← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 137

Sashe 35

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata tarar da Binta a dakin ba motsin da taji a Bayi yasa ta ankare da tana ciki, Jinjirin daya ci sunan Babanta Binta Zakariyya na nade cikin showel ta matsa inda yake yanda aka kwantar dashi yayi kusa da bakin gado sosai, dukda cewar jinjirine amma ze iyayin motsi me qarfin da ze fado hakan yasa ta dagashi ta maidashi can tsakiyar gadon yana ta sharar bacci abinsa daidai nan taji muryar Binta akanta tana cewa
"Waye wannan? Uban me kikeyiwa Dana?"
"Gyara masa kwanciya nayi, naga an barshi a bakin gado" Bara'atun ta fada kanta a qasa. Binta ta galla mata harara ganin itace kafin tace

"Akan me zaki shigo mun har quryar daki me kike nema?"
"Daman maganar Abinci ce yan Bechi sun qaraso wanda aka bayar kuma ya qare shine nace ko zaki saka a qara musu"
"Babu, gayyar yunwa nace babu abincin ko kuwa ni na ce suzo balle na basu abinci?" Bintan ta fada cike da masifa. Bara'atu ta kalleta tace
"Yan uwan Yaya Audu ne fa ba wasu daban ba"
"Yana sama ai seki hau ki gaya masa ya sakko ya girka musu suci tunda yan uwansa ne ko kuma ke ki je ki sake dora wani amma ni abinci na ban dafa saboda wasu yan qauye ba na baqin dana gayyato ne dan haka malama maza fitarmun daga daki tun ranki be baci ba"

Kafin Bara'atu ta sake cewa wani abu burum Yaya Salima ta fado dakin kamar wadda ta labe daman tana jiran lokaci yayi ta shiga. Inda jinjirin yake ta nufa ta dauke shi tana cewa
"Bari a fita dashi mutane nata zuwa ganinsa se kuma ta zare ido ta kalli Binta data cire dankwalin kanta zata canza kaya tace
"Ke zo ki gani wane irin bacci yaron nan yakeyi haka qirjinsa baya dagawa alamar numfashi?"
tana rufe bakinta Babbar Yayarsu Anty Sakina ta shiga dakin ta kallesu sunyi cirko cirko tace
"Lafiya kuwa meya faru?"
Salima ta miqa mata Babyn tana cewa
"Yawwa dubashi kiga Anty se naga kamar baya numfashi" da yake ita malamar jinya ce, nan ta tattaba yaron tayi salati tace
"Wannan ai ya rasu".

Maganar ta taja hankalin Bara'atu da har ta kai qofa ta tsaya, Binta ta finciki yaron daga hannun Yayarta tana duba qirjinsa babu alamar yana dagawa, ta kai kunnenta zuciyarsa bayan ta saka hannu a hancinsa bata ji dumin numfashi ba nan ma shiru seta sake shi Yaya Saliman tayi azamar tarewa kafin ya kai qasa kamar qiftawar Ido Binta ta dira gaban Bara'atu ta cakumeta tana cewa
"Kashe shi kikayi? Na rantse da girman Allah se kin bishi" nan ta shiga kai mata duka kamar me casar gero kururuwarta da ihun Bara'atun ya janyo hankalin sauran dake falo shigo gaba daya, tuni gida ya dauki hayaniya magana ta fasu Bara'atu ta kashe jinjiri gashi can Binta ta riqeta itama tace seta kasheta. Binta ko dukan Bara'atu take babu ji babu gani tamkar ma bata hayyacinta fadi kawai tace

"Wlh sena kasheki, sena bi kadin haqqin dana" ta shiga jibgarta tamkar Mahaukaciya ta kama yaron da yake tsokanarta saboda rashin Imani kuma yan uwanta kaf dake tsaye aka rasa wadda zata kwaci Bara'atun daga inda suke tsayen suke ce mata wai ta qyaleta ga gawar Jaririn a Hannun Anty Sakina.

Ihun Bara'atu na neman ceto da kururuwan Binta tana fadin seta kasheta ne ya janyo hankalin Yan suna. Hankali tashe yan Bechi suka duru darin, su suka taru suka danne Bintan har Bara'atu ta samu ta kubuta daga hannunta tayi mata jina jina fuska ta haye dan duka tasha ta ko ina.

"Meye haka? Kinyi hauka ne Binta zaki kama ta da duka?" Audu da suka sakko da gudu shida Jama'arsa da suka zo mata suna ya fada cikin tashin hankali.
"Wlh ban gama dukanta ba, idan anga na haqura to na kasheta kamar yanda ta kashe mun Da" Bintan ta sake fada tana zaburowa yan uwanta suka riqeta. Cikin rashin fahimta Audun yace
"Wace magana kikeyi haka? Wane dan aka kashe?"

Bayan wasu Awanni.
Ihun kuka da hargowar Binta kawai ake ji a falon,
"Na rantse da girman Allah yanda ta kashe shi itama seta bishi babu uban daya isa ya hanani daukar mataki akan wannan abun" taci gaba da sheqa kuka. Dazun da akayi jana'izar yaron sanda aka zo fita dashi qaramin hauka ta tayar ta riqeshi qam dakyar Maza suka bambareta ta ringa doke doke qarshe se a daki a ka kulleta se yanzun bayan Isha Audu yaje ya budeta da kansa ya tasa qeyarta zuwa samansa inda Yakubu yace ya tattaro su gaba daya aji abinda ya faru. Babu tsoron Allah ko tunanin bayan wannan rayuwar da akwai wata Munira da Salima suka bada shaidar Bara'atu ce ta kashe jaririn dan Munira cewa tayi ta leqa dakin ta hangota zaune an showel dinsa bata dai tsammaci yana ciki ba seda Salima ta shiga ta tarar da ya mutu.

