← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 137

Sashe 78

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aisha tasan Audu dukda Ƙarqarinsu gaisuwa duk sanda yaje gidan Yayan nata, tana bala'in girmamashi dan ganin babban mutum take masa kwatsam sega maganar Aure tana qoqarin shiga tsakaninsu, ita din yarinya ce me matuqar sanyin hali da biyya ga Manyanta wannan dalili ya saka sanda Yayanta ya sameta da maganar Abokinsa ya ganta yana sonta ya tambayeta ko tana da wani da take so tace masa Aa, shikenan magana ta Ƙullu har anje Tambaya.

Yakubu ne ya Tilasta masa cewar dole yaje gidansu Binta, babu yanda za'ayi yaci gaba da jingineta gaban iyayenta tsayin lokaci dan sun masa shiru bayana nufin basu son yarsu bane kawaici kawai sukayi masa kuma da son itama su koya mata darasi ta ganr kuskuren abinda ta aikata dan gaka baze saura sabon aure ba tareda Binta ta san Matsayarta ba. Dole ya shirya zuwa Kaduna, yanda Alhaji Zakariyya ya ringa bashi haƙuri yasa duk yaji wani iri, kamar ze durqusa masa yake roqonsa da yayi haƙuri akan abinda Ƴaƴansa suka aikata masa a madadinsu yana nema musu afuwa, ya Ƙara da cewa

"Bana so ka dubeni cikin yanke hukuncin makomarku kaida Mamana, karka cutar da kanka, idan har kana ganin bazaka iya cigaba da zama da ita ba ina goyon bayanka daka sauwaƙe mata domin tayi abinda ta cancanci hakan, amma idan kana ganin zaka iya yafe mata kayi mata uzuri to, ina da yaqinin abinda ya faru a baya baze maimaita kansa ba domin iyakar Fada, Nasiha da Tunatarwar daya kamata muyi mata a matsayin mu na Iyayenta munyi muma kuma fatan taji".

Se yaga kamar a fakaice Alhajin roƙonsa yakeyi akan ya mayar da Bintan, kuma bai kamatu ace mutum da yayi masa tarin Alkhairi a rayuwa kamar Akhaji Zakariyya ace shi ya gagara maida masa ba, darajar tasa shi Amincewa yayi bikon Binta, ya kuma sanarwa da Alhaji zancen auran da ze daura da Mata biyu sati biyu masu zuwa Alhajin yayi masa murna da fatan Alkhairi haka ma Mama sannan ya kira Binta a gabansa ya shaida mata muddin ta koma ta sake aikata wani abu da ze tunzura Audun ya sake aikota gida to daga can ta nemi gurin zuwa badai gidansa ba, ya sake ja mata kunne sosai kanta na Ƴasa tana kukan munafunci tamkar taji abinda yake faɗi kuma zatayi amfani dashi.

Kwanan sa biyu da zuwa suka juyo tare, zaman dai babu yabo babu fallasa sabgoginsa yake yana ta shirye sgiryen bikinsa. Ta tarar da an sake Ƙalƙale gidan, banda dakinta da yake a kulle hatta da samansa an bare Asalin Tarazo da yake gurin an maida Na zamani kayansa ya sakko dasu dakin da Abdullahi yake ciki nan ya kafa Gadonsa yake kwana yanzun, tsakar gidan ma am Canza Tarazo, kitchen dinsu na waje an gyarashi sosai kamar dai na cikin dakunan su se aka yanki filin tsakar gidan aka sakeyin wani Kitchen din na Langa langa, babu fus bare ta tambayeshi wannan sabon shirin na menene haka a haka taci kwanaki goma da dawowa wanda kuma ya rage saura kwana biyu a daurawa Audu Aure ranar taga ana shigowa da sababbin kayan gado da Kujeru aka haura sama dasu.

Daya dawo da daddare ta dauka ranar zasu koma saman tunda an saka kaya harda katifa amma setaga ya bude sabon dakinsa ya shige abinsa se washe gari yake shaida mata gobe Daurin auransa, amma Amarya daya ce zata tare a goben dayar se wani satin.

