← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 137

Sashe 128

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Afeeya your body is shaking, ki nutsu dan Allah ba fa na faɗa miki maganar nan saboda ki saka kanki a damuwa bane ba...."
"Na fahimta Badar na gane wlh dama kuma nima ina yawan wannan tunanin a raina, Ahmad da be kaishi matsayi da suna a duniya ba Yan uwansa suna ganin ban dace dashi ba ina ga JAY wanda ba yan uwa ba na tabbata mutanen duniya kansu se sunyi mocking ɗinsa idan suka san yar wa ya aura, damuwata kawai Badar me yasa yasan da wannan tsarin na mahaifiyarsa ze zo gurina? Tun haɗuwata dashi ban boye masa komai a kaina ba, na gaya masa Mahaifina ba kowa bane me neman na kansa ne amma se yayi dariya kawai yaga kamar wasa nakeyi, kuma banyi wani abu na ƙarya da ze saka yayi tunanin na fito daga wani babban Ahali ba ko kawai kenan Surata ce ta rudeshi yayi mun kallon daidai da matsayinsa? Kenan a gidan Masu kudi kadai ake samun Yara masu Kyau da sura irina ba'a haifarsu a gidajen Talakawa?" se tayi shiru tana jin kuka yana taso mata, bata iya riƙe shi ba kuwa ta fara Badar ta miƙe hankali a tashe ta dawo kusada ita ta riƙe hannuna tana cewa
"Dan Allah ki dena kuka kinga ana kallonmu"
"Badar ina son Jay, idan na rasa shi bansan ya rayuwata zata kaya ba. Na sani ban kai koda matsayin me aikinsa ba amma zuciyata ta yi ɗage ta kai kanta inda be kamata taje ba kuma shine sila, shi ya kwaɗaitamun soyayyarsa irin wadda na daɗe ina nema me yasa be dubi matsayi da tazarar dake tsakani mu ba ya shiga rayuwata da alƙawarurrukan ƙarya da ya san baze cikamun su ba ya san mahaifiyarsa nada zaɓi kullum yake cemun duk abinda yake so shi take so ba zata taɓa hanashi auran wata mace ba muddin yace ita yake da muradi?"

"To ai Afeeyah kinga shima Yah Sani ya faɗi abinda ya sani ne kawai akan Mamanshi, zata yuwu ta canza ko kuma kamar yanda ya gaya miki ba zata hanashi auran duk macen da yace yana so ba tunda ta fi sonshi cikin yayanta doke taso farin cikinsa. Ni dalilina na faɗa miki maganar nan saboda karki sake jiki kuma daga ƙarshe ba fata ba ki zama disappointed, amma kamar yanda kika ce shi yasan wacece ke kuma a hakan yace yaji ya gani yana sonki ki kwantar da hankali all shall be well in sha Allah" Badar ta faɗa cikin lallashi.

Afeeyah ta kife kai kan Table taci gaba da rera kuka tamkar har ranar rabuwarsu da Jay tazo, she can't imagine loosing Jay, is like loosing her whole life dan bata tsammanin zata sake moruwa, soyayyar sati uku jinta takeyi tamkar ta shekara ɗari uku, daƙyar ta haƙurtar da kanta ta kuma ɗauki shawarar Badar da tace tayi confronting Jay domin tasan makomar relationship ɗinsu tunda wuri tunda dai shi zuciyarta tayi amannan da. Tabbas tana da buƙatar hakan, zata so ya furta mata da bakinsa tunanin da yakeyi akan Ahalin da ta fito sannan zata kawo maaa maganar Mahaifiyarsa taji view ɗinsa akai.

*Assalamu alaikum*
*Ina matan suke, Manyan mata yan kwalisa da suka amsa sunansu na Mata ba muna mata ba Kawayen Binta gumama?*

*SODAH GENERAL ENTERPRISES ce tazo da kanta ba aike ba tana kuma shaida mutu da cewar zafafan kaya sun sauka, kamar yanda kuka sani tana kawo muku suturu na sakawa kama daga kan Atamfa, Laces da dangoginsu*

*Wannan karon ta sake taho muku da tsarabar Supplements ingantattu wato Original bawai copy ba. Ku sani bayan abinci jiki yana da buqatar qarin wasu sinadarai da zasu taimakawa ginuwar jikin da lafiyar kowanne bangare na jikin, SODAH ENTERPRISES tana da General Supplements ma'ana wanda suke tattare da Vitamins da dukkan jiki yake buqata sannan tana da special supplements wanda HQ wato gidan mutunchi yake buqata domin sake tsare qima.*

*Ina wadda take fama da skin nata yaqi dadin azanci? Fata ta bushe tayi dabbara dabbara ta shafa mai duk a banza se qara lalacewa tayi? To maza ki leqa gurin SODAH ENTERPRISES domin tana da sabulu me kyau da inganci me gyara fata tayi kyau ta goge tayi sulbi baya saka Fari asalin kalarki ze sake fiddo miki ya kuna goge duk wasu tabo ko rashes da suke hanaki walwala, sabulunta babu chemical ba kuma na bleaching bane yawwa karki tsammaci da zakiyi haske Aa sedai glowing kalarki ta ainihi ze fitarda.*

*A tuntubeta kai tsaye akan 08137145294*
*Ko ki danna wannan link kai tsaye domin magana da ita*
https://wa.link/wwvjr3
*Location Kano, tana Nation wide delivery*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 15*

A daddafe suka ƙarasa exams idan kaga Afeeyah se ka ɗauka jinya takeyi saboda yanda ta fita a hayyacin ta. Tun daga ranar da Badar ta bata taƙaitaccen labarin Mahaifiyar Jay ta shiga wani yanayi na tunani da lissafin yanda makomarta zata kasance. Ƙarin tashin hankalinta kwanki huɗu kenan basuyi waya da Jay ba, zeyi mata text safe rana dare ya tambayeta ya take amma a ƙarshe ze sake jaddada mata karta kuskura tace zata kirashi har se ta kammala Exam ta san koda ta kira kuma baze amsa ba ita kuma taso suyi magana, ya warware mata abinda ya addabeta a zuciyarta ko ta samu nutsuwa.

