Sashe 81
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sun isa Asibiti tana tsammatar taga kowa ta kama gabanta dan a zatonta dubiya su biyun zasuje se gani tayi sun nufi bangare daya na yan Awo dan a waje ya ajiye su yace idan yaje kamfani Musbahu and juyo da motar ya jirasu ya mayar dasu gida.
Binta ta ringa binsu tana jira taga abinda ya kawo su gurin Awon ciki sedai daga yanda taga suna gaisawa da Ma'aikatan gurin tasan da sanayya a tsakani suka zauna gurin jira ana bin layi bayan an karbi Katunansu jikinta har rawa ya dauka sanda taga kowa ta zaro kati daga jaka ta miƙa kenan duk cikine dasu bata sani ba? Yaushe akayi? Tana zaman me?
Aka ringa kiran Binta Zakariyya ina bata ma jisu ba tayi nisa a duniyar tunani da zullumi karfa suma duk su haifi Maza dan taga kamar Audu bashi da ƙwan haifar ya mace. Matar da take musu awon ta kallera tace
"Baiwar Allah tunanin me kikeyi haka duk kin firgice kalli fa har jininki ya ɗaga?"
"Kedai kiyi aikinki ki sallameni ina da abinyi" Binta ta gwaɓa mata magana aiko matar ta harziƙo itama tace
"Se nice banida aikinyi ko ai bacci kika ga ina yi yanzu ko rawa"
"Kiyi haƙuri Sista" Hadiza ta tsoma musu baki aiko Binta tayi kanta da masifa ganin a waje suke yasa ta mata shiru se ma'aikatan ne suka haye itama Bintan kamar sa cinyeta Awon da ba'ayi mata ba kenan ta tattara ta fice ta haye Bus se unguwarsu Turai dan tana buƙatar su tattauna wannan matsala ta yaya za'ayi su biyu suyi ciki.
Audu kuwa isarsa kamfani ya tarar da wani mummuman Labari, motoci guda biyar da suka dakko masa Mai daga kudu haka nan wuta ta tashi sun ƙone ƙurmus harda direba guda daya dayayi ƙundunbala saboda motarsa ce ta ƙarsher sun tsaya zasuci abinci Abin ya faru tamkar Tsafi kawai wuta ta kama motar tsakiya kanka kace me sauran sun dauka an hanashi amma ya kafe ya tafi a zatonsa ze iya janye motar kafin wutar ta cimmata se gashi yana shiga ta kama gaba daya se tokarsa aka tattare.
Babban abin al'ajabi kamar yanda aka bashi labari ba iyakacin motocinsa bane a gurin mota tafi Ashirin da suka taho tare duk sukayi fakin suna cin abinci amma ibtila'in akan nasa suka sauka basu taba komai ba duk kuma iyakar ƙoƙarinsu na su kashe wutar abu ya gagara. Hankalin Audu ya tashi matuƙa domin ba ƙananan kudade ne suka narke ba sannan ga Rai da aka rasa. Gaba daya suka ɗunguma gidansu Direban daya rasu me suna Lawan sukayi musu Ta'aziyya, ya bawa Iyalansa kudade masu ɗan kauri da kayan abinci yace kafin su yanke abinda ya kamata suyi musu. Wannan damuwar tasa ya manta da matansa na Asibiti a can kuma bayan sun gama har bayan Azahar shiru Musbahun dayace ze zo ya maidasu beje ba Hadiza tace su tafi kawai ta yuwu aiki yasha kansa ya manta.
Hakan ko akayi suka kamo hanya suka dawo gida, sun sauka a bakin titi Hadiza tacewa Aisha
"Ko zamu ƙarasa gidan Yaya Yakubu dan naji Babansu Baba yace sunzo gari muje muyi Bikon Yaya Balaraba be kamatu ace bama zumunchi da ita ba gaskiya"
"Amma bazeyi faɗa ba?" Aisha ta faɗa cikin sanyinta. Hadiza tayi murmushi tace
"Haba dai gidan Yaya Yakubu ne fa babu faɗan da zeyi kuma tunda ba girki zamuyi ba kinga bamu da matsala da anyi la'asar se mu wuce gida idan ya dawo se mu sanar masa da munje".