Kamar sabuwar galahanga haka ta bude baki tana kallonsa jin wannan magana, wai Amarya daya, ita dayar se wani satin,
"Amaren har su nawane?" Ta jefa masa tambayar, ya wani kalleta sheqeqe kafin yace
"Su biyu ne kafin Allah ya kawo cikon ta hudun"
"A nan gidan zaka zubamu mu ukun?" Ta sake tambayarsa wannan karon kallonta kawai yayi be amsa mata ba ya juya ya fita.

Kuka ta fashe dashi, kishiya har biyu rana daya ita Binta ita za'ayiwa wannan tozarcin? Duk Bara'atu ce ta janyo mata wlhba zata saɓu ba dole ta nemi mafita. Har ta saɓi mayafinta zata fita ta tuno cikin sababbin sharuɗɗan daya gindaya mata harda fita babu izini, ta mayar dan yanzu neman yarda takeyi dole tayi biyayya akan duk abinda aka gindaya mata. Kuka wiwi ta ringayi, Turai take so taje ta gani su shawarta babu halin fita, tayi data sanin ƙin nemo Lantana tunda ta dawo da yanzu ita zata tasa kawai ta aiketa gidan Turan tunda ita ba zata iya zuwa ba. Yanzu haka zata zauna a kawo mata Kishiyar babu ko wanda ze tayata zama ya danne mata Ƙirji?

Washe gari kuwa kamar yanda yace tun farar Safiya yasha wanka ya bar gidan, fitarsa babu jimawa sega mota cike da Yan Bechi, su Bilki da wasu daga cikin faccalolinta. Tsohon falon Bara'atu suka baza tabarma suka aje kayayyakinsu. Gaisuwa kadai sukayi da Bintan suka hau haramar dora abincin dan sunzo da cefanensu rankatakaf kafin su shigo Audun ya fada musu inda zasu tsaya su karba danyan abinci kadai suka diba a store dinta suka hau girki.

Binta na daki kamar tsohuwar mayya ita da gidanta amma bata iya fitowa su kuwa hidima suke suna raha suna dariya, suka sauke abinci suka ware na Yan Daurin Aure idan dawo da kuma na karbar Amarya sukaci nasu kafin suka hau wanka da shiryawa.

Afujajan kamar an jehota Lantana ta diro gidan, taje sau babu Adadi sanda Binta bata nan seda Audu yace ze saka a kulleta idan ta sake zuwar masa gida neman wata Binta kafin ya samu salama ta dena zuwa. Binta na kwance ta dirar mata kamar jifa tana haki harta bata tsoro,
"Hajiya, ashe har bayan mutum ya mutu ma yana iya cigaba da kitsa tuggu da munafunci?" Lantanar ta tambayeta, Binta tana gyara zama ta galla mata harara tana cewa

"Wane kalar hauka da dabbanci yake damunki Lantana zaki faɗo mun daki haka se kace Asiri? Yaushe na fara sakar miki fuska da zakiyi mun wannan sakarcin?"

"Hajiya ki ƙyale wannan maganar tukunna muyi wadda ta kawoni, kinsan wacece Amaryar da Alhaji ya auro miki kuwa?" Lantana ta bagarar da maganar Bintan, itama jin an soso mata inda yake mata Ƙaiƙayi yasa ta zabura tana tambayar wacece.

"Ƙanwar Sadiya ce Aminiyar Kishyarki Marigayiya Bara'atu, nidai nace ko a mafarki take zywarwa Sadiyar suka Ƙulla wannan Munafuncin? Ko kuwa daman tun Marigayiyar na raye ita Sadiyar tayi niyyar cin Amanarta ta aurawa Alhaji Ƙanwarta?"

"Allah mungode maka daka bamu lafiyar jiki data Ƙwaƙwalwa" Bilki datavshiga tambayar Binta ta bada abinda za'a saka mata abinci ta tsinci zancen nasu me kama dana zararru.