Ranar Thursday suka kammala, ƙarfe bakwai da rabi suna shirin fita Ahmad ya kirata wai ya shigo Zaria yana Dogarawa lokacin, tayi kasaƙe da waya tana mamaki dan gaba ɗaya ma ta manta da batun ze zo ɗaukarta yau, ita bata ma shirya kayanta ba dan lissafinta kawai se gobe Juma'a zata wuce gidan amma tunda yazo babu damar tace ya koma hakan dai dole zata shirya ta bishi su tafi dan haka suna fitowa daga Exam basu tsaya komai ba suka wuce Hostel. Ahmad ya sake kiranta akan idan babu damuwa zeje Kd yanzu ya amso wani saƙo kafin ta gama shiryawa ya dawo

"Idan ba sauri kakeyi ba ka jira kawai mu tafi tare se mu kai Badar gida" ta faɗa masa, Badar ta ƙwalalo ido tana kallonta tace
"Ni nace miki yau zan tafi?"
"Nima ai ba yau nayi niyyar tafiyar ba saboda ya rigada yazo yasa dole zan tafi, ki tashi dan Allah karmu tsayar dashi" Afeeyah ta gaya mata. Dole Suka kashi kaya dan shirin da basu ƙarasa ba kaɗan ne, Badar nata mitar batayi sallama da Sweetynta Nurain ba kuma sunyi yau ze kaita yawo yanzu tasakata tafiya gida ita dai ta toshe kunne har suka kama hanya.

Badar da Ahmad keta hirar su ba tareda sun damu da Afeeyah ba dan daman sun saba muddin tafiya ztacehaɗa irin haka shiru takeyi tabarsu idan ma daga shi se itane sedai ya gaji da magana ya kunna Radio. A gidan Hajiya Ummu Yayar Hajiya Binta ya karɓi saƙon Laces ne ya siyawa Momy, a mota ya barsu ya shiga shi kaɗai da ze fito Hajiya Ummu da itama zata fita daman shi take jira ta biyo shi suka fito tare.

"Au daman tare kake sa baƙi shine ka barsu a Mota Ahmad? Rowar yar tawa kakeyi mun ko kuma baka riƙeni uwa ba shiyasa ka hanasu shigowa?" Hajiya Ummu ta faɗa. Ahmad ya duburburce, sam be kawo zata fito ba kuma shi be ƙiyi musu tayin shiga ba sedan baya so su ɓata lokaci dan yasan Antyn Ummun cewa zatayi se sun zauna sunci abinci dan shi kansa daƙyar ta barshi ya fito shaf shaf ɗin gashi kuma yanzu yayi complicating abun.

"Wlh Mama ba haka bane, ita wannan gida zamu sauketa Fatima kuma mu wuce Kano tare. Naga rana tayine bana so mu ɓata lokaci amma kiyi haƙuri bari su shigo". Yanda duk ya rikice yana mata bayani yasa tayi murmushi tace
"Karkayi kuka na yarda ba da niyya kayi ba". Ahmad yayi dariya, Badar da Fatima suka fito suka gaisheta ta amsa da fara'a tana tambayarsa wacece Surukar tata a cikinsu.

"Ki zaɓa Mama" ya faɗa yana shafa kai, tace
"Kowaccece a ciki Allah ya tabbatar da Alkhairi, saura ɗan uwanka ya kamata shima ya bar ruwan ido haka ya fitarda mata" ta koma cikin gida bayan tace su jira tana zuwa. Hijabai ta ɗebo ta basu sukayita godiya. Badar data karɓi ledar bayan sun shiga mota kafin Ahmad ya shiga tacewa Fatima
"Ke Hijaban Ummu-Maheer (07061838488) ne, kinga ledarta".
"Ai sun zaga duk inda bakya zato Kyau iya kyau, kasha gayunka da kuɗi ƙalilan a ringa zaton tafiyayye kika saka dole ki ganshi a gurin manyan mata irinsu Hajiyar nan".

Suna yan hirarrakin Ahmad ya dawo suka kama hanya. Tilas seda sukaci abinci sukayi Azahar kafin Momynsu Badar ta barsu suka tafi. A hanya Ahmad nata mata santin kirkin Maman Badar. "Ai Momy badaga nan ba gurin kirki, ita Badar ta gado" amsar data bashi kenan ta kame baki ya gaji da jan maganar shima ya kunna musu karatun Alƙur'ani ƙasa ƙasa suka cigaba da tafiya.

Lokaci lokaci yake kallonta yana ganin yanda ta mayar da hankali kan wayarta kome takeyi se Allah idan ta nisa kuma taja tsaki ita kaɗai tayi tagumi ta kalli window. Yana so ya tambayeta me yake damunta amma ya kanne, so yake ya fara jurewa yana danne sonta ko ze samu ta fara dubansa da kimar da yake so. Bukar ya gaya masa ya bata iska, bawai barta ba tunda yana sonta amma ya koyi kamewa shima ya dena nuna mata cewar idan babu ita baze iya rayuwa ba.
Chapter 128 · 0% Book details