← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 137

Sashe 38

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A daren ranar sun shirya washe gari zasu taho dukda Bashir be so ba sedai gari na wayewa Audu yacewa Ali su bari se gobe su tafi"
"Sedai na tafi na barku a nan dan ni banga abinda ze saka na qara kwana a gurin nan ba" Alin ya bashi amsa.
"To ka rakani na gwada sa'ata, idan ta kulani shikenan ko yau din zamu iya tafiya" cewar Audu. Kallonsa kawai Ali yayi dan lamarin Audun ya fara bashi tsoro. Ya tsoron kar maganar Hausawa ta tabbata da sukace zama da madaukin Kanwa na kawo farin kai, idan Audu ya dauki Halin Bashir to in beyi da wasa ba shima zasu jashi ciki dan haka ya kakkabe rigarsa ya fice daga dakin yana cewa shidai ya tafi ze hau motar Haya.

Qarfe goma suna tsaye bakin mota gaba dayansu, Bashir sunyi fada da Karuwar daya kwana da ita har taji masa ciwo da kwalba ya mata dukan mutuwa wannan fushin ya saka ya fasa qara kwanan da yayi niyya yace su tafi shi Ali daman harya fara cigiyar inda ze samu motar Kano yaga sun fito. Bashir na sallama da jama'ar sa Audu har ya shiga mazaunin Direba dan shi ze jasu saboda ciwon hannun Bashir sega Zubaida ta fito daga gidan taci kwalliya daurin nan kamar ze fadi saboda yanda ta tsikara shi hannu ta riqe da jaka madaidaiciya da zata ci kala a qalla Kala uku se qaranar jakar mata a daya hannun da alama wani gurin zataje kuma tafiyar kwana ce.

"Yar dagwas, an sauka daga sarautar kenan" Bashir ya fada yana kallonta, tayi far da ido, cikin yanga da iyayi tace
"Eh, ina kayi? Naga kamar tafiya zakayi ko?"
"Kano na nufa, kefa na ganki da jaka da alama balaguro zakiyi"
"Zan sauka a Zariya" ta fada tana wucewa motar, ta aje jakarta akan Boot ta wuce ta bude gaba ta shige kai kace motar tace. Bashir ne ya saka mata motar a Boot haka suka kamo hanya, duk yanda take daurewa seda ta biyesu ta shiga hirar, sun tsaya a hanya zasuyi sallah Audu ya samu damar yi mata magana shida ita.

"Kaga malam, nifa ba irin sauran masu Arhar da kuka saba tayawa bace" ta bashi amsa tana farfara ido ta wuce ta barshi a gurin yana murmushi kamar wawa. Dagaske sonta yake, irin soyayyar nan ma me zafi. Har qofar gidan da zataje suka sauketa a Zariya dukda tace su ajiyeta tun akan hanya.
"Nan ne sabuwar maboyar taki kenan? To sena rako Abokina" Bashir ya tsokaneta, ta harare shi kafin ta Audu tana taunar cingam qas qasa tace
"Nagode Samari, se wani jiqon"
"Shege Abokina wlh ka samu shiga, kasan uban nacin da nayi akan yarinyar nan kuwa amma taqi bani fuska? Kai bani kadai ba kowa mararinta yakeyi amma yarinyar nan yanda kasan kudi wahalar samu ne da ita, daga qusoahin gwamnati se Sarakuna take kulawa" Bashir ya fada yana dukan kafadar Audu.

Ali yaja tsaki yace
"Wlh kayiwa kanka fada karka kuskura ka bari shaidan ya maka ingiza me kantu nidai babu ruwana daga yau ma in sha Allah bazan sake binku fita irin wannan ba"
"Nifa na gaya maka sonta nakeyi dagaske" Audu ya fada bayan sun hau titi. Bashir ya ringa dariyar iskanci yana cewa
"A sannu dai duk zasu hau saiti, wato ina gaya muku dadin duniya a sha ruwa ga mata, kai Allah ka yafe mana kurakurenmu".
Haka har suka iso Kano.

Ba'a rufa sati ba ya kama hanyar Zariya ba tareda ya sanarwa da Abokanansa ba saboda yanda tunanin Zuby ya addabeshi, yaje gidan da suka ajiyeta wanda se sannan ya gane nan ma gidanmata masu zaman kansu ne, ya rasa ta inda ze fara nemanta. Har gurin Magajiyar gidan aka kaishi tace babu Zubaida a gidan haka ya haqura ya dawo Kano da qunar zuciya sedai duk yanda yayi akan ya yakiceta ya haqura da tunaninta abin yaci tura. Gaba daya ya shiga damuwa ya zaman har walwalarsa ta ragu. Da Binta ta matsa masa da tambaya se ya ce mata Asara yayi, aiko ta si ta fishi shiga tashin hankali ma dan Binta na son kudi, dukiyar Audu kuwa jinta take kamar tsokar jikinta a kullum zancenta Duk abinda yake dashi nata ne tunda itace sila shiyasa take baqin ciki idan yayi Alkhairi wa wasu, ta bangarenta kuwa duk abinda take dashi ko take samu babu me ci, hatta a karan kanta mugunta takeyiwa kanta dan da wani ya mori abu tareda ita gara ta haqura da abun itama.

Wata biyu Audu ya kwashe yana dakon soyayyar Zuby, dayaga abin baze fita daga ransa ba tilas ya samu Bashir ya roqeshi akan ya nemo masa ita.
"Wlh sonta nake Bashir kuma da Aure" ya fadawa Bashir din.