Sakina dai tayi shiru, har ranta bata so abinda sukayi ba, magana ta gaskiya yaron ya rasu tun kafin Bara'atu ta shiga dakin, qus qus din da ta tarar dasu sunayi na taraddadin yanda zasu fada mata ne suma basu san menene silar mutuwarsa ba haka nan suka lura da babu rai tattare dashi shine suka shimfide mata shi a kan Gado ita kuma Bara'atu ta taka sahun barawo kuma tana shiga Salima ta kitsa ai kawai suce itace kuma har yanzun basu fadawa Bintan ainihin abinda ya faru ba.

Yakubu ya kalli Bara'atu data zama wata abar tausayi, fuskarta a kumbure ga duka ga uban kukan datasha. Cikin tausayawa yana kallonta yace
"Bara'atu menenr gaskiyar abinda ya faru?"

"Wallahi Allah shine shaidata ko taba yaron nan banyi ba. Ni daga haihuwarsa ma sau daya na taba riqeshi a Asibiti, sanda na shiga dakin na tarar dashi sun kwantar dashi a gefen gado abinda ya saka na matsar dashi tsakiya saboda naji tsoron karya motsa ya fado shine Binta ta fito ta ganni ko ita idan zata fadi gaskiya a tsaye ta ganni ban zauna mata a daki ba ga yan uwana nan a tambaye su da fitata daga daki zuwa sanda abin ya faru ya isa ace na zauna akan Jariri ya mutu har jikinsa yayi sanyi?" Bara'atun ta fada cikin dasashshiyar murya me ban tausayi. Yakubu ya gyada kai cike da aminta da zancenta ya kalli Audu yace

"Kaji daga kowanne bangare se kayi alqalanci bisa Adalci"
"Alqalanci? Shi ne ze yanke mun hukunci akan kadin ran dana da aka dauka? To billahillazi huwarrahamanu ba'a isa ba, ku barni na kasheta da hannuna ko kuma gobe na tafi kotu, ina da qwararan hujjojin da zasu saka a zaman farko Alqali ya saka a gillewa muguwa kai ta bishi, wlh ran dan baze tafi a banza ba" Binta ta sake zaburowa tana fada.

"Ya isa kiyi shirunki babu wanda yace ran danki ze tafi a banza" Audu ya fada, kafin ya kalli Bara'atu yaci gaba da cewa
"Dama ai kinyi furucin se kin ga bayan ta ita da abin cikinta. Allah be baki nasara ba tun yana ciki baki haqura ba seda kika aiwatar da shirinki yanzun ko Bara'atu yaushe kika zama muguwa me baqar zuciya haka? Ina tsoron Allan ki da har zaki iya zama akan Jinjirin kwana bakwai har seda ya daina numfashi me ya tsare miki a duniyar daya saka kika kauda shi?"

Shiru ne ya gifta gurin kamar kowa ya mutu koda yake da yawa daskarewa sukayi basa ma numfashi tsabar mamakin Kalaman Audu, Yakubu har zamewa yayi daga kan kujera yana leqen fuskar Audun ya kuma gaza furta komai. Audu yaci gaba da magana yana cewa
"Na gaji da wadannan mugayen halayen naki Bara'atu, daman simi simin mutum da yawanku mugayene, zuciyarku cike take da mugunta fal gashi kuwa kin fara fito mana da ita. Yau kin kashe Zakariyya, qila gobe Kan Bintan zaki juya idan aka kwana biyu kuma ki hau kaina na mutu ki gaje abinda na tara dake da yayanki ko ba haka ne shirinki ba shiyasa bakya so Binta ta haihu saboda ya zama yayanki kadai suke da gadona to bazan jure ba, ai se da igiyoyin aurena akanki ne idan na mutu zaki ci gado na ko? To kije kawai Allah ya hada kowa da rabonsa na Alkhairi na sawwaqe miki igiya daya".

Tirqashi, wasa farin girki

*A nan na kawo qarshen Free pages na littafin MATAR MUTUM, zanci gaba a Arewabooks ku duba @Maryamfarouk01*

*Domin samun cigaba a whatsapp maza ki tura da 500 zuwa Asusun*
*7061838488*
*opay*
*ko kuma*
*0709290797*
*Access bank*
*Maryam Farouk*

*Se a tura shaidar biya ta wannan layin 07061838488*
Idan katine a dauki hotonsa a turo ta lambar sama, VTU kuma a saka a Layin sama.

Yan Niger ku tuntubeni kai tsaye domin na hadaku da wadda zaku biya kudinku a gurinta Nagode.

https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER)*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 15*

https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG

"Allah ka gani babu saka hannuna a cikin wannan al'amarin, Allah karkasa haqqin baiwar Allan nan da suka dauka ya bibiyeni" Ummu ta fada bayan data gamajin abinda ya gigita mata tunani. Da safiyar sunan aka kirata daga gurin aikinsu, ita din yar jarida ce kasancewar ta dauki uzuri ta tafi Kano se kuma wani aiki ya taso dan haka manajansu ya kira akan taje a maimakon ace se an taso wani daga Kadunan yazo tunda tana tareda abin nadar rahoto da sauran abubuwan buqata shiyasa ta tafi bata san badaqalar da aka kwasa ba seda ta dawo kuma da ace tana nan tabbas da bata goyi bayan abinda suka aikata ba dan ita din itace Mahaifinsu sak gurin dattako. Ta Jinjina abin ta kumayi matuqar mamakin yanda yan uwan nata suka iya aikata wannan ta'asa.
Chapter 35 · 0% Book details