Faran faran Balaraba ta tarbesu daman ta dan wayi Hadiza sukan hadu idan tazo gidan Yayarta lokacin da suke can unguwar suma Aisha ce bata sani ba dan bataje gidan ba Yakubun dai yaje yaga Amare da yace suje tace Aa ai bata da sauran dalilin zuwa gidan Audu kuma. Se da sukayi sallar La'asar sannan sukayi haramar tafiya ta hada musu tsaraba cikin abubuwan data zo dasu, Dada da jininsu ya haɗu da Aisha tana ganin sun tashi tacezata bisu
"Ki bari muje da ita idan yaso se Baffansu ya maido ta anjima da daddare" inji Aisha suka tafi da ita.
Sun riga Binta komawa gida itace da girki kuma, sun tarar da yaran sun dawo daga makaranta Abdullahi ya tafasa musu taliya sunci da sauran miyar da yace ya gani a Kicin, shidin yana gida yanzu sun gama jarabawar fita daga sakandire da Audu yace ze fara zuwa kasuwa se kuma yace ya zauna ya huta dan ƙasar qaje yake da burin turashi idan takardar sa tayi kyau.
Binta bata dawo na se guraren biyar da rabi ta shiga gidan tareda Lantana da alama ko ta biya ta gidan tane ta kirata shigarsu babu jimawa Mairo ma tazo ta fara shirin dora abincin dare. Shiru shiru har akayi Isha'i Audu be dawo ba, Binta ta sake cika tayi dam saboda ita keda girki shiyasa yayi zamansa a waje da waccen yar shilarce ai da tuni a gidan ma zeyi Magriba jikinsa na rawa se kace nata Matancin na Gwal ne. Har tara ta buga shiru babu Audu, Hadiza ta leƙa falon Binta dake zaune tana kaɗa ƙafa tana kuma ayyana tijarar da zatayiwa Audu yau idan ya dawo taji muryar Hadizan na tambayarta ko ya shigo.
"Ke matarnan ki fita daga sabgata wallahi tallahi idan kika tiƙeni sena miki abinda bakiyi tsammata ba. Wato kunga gurin zama har kun bude mara kun ɗauki ciki to wlh ku kwana da sanin zaku haifesu a gidajen ubanninku kuwa" Binta ta faɗa tana miƙewa tsaye. Hadiza da fuskarta ke cike da damuqa tace
"Ni ba tashin hankali ya kawoni gurinki ba, gani nayi ya zarta lokutan daya saba dawowa kuma idan ma zeyi dare irin haka yana sanar mana shiyasa hankalina ya tashi. Mijina na fari daga irin wannan fitar shiru shiru se bugamun ƙofa akayi na buɗe aka shigo da gawarsa"
"Keta shafa wannan ni tsakanina da tsohon mijin naki ai Allah ya isa ce da be mutu ba ai da Mijina be kwaso mun ke kinzo kin addabeni ba, ki barmun ƙofar daki kuma Audun ai ba Ji njiri bane da za'ace ya bata" Binta na rufe baki sujai dirar mota mintina kaɗan ya shiga fuskar nan kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa be kulasu ba ya durfafi sama harya fara hawa meya tuna kuma ya sakko ya wuto Ɗakin Binta.
"Au da hankalinka ya gushe can zakayi kenan an maka kiranye ka shigo kamar wanda aka jefo baka ko gani dakyau ai seka tafi can ɗin" Binta ta faɗa tana babbake ƙofarta. Hadiza tayi masa sannu da zuwa ya ɗaga mata hannu yana cewa Bintan
"Matsa na shige"
"Ai sedai ka koma inda da ka niyyaci zuwa" inji Binta. Tsaki me ƙarfi yaj ya juya ya haye saman Hadiza tabi bayansa Binta ta kwarma Ihu murya a sama tana kiran yau akwai tashin hankali a gidan ashe.
