Sashe 83
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To kice mana, idan ma kina sonta ki riƙe na baki kuma karki sake zagina wlh dan na fiki iya tashanci" Binta ta hayayyaƙo mata, matar zata sake magana sauran suka tareta sukace ta barta da alama tana da taɓi a ƙwaƙwalwarta.
"Sedai uwarku ce me taɓi a ƙwaƙwalwa bani ba" ta bisu da zagi sanda suka fita taci gaba da kukan ta.
Haka suka tattaro suka dawo gida abin dai babu daɗi yanda Binta ta ringayi kamar me taɓin hankali duk saboda ta haifi Mace wannan fincika da tayiwa ƙafar Nazira ita tayi sanadiyyar Nakasarta wanda ba'a gane ba har seda ta kai munzalin tafiya sannan bayan dogon bincike likitoci suka gano wasu ƙananan jijiyoyin dake riƙe Sangalalen ƙafa da tafin ƙafarta ne a tsinke shiya nakastata ya zama ƙafar bata ɗaguwa sedai ta jata a ƙasa.
Lokaci daya Hadiza da Aisha suka dawo, tafiyarsu lamuran Asare Asaren da Audu yakeyi ukayi sauƙi, suna dawowa tamkar an watsawa wuta fetur abu ya koma sabo farfaɗowar daya fara aka sake kwanciya rigijin harma abin yafi nada muni. Akace zuciya bata da ƙashi balle kuma irin ta Audu me cike da wasi wasi a hankali se famfon da Binta take masa akan ya auro masu fararen ƙafa ya fara tasiri a zuciyarsa. Ya fara tsangwamar Hadiza da Aisha domin a cikinsu ne yake ganin akwai silar taɓarɓarewar Arziƙinsa, kyara, hantara, wulaƙanci ya fara yawa, Hadiza bata shiru idan ya mata ramawa takeyi daman Binta bata isheta kallo ba dan tasan gamonsu Aisha ce take masa shiru dan haka diban Albarkar tasa yaso yafi yawa akanta musamman da Binta ke yawan cewa daman an fi samun masu farar ƙafar cikin mata masu shiru shiru kuma ai data tafi wankan gida abubuwa sun farfaɗo amma tana dawowa ta dawo da tsiyarta.
Abu dai gaba yakeyi kullum ba baya ba, idan yayi kamar yabi ta Binta yaje ayi masa istahara a fayyace masa wwacece silar rugujewar Arziƙinsa se kuma ya tuna nasihar Yakubu dayace jarabawa ce saga Allah idan yayi haƙuri a sannu komai ze zama tarihi seya kanne yaci gaba da Addu'ar neman ɗauki daga ubangiji. Cikin wannan yanayi aka cinye shekara guda wanda a kullum ta Allah abin zama yake jiya tafi yau, Audu da harya fara mance lissafin abubuwan daya mallaka se gashi a hankali ya fara ɗaga kadarorinsa yana siyarwa a ƙoƙarinsa nason farfaɗo da harkar Mansa dake neman durƙushewa baki daya ya saki komai ya mayar da hankali akanta domin itace ƙarfin tattalin Arziƙinsa.
Binta ce takai wa mahaifinta rahoton abinda yake faruwa da Audun, shiri tayi ta kwashi kayanta domin tafiyar da tayi bata saka ran zata dawo ba, to ta dawo tayi me? Arziƙin da take zaman gadi yana shirin bin rariya wahala na doko musu sallama ita kam bada ita za'ayi wannan zaman ba. Alhaji Zakariyya ya tashi ɗan aike takanas aka kira masa Audu, sun tattauna amma a duk maganar da sukayi ya kasa gano musabbabin wannan Asara dake hawan Audu kamar wanda akayiwa Baki haka nan be bi takan shirmen Binta ba ya sake daukar Kudade masu kaurin gaske ya bashi yace kuma duk in wata matsala ta tashi karya jinkirta ya je gareshi, wannan karamci na Alhaji Zakariyya ya ƙara samarwa da Binta gurin zama a zuciyarsa domin ya sani Allah ne ya haɗa shi da Alhajin amma Auran Binta na daga abinda ya ƙara dankon zumunta a tsakaninsu kuma duk abinda zeyi masa zeyi dan Allah kuma saboda yana auran yarsa, wannan tasa ya ƙara kulla aniyar riƙe Binta dakyau domin bashida wata hanya da ze sakawa da Alhajin sama da hakan tunda duk sanda zwje gurinsa se yayi masa tanbihin ya kula masa da Binta karya dubi halinta.
