Sashe 103
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Soyayya ta ƙullu tsakanin Fatima da Ahmad ko ace farashin soyayya nata hauhawa a zuciyar Ahmad domin abinda yakeyi yafi kama da One sided Love sedai ya kasa fahimtar hakan. Kwana uku tsakanin zuwansa na farko ya sake komawa daga nan kuma ya mayar da zuwan nasa sau biyu a sati bayan nan kuma kullum a ƙalla ze kirata waya sau uku yaji ya take, kulawa da tattali duk irin wadda yasan zata farauto masa da zuciyarta yana mata amma ko a jikinta shan ƙamshin nan ma ƙaruwa yake ko a waya idan suna magana yanayin da take amsawa tamkar bata so amsarta bata wuce Eh ko Aa shi zeyita zuba surutu inya gaji yace tana jinsa tace Wh bata da abin cewa ne shi yasa tayi shiru hakan kuma yake jurewa baya fushi yana cigaba da lallaɓata.
A cikin haka suka koma makaranta wanda taji daɗin hakan sosai saboda ko babu komai zata huta da zuwan da yakeyi sannan zata samu uzurin da zata ringa gujewa wayarsa yanzu dan a gida Idan ya kira Umma data fahimci Ahmad ɗin be samu karɓuwa gurin Fatiman ba ita take takura mata tayi ta mata faɗa idan ta bar wayar tana ƙara ko yazo ta tsaya nuƙu nuƙu taƙi fita. Ta kance mata wulaƙanci babu kyau, bata san abinda Allah ya tsara ba kuma ita bataga makusarsa ba da zatace beyi mata ba dan a zuwansa na biyu ya shiga har ciki ya gaidata itama data ganshi ta fahimci nutsuwa da Kamalar da Malam yace yana da ita. Yaro ne amma Allah ya hore masa nutsuwa da dattako daya zarce shekarunsa kuma duk wasu iyaye na kwarai tabbas zasuyiwa Yarsu sha'awar samun Miji me kulawa tamkar Ahmad ɗin.
Bayan sun koma makaranta haka zeyita kiranta ba zata ɗaga ba, tun su Badar basu sanda Ahmad ba dan bata gaya musu ba har suka gane dalili wata raba ya kirata tana sallah Badar ta amsa wayar suka gaisa ya kama sunanta shikenan hira ta ɓarke, Fatima bata so ba domin muddin Ahmad yayiwa Badar tasan ta shiga uku, takura kam ko ruwa me daɗi ba zata barta tasha a dalilin Ahmad ba shiyasa take ta ɓoyewa gashi yanzu Badar ɗin ta ganoshi.
"Dukda banga guy ɗin nan ba tun daga voice ɗinsa nasan ya haɗu, wato Afee kin iya catching Big Boys matsalar duk yan iska ne in disguise Allah yasa dai wannan na Allah ne dan wlh daga magana a waya harya burgeni yana da nutsuwa ga kirki, waye shi? A ina kuka haɗu" Badar ta tambayeta bayan ta gama waya da Ahmad ta bashi uzurin abinci zataci shi kuma ya shaida mata ze fita Jafar ne yazo ze ɗauko shi daga Airport.
"Ya samu hutu ne shine yazo Gaisuwar Rasuwar Brigadier General Baballiya Bechi, ƙanin Alhajinmu sa sukayi Hatsarin jirgi last two weeks ai kinji labari ko?" Abinda ya gaya mata da duk ya saka taji kunya kenan. Sanda akayi rasuwar ta gani a SM, kuma anyita surutun a gari kan set up ne akayi musu ba wai Accident bane ba ance akwai wani sirri da suke shirin bankaɗawa na wata badaƙala data faru shine kafin nan masu laifin suka kawar dasu, tunda taga Bechin a ranta ta kawo yana da alaƙa da Ahmad kuma ta gani ya saka a Status harya tura mata cewar an masa rasuwa kunyar data ji yanzu irin gaisuwar da tayi masa ta
"Allah ya jiƙan rai" kawai tace, babu wani sympathy babu nuna concern na cewar Kawunsa ne na kusa ya rasu tana ganin shiyasa yanzu yake gaya mata Jafar yazo dan tasan Mutuwar me muhimmanci ce a gurinsu tunda har na wata ƙasar ya taho ita kuwa ba wanda ta gayawa a gidansu ma balle ko a waya su masa gaisuwa.