"Amma dai Audu baka da hankali, to ai koni da nake cikakken dan Bariki iyakata da Karuwa na biya buqata ta mu rabu a gurin duk matan da suke yawo a garin nan ka rasa wa zuciyarka zata so se Karuwa? Hauka kake ko shaye shaye ka fara?" Bashir ya fada cikin madaukakin mamaki.

"Nidai idan zaka nemo mun ita kawai ka nemota Malam babu ruwanka ko Magajiya ce a hakan naji na gani kuma ina sonta in har ta amince kuma auranta zanyi" Audu ya bashi amsa cikin tsare gida. Bashir ya kunna sigarinsa yana zuga yace

"Babu shakka Haqqin Bara'atu ya fara dabaibayeka tun ba aje ko ina ba, ka saki yar gidan mutunchi me Cikakken Asali zaka maye gurbinta da Karuwa to Allah ya kyauta ka shirya gobe muje Zariyan, da kace musu Yar Dagwas da tuni an nemo maka ita sedai kuma idan suna ta canza a can dan halin matan Bariki ne basa amfani da sunansu na Ainihi.

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 16*

Kamar yanda Bashir ya fada suna isa suka tambayi yar dagwas se gasu a dakinta aka rakasu. Zubaidan na kwance kamar mara lafiya suka shiga, ta ringa kallonsu da mamaki dan bata gane Audu bama Bashir dai data fi waya shi ta gane.
"Lafiya? Tara ko bashi?" Ta fada cikin tsiwarsu irin ta yan Bariki bayan data miqe tsaye. Audu dai se binta yake da kallo Bashir yace

"Ai kya bamu gurin zama musha ruwa tukunna yar dagwas", tayi gatsine kafin ta dauki wani siririn mayafi ta yafa a kanta da babu dankwali ta fita tana tafiya a hankali.
"Duk yanda akayi dan Hau ta hadu dashi ya lakada mata na jaki shiyasa ka ganta haka" Bashir ya radawa Audu. Wani duumm yaji a zuciyarsa, shikam So be kyauta masa ba ya rasa macen da ze zargo masa se yar bariki wadda jikinta bashida shamaki da Maza.

Zuby ta dawo da kwalabe uku a hannunta, biyu na Giya is Coca cola daya ta ajiye a gabansu.
"Ga naka nan wadannan nawa ne" Bashir ya fada yana tura masa Coke din. Seda ya zuqe kwalba guda kafin ya kalli Zubaida dake zaune daga gefe ta jingina tana kada qafa yace
"Tafiyar ta Aboki na ce, kwanaki ma yazo yayi ta bulayi ni ban ma san ya akayi yasan sunanki Zubaida ba yazo haka ya koma ba tareda ya sameki ba, bari na baku guri na dan nemi inda zan rage lokaci" ya fada yana miqewa da dayar kwalbar a hannunsa.

"Kaga jashi ku tafi ni ba lafiya ta isheni ba kuma ko qalau nake kasan tsadata ba haka nan ake fado mun ba kamar wata mara Aji" ta dakatar da Bashir din, se yayi murmushi yace
"Al'amarin da yake tafe dashi yafi wannan kedai ki saurareshi kawai" daga haka ya fita ya barsu.
Audu ya muskuta yana kallonta soyayyarta na qara huda zuciyarsa yace
"Bakida lafiya ne"
"Matsala aka samu nayi ciki, uban yace ze karba kuma naga kar daga baya yazo ya mun Akuya na zubar" ta fada masa kai tsaye kamar wadda ta aikata abin kirki, is ya kasa cewa komai ya zuba mata ido kawai zuciyarsa na bugawa.

Ina jinka fadi abinda ya kawoka dan kwanciya nake so nayi" ta sake fada tana gyara zama, zaman shima ya gyara ya fuskanceta dakyau kafin ya shiga zayyano mata abinda yake cikin zuciyarsa dan ya gaza dannewa,
"Kuma ni da Aure nake sonki, ina so ki bar wannan rayuwar ki koma gida gaban iyayenki wannan rayuwar bata dace da Mace kamarki ba, ki je kiyi Istibra'i zan aureki".

A duk maganganunsa fadar ta koma gida gaban iyayenta ne ya jefata a wani hali ya tado mata da tsohon mikin dake zuciyarta nan da nana hawaye suka wanke mata fuska. Kewar gidan da Mahaifanta ya taso mata se gani yayi ta hade kai da guiwa tana kuka wiwi. Hankalinsa ya tashi da kukan da take ya kuma shiga mamakin me ya sakata kuka, shidai ba wa'azi yayi mata ba balle ace tsoron Allah ne ya ratsata kawai ya gaya mata yana sonta ne ze Aureta amma take wannan kukan kamar wadda zata mutu take.

"Ki dena kuka dan Allah" ya fada cikin rabewar murya.
"Ka tashi ka fita" ta bashi amsa cikin bada umarni. Ya tsaya amma tsaqar data buga masa tasa dole ya fita cike da mamakinta ya zauna a qofar dakin.

Zubaida kuwa tana kuka ta koma tunanin Baya, gida take tunuwa da mahaifiyarta tareda sauran yan uwanta da kuma dalilin daya fito da ita. Duk ranar da aka ambaci Iyaye ko Gida se tayi irin kukan nan, tana so ta sake ganin nata amma bata da hali. Kalaman Mahaifinta suka dawo mata sanda yake korarta daga gida.
"Ki tafi, idan kika sake waiwayarmu Allah ya isa iyakar abin kunyar da kika jamun ya isa ki tafi duk inda zakije Zubaida na yafeki daga cikin Yayana".
Chapter 38 · 0% Book details