Wannan kudi da Alhaji Zakariyya ya bawa Audu basuje ko ina ba yana dawowa Kano wani Abokinsa yayi masa tallar Farin wake, a shekarar an samu ƙarancinsa acan wani ƙauye suka samoshi yace su siya da yawa su ajiye zuwa A kwana biyu idan farashi ya hau su fitar su siyar dashi su samu riba. Audu be taɓa yin irin wannan kasuwancin ba dan ko wani yaji ze siyi kaya ya ɓoye zuwa yayi tsada sannan ya siyar se yayi magana ya nuna masa rashin dacewar hakan amma a halin da yake ciki yanzu ta yanda ze farfado da jarinsa kawai yakeyi shiyasa ba tareda dogon tunani ba ya siyo wake aka jibge a suto, ba'a rufe watanni uku ba wake yayi muguwar tsada ya ninka kudinsa sau biyu akan abinda suka siyeshi lafiya lau Alhaji Mala Abokin Audu ya kwashe wakensa ya kai Kasuwa ana bude store din da kayan Audu suke aka tarar da wake dai babu na moro Ƙwari sun masa kaca kaca dayawa har ya fara yin gari tsabar yanda ya lalace kamar wanda ya shekara biyar a ajiye.
Hankalin Audu yayi ƙololuwar tashi da wannan Al'amari, Alhaji Mala da Bashir suka sake jaddada masa tabbas idan ba Asiri ba to cikin matansa akwai me Baƙar ƙafa a tasu falsafar. Mala yace ya shirya ze kaishi gurin Malaminsa duk abinda ake ciki ze fayyace masa, yace Malamin yayi tafiya nan da sati ze dawo shima daman zeje dan akwai tafiya da zeyi yana so a bashi sa'a.
"Ai Ba'a zama haka Alhaji Audu yanda mutane suka ɓaci da jefw jefe wani ido kawai ze saka maka kaga komai naka ya tasamma lalacewa idan kayi sake magauta se sun kaika ƙas wlh kana kallon dai yanda abubuwa suke tafiyar maka kai base an ce maka da wani abu a ƙasa ba, idan ka biye ta wannan Yayan naka kana ji kana gani sedai ka koma jiran wa wani shago ana sammaka na cefane sunanka ya tashi daga sahun matasan masu kudi ka koma layin yan karayar Arziƙi" Inji Mala.
Yana komawa gida ranar Binta ce take da girki, damuwa ta masa yawa yanzun shiyasa abu da yawa ba s an tambayeshi ba yana zaune zeyita rattabo zance kamar wanda kansa ya kwance.
"Ina za'a jira har nan da sati ai ka tashi kawai kaje nan gurin Malam Salisu Mijin Lantana, ba tuntuni nake gaya maka ba amma kaƙi jin ta tawa ai yanzu da aka faɗa maka a waje ka yarda. Bari kaga inje in gano maka idan yana nan ai ba'a bori da sanyin jiki wlh gara asan abinda ake ciki" Binta ta faɗa tana saɓar Hijabi.
Audu bashida zaɓi a wannan gaɓar ruwan kashe gobara kawai yake buƙata shiyasa be hanata ba, Hadiza na zaune tsakar gida kan tabarma tana cin Abinci garin da dan zafi zafi ga tsohon cikin da take dashi ya ƙara mata jin zafin Binta ta wuceta tana cewa
"Maza kici gobe sedai kici a gidan me dattin hula".