A saman kuwa harya fara cire kaya Hadiza ta isa, a tausashe take cewa
"Da alama gajiya tasa ka manta ba a nan kake na yau"
"Ina sane, sedai in kema korata zakiyi se in tafi" ya bata amsa.
"Ba haka bane, rigimar Maman Zakariyya ce bana so kana jiyowa gata can tana masifa bana son tashin hankali ko ƙo dazun a Asibiti seda aka ce mu guji yawan hayaniya" ta sake faɗa cikin taushin lafazi. Audu ya rafka tsaki, da matan nan sun san me yake ciki da sun ɗaga masa ƙafa. Rigarsa ya raruma ya sauka sukayi kiciɓus da Binta na hawowa ya raɓeta ya wuce ɗakin Aisha.
Ganinsa ba yanda ta sababa yasa ta masa sannu da zuwa ya shige ɗaki ta bishi da ruwa, tana jiyo hayaniyar Binta dukda bata jin me take faɗi sosai. Abincinta ta kai masa beci ba yana kishingiɗe ya harɗe hannaye ya zurawa guri daya ido, ta ajiye, tana so ta tambayeshi ko lafiya amma ta kasa se kawai ta fita ga Dada da tayiwa mamarta alƙawarin za'a maidota hartayi barci yanayinsa kuma ya nuna ba lafiya ba balle tayimasa maganar.
Tana zama Binta ta faɗo kamar jifa, ta mata kallo daya ta maida idonta kan Talabijin yanayin kallon Hadarin kajin da tayi matan ya saka Binta yin shiru dan kwarjini yarinyar ta mata, tabbas Sarauta ba Ƙarya ba. Ɗakin data san zata samu Audu ta tura ta shiga, Aisha bata san ya sukayi ba taga Binta ta fito sumi sumi ta wuce. Data sake leƙawa se taga kamar yayi barci dan haka ta shige dayan dakinta suka kwanta tareda Dada.
*PROMO PROMO PROMO*
*Nace kina da Labarin MOMMY MOROCCO ME KAYAN MATA KUWA?* *Ko kuwa dai kina nan zaune baki wangale kina fama da masu niqa Kuka da Citta ko su qulla miki Garin Masara da sunan Magani*? *To ki karkade kunnenki Yar uwa ki kuma maza ki dauraye qafarkin nan da tayi furu furu domin MOMMY MOROCCO Ta diro Nigeria kuma tafe take da Abin Arziqi Niqi Niqi*
*Ina mai farin cikin shaida muku Moommy Morocco zatayi BONANZAr kayanta na kwana biyu*.
*Tazo muku da zafafan magungun wanda ya taba amfani dasu ne kadai ze baki labari Ingantattun magunguna na gani na fada ajin farko wanda aka hadasu cikin tsari da kula daga Ganyayyaki da kayan abincinmu masu qara lafiyar jiki da saukarwa Mace Ni'imar da take buqata kayanta babu Algus babu abinda ze cutar dake da yardar Allah*
*1-Da akwai hadin First ladies exclusive VIP package*
*2-Qafarka qafata package*
*3-Kankat package*
*4-Da kuma Mini package*
*Tazo muku da gangariyar maganin SANYI sadidan na Jiki dana Mara wanda In sha Allaahu ba ke ba sanyi kuma za a iya ba wa Yara, Maza ma suna sha*
*Bata tsaya iya nan ba tazo da Turarukan ta na ban mamaki se wanda ya gwada ze bada labari, Kedai kada ki bari de wannan damar ta wuceki domin ta zabtare Farashin kayanta har zuwa kaso 50% discount! Kyaso wannan gara basa ta wuce ki kuwa Indai ba Bintan Audu kike ba* 🥴🥴
*A tuntubeta a WhatsApp:09086233009*
*Ko kiran waya a 08029988065*
*Siyan Nagari Maida kudi gida*
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*