← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 137

Sashe 126

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai shiyasa nazo da jaka tashi zakayi mu tafi bankin ka ciremun kuɗina na gaji da wannan ƙarairayin naka kullum bayan Alhaji Zakariyya ya gaya mun ya karɓi nasa ni kake so ka cuta kenan ka cinye mun kuɗi to baka isa ba" Hajiyar ta faɗa cikin ɗaga murya. Naziru ya dafe kai, ya rasa bayanin da zeyiwa Hajiya ta fahimceshi, saboda Allah tayaya ze tura mata Miliyan ɗari uku ko kuma ya cirosu ya zuba mata a Ghana Must Go a wannan halin da EFCC ta matsa ko da account ɗin kamfani cikin takatsan tsan suke abubuwa balle aga kuɗi irin haka suka fita daga personal account ɗinsa ai tona masa asiri zatayi.

"Hajiya shima kayan kuɗi ya karɓa ba zallarsu ba kuma kiyi haƙuri ki dena ɗaga murya mutanen gidan sunajinki" ya faɗa a tausashe. Ta zabga masa harara tace
"Ni kuɗi na nake so, waima kayan uban wane kuɗi kuke magana akai kamar wasu marasa gaskiya haka yace mun wai kaya ya karɓa su kayan basu da suna ne bayan Mai akwai abinda ka fara siyarwa ban sani bane da ake samun kuɗi saboda mugunta baka gaya mun ba balle na gwada nima?"

"Zinare ya karɓa na gaya miki na fara haƙar zinare a Zamfara ai"

"Dan ubanka da akace dutse yana ruftowa mutane so kake ka mutu saboda rashin godiyar Allah zaka zurƙuma cikin rami wai haƙar zinare Naziru?" Hajiya ta faɗa tana zare ido kamar ance mata dutsen ya rufta dashi. Ya kalleta, da ace watace daban daya tambayeta a duniya waya kaita son zuciya amma uwarsa ce duk iskancinsa baze kwatanta haka ba se yayi murmushi yace

"Bafa da kaina nake shiga ba Hajiya kamfani ne suke haƙan da injina kuma jari kawai na saka ina karɓan ɗanyan gold se na fitar a sarrafashi"

"To nima ina so a saka kuɗin, amma ni idan an haƙo gida za'a kawomun abuna in ajiye se yayi tsada sannan na fitar na siyar sarƙoƙina ma zan kwashe su idan zan tafi Umarah Turai tace sunfi daraja yanzu acan zan siyar se in baka kuɗin a ƙara jarin yanda za'a ringa samu da yawa. Wallahi fa ance kuɗi akeyi sosai da harkar nan, kaga yaro bashi da ko taro amma dayaje ya shiga rami ya dawo kaga ya zama Miloniya wannan tubda da Inji nema za'a haƙo sedai muna zaune muyita karɓar kaya toh haka za'ayi, amma bani ko Goma ce yanzu na tafi da ita dan na saka rai zan siyi filayen nan har nace a dubamun na bakin Titi zasu fi daraja idan an kwana biyu".

Naziru ya sauke ajiyar zuciya jin ya tsarata kuma ta hau kafin ta sake botsarewa ze san abinyi. Dole ya shirya suka fita Banki ya cire 10M aka saka mata a Ghanarta ko tsoro bataji ta haye Napep wai ta tafi Janguza, dayace ze kaita cewa tayi Aa, a dabararta karyaje yaga inda Filayen suke. Yakubu sau biyu yana sace mata Takardun Manyab Fikaye yaje ya siyar, dake bata mantawa da komai nata har gewaya take zuwa taga lafiyar kadarorinta ɗaya taje taga an yi gini har An saka Amarya ɗayan kuma Plaza akayi tayi masifar tayi bala'in ƙarshe tayi Allah ya isa dan Yakubun taurin kaine dashi kamar me kuma hauragiyarta ba tsorata shi take ba, sa'idar data samu yanzu matsayinsa daya ƙaru a Kamfani, sedai shegen Yaron kamar yanda take faɗa kansa kawai yake Azurtawa. Ko sun so ayi cuwa cuwar da aka saba ya kankane komai ya hana ta tabbatar idan suka matsa kuma kamar yanda yake cewa tsaf ze fasa ƙwai, rabuwa dashi tayi yanzu amma tana nan zatayi maganinsa yanzu maganar auran Hajiya ƙarama data taso ce a gabanta daia Abba Tee har iyayensa sunzo anyi tambaya shima Yakubun Aure zeyi.

AFEEYAH

Sannu a hankali soyayya da shaƙuwa me ƙarfi ta shiga tsakaninta da Jay, wani irin so take masa da bata san iyakarsa ba, kodan ya dace da duk wani mafarki nata akan Mijin da take so t aura ne oho?
Ahmad da kansa ya gane cewar akwai wani al'amari a gabanta wanda ya sake karkatar da hankalinta daga kansa saboda yar hirar da yake samun dama sunayi ma yanzu gagara takeyi, duk sanda ze kirata uzuri zata bashi na tana wani abun musamman da suka fara Second semester exam daga tace masa karatu takeyu se ta gaji zata huta alhalin lokacinta karankaf yanzun na Jay ne, karatun kansa ba wani mayar da hankali takeyi kamar da ba da idan akace zasu fara exam da sati ɗaya ma ta dena hawa Social media tattara hankalinta take tsaf har se sun gama sannan to wannan karon kuwa se a hankali, idan tana waya da Jay manta kowa da komai takeyi bata ma son abinda ze katseta se su raba dare suna magana har se da kansa yace ta kwanta tayi bacci dan bata faɗa masa ma mun fara exam ba seda sukayi guda huɗu ya rage uku su gama sannan ranar kuwa tasha fada ta kuma ƙara tabbatar da Jay baya ɗaukar nonsense dagaske kamar yanda yake cewa.

