo muyi magana?" Jay ya faɗa tamkar me barwa matarsa sallahun ze fita wani guri, mamaki ya sake kasheta amma cikin tsiwa kuma ta miƙe tsaye tana kakkaɓe jikinta tace
"To ni meye haɗina dakai kuma da zanƙi bacci na jiraka?"
"Abinda nake so muyi magana akai kenan, ina so kisan meya haɗaki dani yau" ya bata amsa a tsume jin zata fara masa rashin kunya, wai kuma se shakkarsa ta shigeta harta gyara harshenta tace
"Karma ka kirani dan bacci na zanyi koma zan kashe wayar kawai tunda kai idan ka fara kiran mutane se kace sunci bashinka baka haƙura se an amsa"
"Wait for me please" ya faɗa da taushin daya saka ta ɗaukewa na sakanni, yayi miskilin murmushi, ya gama gane lagonta ba ita kaɗai ba yammata da yawa muryarsa na cikin abinda yake saurin kassarasu shiyasa ya laƙanci salo salo da yake amfani dasu gurin ladaftar da masu kunnen Ƙashi irinta.
"Will you?" Ya sake faɗa da sautin dayafi na farko taushi, tsikar jikinta ta hau zuba, kai ta ringa ɗagawa kamar Ƙadangaruwa kawai kafin dakyar tace masa
"Toh, amma kar yayi dare da yawa"
"Till i call, bye, I love you" ya sakar mata maganganun kafin ya kashe wayarsa. Taji I lobiyu tabi kashi Miliyan amma bata taba jin wadda ta gamsar da ita irin wannna da bata da tabbacin da gaske yake ko ƙarya ya sharara ba.