Hoton Ahmad kawai ta nemo ta miƙawa Badar data addabeta da waya, cikin Mamaki take kallonsa tace
"Ahmad Bechi? Wlh Afee kinyi Miji kinsan kirkin mutumin nan kuwa?"
"A ina kika sanshi?" Ta tambaya tana tsare Badar ɗin da ido wani abu da bata taɓa tsammatar zata jishi akan Ahmad ɗinba ya taso mata wato kishi.
"A IG mana, ai ina following ɗinsa" b
Badar ta bata amsa. Seta tsume fuska tace
"Shine har kika san kirkinsa daga ganinsa a IG kuma"
"Ai mutumin kirki baya ɓuya, kuma idan da kinsan yanda mutane suke yabonsa da bakiyi mamakin dan nace yana da kirki ba, kin san yanda yake taimako kuwa? Ke dai Allah yana sonki Afee, kinga ya canza miki da abinda yafi duk shegun da kika rasa Alkhairi wlh ki gode masa"
"Allah ya saka mu a danshinku Afee, ke kam Allah ya taimakeki da jinin manyan mutane, Bechi Family fa?" Ilham roommate ɗinsu ta faɗa nan suka shiga hirar caaa caaa kowa na tofa Albarkacin bakinsa.
Ahmad
Ƙarfe biyu ya fita ɗakko Jay wanda suka samu delay na jirgi daga Abuja zuwa Kano, tun daren jiya ya sauka daga London, ya biyo jirgin Abj to Kn na sha biyu da rabi na rana basu taso ba se biyu da wasu mintina uku saura suka sauka a Kanon. Beyi mamaki daya kira Yah Ahmad yace masa already yana cikin Airport ɗin ba. Be taɓa barin sa yayi jira muddin yana gari shi ze zo ya ɗaukeshi kafin Jirginsu yayi Landing Ahmad ya isa Airport wani sa'ilin har Abujan yake zuwa ya taro shi su taho Kanon Tare.
Cikin tsananin murna da ɗokin ganin juna suka rungume juna kowanne yana jin soyayyar ɗan uwansa na sake ratsa Jini da jijiyarsa.
"Kullum ƙara girma kakeyi da fresh, look at you, idan muka jera za'ace kai Yayana ne na uku ma" Ahmad ya faɗa cikin zolaya yana kallon Jay daya ɓata fuska irin na sangartattun yara wai yace masa tsoho. Kuma da gaskiyar Ahmad ɗin, A tsaye Jay yake gansansan kamar ya haɗa jini da samudawa koda yake jinin Binta da Audu fa kowanne ba baya bane a garin jiki.
Suna tafe suna hira gwanin sha'awa har suka isa gida. Hajiya na tsaka da shiri domin wannan karon ta rantse gayya zasuyi suje taro Jay ɗin se Kano gaba ɗaya ta san da ya dawo. Idan zezo gida babu wanda yake sani, ko a jirgi badda kama yakeyi saboda ya tsani irin taro da hargowar da mutane sukeyi duk sanda suka ganshi a cika guri ayita ihu ana ɗaukar hotuna dashi ayi blocking masu uzurirrika shiyasa kusan shekara biyar kenan ya canza salon zuwansa Nigeria, hatta da manager sa na nan wrong schedule yake bashi dan shi yake sanarwar Jay ɗin na tafe ya haɗa masa mutane shiyasa ya zaɓi boye zuwansa, Ahmad kaɗai yake gayawa se idan ya dawo a kwashi tsiya da tsiyataku da Hajjaju dan idan zezo Yau ce mata yakeyi se Jibi sedai ta ganshi kamar dirar kirsimeti.