"Ban shiga sabgarku ba Bilki karki kuskura kishiga tawa" Binta ta gargadeta, se da tayi irin dariyar nan me cusa takaicin kafin tace

"Allah ya huci zuciyar Hajiya Binta uwargidan Dan Uwana Audu, daman kwano nazo ki bada a saka miki abinci, idan kuma kin Ƙoshi shikenan"

"Ku kuke yunqar Abinci nida kika ganni kinsan daga gidan wadata na fito abinci ya ishemu shiyasa har muka cida Dan uwan naki Butulu dayaci ya Ƙoshi yake gwada mana halin nas ana butulci, ita kuma annamimiyar da tana Ƙasa a kwance ma ba zata barni na huta ba wlh zamu gamu, Addu'a zan durfafiyi ubangiji ya shiga tsakanina da ita" Binta ta zaburoqa Bilki, seta juya tana dariya tace

"Tabbas jahilci yafi hauka ciwo, amma naji dadi da kikace zaki durfafi Addu'a, Allah ya dubeki ya kawo miki sauqi cikin lalular da take damunki Binta" daga nan ta fice Binta ta yunqura zata bita taji ba'asi wai tace mata Jahila kuma mahaukaciya Lantana ta tareta.
"Hajiya keda akuyarki tayi kura dan Allah ki nutsu ki Ƙyalesu yanzu matan unguwar nan zasu fara shigowa dan Sadiya babu wanda bata gayyata ba daman surutunki ya gama cika unguwa wasu ma cewa suke Asiri kikayiwa Bara'atu dukda ta fita daga gidan nan seda kika aikata lahira da yawa kinga ba fuskar da zasu shigo miki suka samu ba yanzu ko dalilin bikin nan kowa zata shigo kinayin abu a tafi dake a baki sharri se iya wanda kikaji wlh" da wannan ta tausheta suka zauna jigum jigum babu jimawa kuwa mata suka fara tururuwa a cikin gidan.

Ana sallame sallar isha'i aka kawo Amarya gida ya sake cika danƙam da mata, Lantana ce ta fita ta gano mata ina za'a saka Amaryar dan tana ta lissafa inda ze ajiye dayar tubda dai gidansu dakin mata biyu ne ko kuwa can ze gwamutsu kowa ta dauki daki daya su haɗa falo bata san musu ba.

Lantana tazo mata da labarin daya sake gigitata, wai sama aka dora Amarya, dama tana ta jiyo dudubniyar mutane ta dauka zazzabi da ciwon kan daya rufetane yasa take jiye jiye ashe da gaske ne, lallai wato da Gaske Audu ya tashi ci mata mutunchi a wannan karon.

*PROMO PROMO PROMO*
*Nace kina da Labarin MOMMY MOROCCO ME KAYAN MATA KUWA?* *Ko kuwa dai kina nan zaune baki wangale kina fama da masu niqa Kuka da Citta ko su qulla miki Garin Masara da sunan Magani*? *To ki karkade kunnenki Yar uwa ki kuma maza ki dauraye qafarkin nan da tayi furu furu domin MOMMY MOROCCO Ta diro Nigeria kuma tafe take da Abin Arziqi Niqi Niqi*

*Ina mai farin cikin shaida muku Moommy Morocco zatayi BONANZAr kayanta na kwana biyu*.
*Tazo muku da zafafan magungun wanda ya taba amfani dasu ne kadai ze baki labari Ingantattun magunguna na gani na fada ajin farko wanda aka hadasu cikin tsari da kula daga Ganyayyaki da kayan abincinmu masu qara lafiyar jiki da saukarwa Mace Ni'imar da take buqata kayanta babu Algus babu abinda ze cutar dake da yardar Allah*
*1-Da akwai hadin First ladies exclusive VIP package*
*2-Qafarka qafata package*
*3-Kankat package*
*4-Da kuma Mini package*

*Tazo muku da gangariyar maganin SANYI sadidan na Jiki dana Mara wanda In sha Allaahu ba ke ba sanyi kuma za a iya ba wa Yara, Maza ma suna sha*
Chapter 78 · 0% Book details