Har yajin kiranta yayi na wuni guda aikuwa taji a jikinta dan ya mata mugun sabo da soyayyarsa me tsayawa a rai. Jay ya iya soyayya, ya iya saka mace ta manta kanta duk taurin zuciyar Mace idan ta shiga hannun Jay tilas ta sallama dan yasan duk wani lago na mace da ze karya ta dashi, ita da kanta ta kance salon Jay da Ahmad yana kama. Tabbas da ta bawa Ahmad dama ta buɗe masa zuciyarta ze mallaketa tsaf ta yanda wani baze samu matsuguni ba amma ta rasa abinda ya hanata yin hakan, ta yuwu dalilin zuwan Jay ne, wani lokacin se taji muryoyinsu har kamanceceniya yake mata kawai dai ta Jay tafi ta Ahmad tashi, haka idanunsu iri ɗayane, seda tayiwa hoton Jay kallo na tsanaki ta fahimci haka idanunsu iri ɗayane, shape ɗinsu, kalar kwayar idon da komai Badar tace mata wai Sexy Eyes kenan masu irin idanun sun iya soyayya kuma dasu suke cafke zukatan Yammata ta yarda da hakan dan bata iya haɗa ido da Ahmad se taji gabanta na faɗuwa duk sanda ta kalli idonsa ji take kamar ta sallama masa amma taurin kai irin nata ya sa har aka kawo i yanzu.

Saura kwana biyu su gama Exam ranar Ahmad ya kirata, kwana biyu ya bata space tunda tace masa Exam sukeyi idan ya kira bata ɗaga ba kota amsa ta bashi uzuri sosai ransa yake sosuwa shiyasa ya zaɓi daya barta ta gama exam ɗin idan har da gaske itace uzurin daya saka baya samun lokacinta. Tana kwance duk batajin daɗin dalilin yajin kiran wayar da Jay ta daka mata, tunda ya fahimci Exam suke kuma take wasa da karatunta tana biye masa shine yayi fushi. Ya gaya mata baya son mutumin da bashida focus, yana sonta amma baze taɓa haɗa lokacinta da Aikinsa ba me yasa ita zatayi wasa da Karatunta saboda shi?

Yace baze sake kiranta ba se sun gama kuma ta tura masa da Time table sannan idan ma ta kirashi baze amsa baz kullum da safe ze mata text haka da rana da dare amma babu phone call saboda magana dashi yasa takeji kamar wata mashashshara ce ta kamata duk ta rasa gane kanta. Tana ganin wayarta na ringing ganin Ahmad ne kamar ba zata amsa ba se kuma ta ɗaga dalilin tunanin da tayi a ranta, tabbas Alhakin Ahmad ne tun ba'a je ko ina ba Allah ya jarabceta da Jay.

A sanyaye suka gaisa daga ita harshi babu wani me karsashi,

"Yaya Exam ɗin? Saura guda nawa ku gama?" Ya kauda shirun da sukayi bayan gaisuwa ta bashi amsa a taƙaice da
"Lafiya lau, saura biyu"
"Masha Allah, Allah ya bada sa'a" daga nan suka sakeyin wani shirun. Ya sani idan zasu kwana a haka ba lallai ta sake cewa komai, wlh daze iya da ya rabu da yarinyar nan dan duk wata hanya da mace zata nuna bata ra'ayin mutum ta nuna masa amma zuciyarsa ta kasa haƙura da ita. A kullum cikin Addu'a yake akan idan babu Alkhairi a tarayyarsu Allah ya cire masa ita daga zuciyarsa ya musanya masa da wadda ta fita amma abun kamar ana rura wuta ƙaruwa yakeyi.

Idan Jafar yana bashi labarin sabuwar soyayyar daya gamu da ita se yace shi kam bashida sa'a ne a soyayya da Alama. Bega Yarinyar da Jay yake so ba, amma yanda har Jay yake labarinta ya sani ba ƙaramin sonta yakeyi ba itama kuma tana riritashi, ze iya cewa be taɓa ganin Jafar a yanayi na soyayyar gaskiya irin wannan ba, yace masa auran yarinyar zeyi, Bahaushiyace yar Nigeria a Zaria suka haɗu. Yaƙi ko gaya masa sunanta dayace ya tura masa hotonta ya nunawa Fatima ko ta santa nan ya fitittike ya ringa zuba masa Tijara yace kuma baze tura ba se ya dawo zasuje ya ganta face to face ko sunanta baze gaya masa ba balle ya faɗawa Fatiman.
"Tana da Friends haɗaɗɗu irinta zan samo maka guda ɗaya ka fita daga sabgar waccen Ajawon Fatiman da take wahalar da kai Yaya Ahmad" abinda Jay ya gaya masa.

Ahmad yaja numfashi, kusan minti bakwai daga shi har Fatima babu wanda yace wani abu. A sanyaye yace
"Fatima, idan wani laifi nayi miki kiyiwa girman Allah ki sanar mun na baki haƙuri, na gaji da azabatar da zuciyata da kikeyi kusan sati uku kenan kin hanani zaman lafiya nace zanzo kince Aa, idanna kiraki a waya koda yaushe cikin bani Excuse kike me nayi miki? Idan maganar kai gaisuwa da nayi ce kince Aa kuma na haƙura bayan wannan wane laifi nayi miki da kike hukuntani ta hanyar azabtar da zuciyata haka?"
Chapter 126 · 0% Book details