Can ta samu Lantana suka gama ƙulla yanda za'ayi Lantana ta shiga ta zayyanewa Malam Salisu yace babu damuwa duk yanda tace hakan za'ayi. Seda sawu ya fara daukewa Sha daya saura kafin Audu ya tafi gidan Malam kamar wani munafuki, Malam Salisu ya tambayeshi sunan sa dana Matayen nasa gaba ɗaya ya gama zana ƙasarsa yana jan wani kwandalelen carbi se muzurai yake da ido yana motsa baki yayi zane ya share yafi sau biyar kafin ya kalli Audu yace
"Gaskiya Alhaji akwai gagarumar matsala, wai ma ya akayi haka wannan Aure babu bincike?"
"Kamar yaya? Anyi bincike mana" Audun ya bashi amsa yana kallonsa a wani ɗage, Malam Salisu ya murmusa yana cigaba da zanen sa yace
"Ba binciken halayya ko Asali nake nufi ba, Aa burujin ƙasa. Ya kamata ace in za'ayi Auran Alhaji a ringa bincikawa aga taurari matar ya suke zasuyi daidai da naka ko kuwa? Kamar dai yanzu kaga ita ta farin Fatsuma Binta kace sunanta ko? Wannan mahadin Arziƙi ce.
Kaga kai Tauraronka wuta ne, ita kuma Iska ce, ya kaga wuta a lokacin bazara yanda iska take fifitata inta ringaci balbal ai Allah kadai ke iya kasheta to haka ne hadin naku taurarinta suna ingiza Arziƙinka zeyita hauhawa ne to kuma se akayi rashin dace ita Aishatul Humaira taurarinta na Ƙasa ne, wuta kuwa da an yafa mata ƙasa ai mutiwa takeyi to me kankat kuma Hadizatul kubura ita taurarin ruwa ne shiyasa da suka hadu su biyu se ƙarfinsu ya danne na fatsuma suke neman nakastaka kuma in har ba'a dauki mataki ba gaskiya Alhaji abin bazeyi kyau ba dan abinda ƙasar nan take nunamun idan ba'ayi da gaske ba har rigar sawa ka fita seka wayi gari baka da me kyau abinci kuwa wata rana se an kwana ba'a ci ba sannan yawan haihuwarsu yanwan Talaucin da zasu cigaba da saukar maka a gida".
Ranar kwana zaune Audu yayi yana ƙullawa da kwancewa, Binta bata tambayeshi yanda sukayi ba domin ita ta tsara komai se dariya take a cikin bargo dan ta saddaƙar gobe daga Hadiza har Aisha kwanan gidajen tsoffinsu zasuyi. Washe gari da duku duku ya mata sallama yace ya tafi Bechi, be ko bi takan sauran matan ba, yara da suke gaidashi ma be iya amsawa ba ya fita burinsa ya isa Bechi ya samu Hashimu domin wannan sabgarsa ce shine yasan takan Malamai. Ya isa Bechi be zarce ko ina ba se gidan Hashimun yayi rashin sa'a baya nan amma inji Jamila ba dadewa zeyi ba dan yace a aje masa abincin rana. A tsakar gidan ya zauna kan Turmi tsabar halin da yake ciki ya gagara shiga turakar Hashimun da tace ta masa shimfiɗa ta aje masa ruwa da fura.
Seda akayi Azahar Hashimu ya shigo, an gaya masa anga wucewar Audu amma be yarda ba dan har can gida ya ratsa be ganshi ba se gashi ya tarar dashi a tsakar gida kan Turmi fuskarsa ta gama bayyanar da tashin hankalin da yake ciki. A taƙaice ya masa bayani babu bata lokaci ya goyeshi a mashin suka tafi wani dan ƙauye dake gabansu kadan. Bayanan Malam Salisu sunyi kamanceceniya da juna sedai an saɓa lamba a wasu guraren kamar Taurarin Aisha da Binta dashi bafulatanin yace masa taurarinsu iri daya ne da nasa dan haka babu matsala a hadinsu Hadizan dai itace me matsalar kuma akasin da aka samu Taurarinta nada matuƙar haske shiyasa ta tasiranci duka su ukun suke karbar gashi.