Zuwansa na ƙarshe waccen shekarar na buɗe Shagon Ahmad daman bata san da zancen ba ganinsa kawai tayi, ta zabga tijara ta kuma ce Alhaji yayi mata tsakani da Ahmad ya fita a sabgar Ɗanta, ta yaya za'ayi idan ba mugunta ba ya saka ya baro gurin sana'arsa dan yayi Asarar miliyoyin da ake biyansa? Ta kuma ce zancen Ahmad shi kaɗai ya ɗauko shi daga iyafot ya kau, duk in ze sake zuwa zuga za'ayi dangi da Abokanan arziƙi aje a taroshi jama'a su san yana da gata ba wai ace kamar shi sananne a duniya idan zezo gida ya ringa shigowa kamar Ɗan fashin da ake fako a kama.
Shine dalilin daya saka ta haɗo Jama'a kenan dangi da Abokanan Arziƙi, jira takeyi ayi La'asar su ɗebi motoci a tafi Iyafot ɗauko Jafaru, yau ɗin har kwalliya taci, ta saka Sabuwar Atamfarta Super Sheraton, kusan shekarar ta uku a ɗinke, da siyanta kuma zatayi biyar ko Shida ta sallah ce da Alhaji yayi musu sauran da yuwuwa sun dade da bayar da tasu amma ita se Yau Allah ya nufa zata saka shima da fari wani Lace ta saka, sabone amma ajiya tasa ɗinkin ya fita a yayi, tun ana style me Umbrella da hannu me ɗorin Kafaɗa, ga wata uwar boader Lace da aka tattara a wuya da bakin Hannu, da ace Zallar Lace ɗin aka ɗinka mata ko ya shekara goma zata saka abinta dan babbane, Design ɗin Lace kuma baya tsufa sedai ɗinkin jikinsa ya nuna shekarunsa.
Turai ce ta kalleta sanda ta fito ala dole ta ƙure gayu ga Sarƙar Zinare irin design ɗin Saudiyya damɓasheshiya ta sauka har kan ƙirjinta, jan hannunta Turai tayi da sauri suka koma ɗaki tana cewa
"Haba Binta, yanzu saboda Allah da wannan shigar zaki tafi tarar Jafar ɗin se kace wadda ta fito daga riga? So kike ki ja masa abin magana a ɗauke ku hoto a yaɗa a a duniya duk suturunki keko ki rasa wanda zaki saka se wannan Matsiyacin Lace ɗin dan girman Allah ina zaki kai ubannin suturun da kike dasu ne?"
Hajiya ta yamutsa fuska tana kallon Turai tace
"Karki gaya mun mara daɗi mana, me Leshi na yayi? Ina a gurinki na siyeshi ko a lokacin ai ya haura ɗari balle yanzu indai ba cutata kikayi ba kuma"
"Shekararki nawa da siyansa? Ni wlh har na manta da nayi irin Leshin nan bana zaton wadda na bawa ma har yanzu yana nan be zama tsumma ba, yanzu dai duk ba wannan surutun ba su Hajiya Rafi'a da Hajiya Zuwaira duk suna falo yanzu suka iso se kin raina kanki idan kikaga kwalliyarsu, yayayenau kansu da sukazo dasu bakiga yanda suka sha kwalliya ba se ke da ake taron saboda ke ce zaki fita a haka kamar mara kan gado dan Allah wuce ki sauya Kaya, ki nemo na mutunchi wannan rakwacam ɗin sarƙarma kiyiwa girman Allah ki tattarosu muje gurin Alhaji Mansur a narkasu, a maida miki ƙirar zamani".