Sashe 37
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwanci tashi har aka shekara da rabuwar Audu da Bara'atu a sannan kuma Binta ta sake haihuwa aka maida mata da sunan Babanta Zakariyya, rayuwa taci gaba da gungurawa, budi da Arziqi suna qara zuwarwa Audu a shekarar kuma yaje aikin Hajji tareda Yaya Baba babban Yayansu da Goggo Fadi, da Yakubu yaso suyi tafiyar amma yace ba zashi ba dan har sannan be sauka daga fushin da yayi da Audun ba, wannan dalili ya saka Audun bawa Yaya Baba kujerar ita kuma Goggo Fadi Yakubu ne yace ya biya mata, a cewarsa iyayensu Malam da Dada duk basuyi tsahon ran da zasuci arziqinsa ba dan haka yayi mata yasan zasuyi Alfahari dashi a inda yake ai kuwa taji dadi yayanta sunji dadi suka ringa masa Addu'a kamar me wannan abun da yayi ya saka Yan uwan zage jin zafinsa akan rabuwa da Bara'atu, dukda tafiyar ba'a son ran Binta akayita ba amma ba yanda ta iya tunda tana da danyan Jego a sannan haka sukaje suka dawo Audu ya koma Alhaji Audu.
Bayan dawowar Audu daga aikin Hajji ya tattara kudade daya dade yana tarawa tun bayan daya fara harkar mai. Kaduna ya nufa dasu ya samu Alhaji Zakariyya. Sanda Alhajin ya gama sauraron jawabinsa tsaf yana kallonsa yana murmushi. Shikam haka nan Allah ya dora masa qaunar Audun, tamkar sun hada jini ta wani gurin.
"Da gidan Mai, da jarin dana baka duk kyautace Abdullahi shiyasa hatta da filin da sunanka aka siyeshi haka nan na baka zabin sunan da za'a sakawa Kamfaninka. Ina fatan ya zame maka hanyar riqe kanka da Ahalinka gaba daya kuma Al'umar annabi su amfana da dukiyarka" Alhajin ya fada yana kallonsa. Haka Audu ya dawo Kano cike da mamakin karamci irin na Alhaji Zakariyya, wannan ya saka ya qara daura aniyar kulawa da Binta domin yana ganin babu wani abu da zeyiwa Alajin ya biyashi tamkar kyautata mata.
Yanayin Budi da sana'arsa ta sakashi haduwa da sababbin Abokanai matasa masu tashen kudi kamarsa a lokacin, kamar kuma yanda rayuwa take a kowanne fanni mutum yakan hadu da Abokanai na kwarai dana banza, ya rage a karankanka kayiwa kanka Alqalanci kabi wanda Tarbiyya da dabi'arku tazo daidai to hakan ce ta faru da Audu yayi sababbin Abokanai da suka kasance Yan cikin kwaryar Birni wayayyu kuma yan Boko sun fantsama cikin harkar Man fetur domin sannan itace harka data bullo da akeyin kudi da ita a dare daya.
Alhaji Bashir da Alhaji Ali sune mutum biyu da suka fi shaquwa da Audu saboda koda tafiya ta kamasu zuwa inda suke dakko Mai tare sukeyi sannan suna wasu sabgogin Kamar fitar Kayayyaki irinsu Cocoa da Qaro zuwa qasashen dake da buqatarsu. Wannan shawarar Audu ce dan tun yana zaman bakin rimi yakan tsince hirar ana zuwa daga waje ana siyan wadannan Abubuwa. A yawace yawacen kasuwancins yasan duk inda ake samunsu dan haka suna haduwa da Alhaji Bashir wanda shi kuma yana da kyakykyawar Alaqa da wasu Turawa dan a qasar waje yayi karatu nan da nan aka qulla kasuwancin se Ali ya shigo ciki shi kuma ya nemo musu masu siyan Qaro nan da nan Kasuwa ta bude musu Arziqi kamar ana ruwansa ta ko ina zubowa yakeyi.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*
Audu be tsaya iya nan ba yana Noma, manyan gonaki ya siya a Bechi sannan a Gadonsu da yake juyawa an fitar kowa ya siya masa tasa Bilki da Aisha sun bawa Mazajensu suna kula musu da ita shi kuma ya karbi hayar ta Yakubu data Baballiya yana Nomasu, babu abinda baya Nomawa haka nan be yada saide saiden Kasuwa ba Shagonsa na kayan yara da mata na nan ya qara bunqasa ya zuba yara suna kula masa dasu.
Alhaji Bashir shine me rawar kai a cikin guruf dinsu kuma shi ya fara diban Audu suna yawo a gari, shine rakashi gurin waccen yau gobe gurin waccan, tun yana zuwa rakiya kawai har ya zama shima ya fara kule kulen Mata. Dukda dai iyakar hirace take hadashi dasu sabanin Abokin nasa da yake taba shashanci da Matan. Ya kashe musu kudi su biyashi da Jikinsu bayan harkar mata har ruwa yana korawa kuma duk abubuwan da yakeyi yakan nunawa Audu hakan ba komai bane, a nan Nigeria ne ake daukarsu a wani Abu amma yej turai yaga rayuwa kuma menene amfanin neman da sukeyi idan ba zasuji dadin rayuwarsu ba?
Ali ma yana kula mata amma shima kamar Audun hirace kawai amma kuma su ukun ko da yaushe suna tare, duk yawon da Bashir zeje zasu rakashi su suka bude masa Ido da zuwa Hotels, su kama daki su wuni suna hira da yan mata a kashe musu kudi. A tun ana fitar rana har ta kai an koma ta dare. Idan ya dawo gida da Magriba ya gama uzurinsa ze salla wanka ya fita, Binta ta bararraje a gida hankali kwance ita kadai Babu Bara'atu. Bata wani damuwa da fitar tasa tunda tana samun duk wasu buqatunta idan ya zauna a gidan ma.me zeyi mata kuma a tunaninta be kawo mata cewar gurin Mata yake zuwa ba musamman data san yana harkoki da yawa yanzun.
A irin wannan yawaye yawacen Bashir ya kwashe su gari ya gari har kwantagora, basu san inda zasu ba seda suka gansu tsulum a gidan Karuwai, wai Ashe Ajo za'ayi shi kuma Bashir din da yake babban kwastoma ne kusan duk wata Karuwa data amsa sunanta a Kano yasan da zamanta to dalilinsa na zuwa kenan harya kwashi Abokanansa suka tafi tare. Ashe qaddarar Haduwa da Zubaida Yar Dagwas ce takai Audun Kwantagora, kyakykyawar yarinya Baqa me matsakaicin jiki yana ganinta Bara'atu ta fado masa a rai, idan yace be damu da rabuwarsu ba yayi qarya amma yakan danne zuciyarsa da cewar tayi abinda ya cancanci ya rabu da ita.
A yanda ya fahimta ko a cikin Karuwan Zubaida me Aji ce domin daga shigarta zuwa yanda take kamewa a gefe tanawa kowa kallon be isa ba ga Maza nata zuwa suna mata magana amma taqi koda yi musu kallo arziqi balle ta karbi tayinsu, bayan an tashi daga Ajo Bashir ya wuce sharholiyarsa Ali da Audu na zaune a dakin da suka sauka. Babu irin macen da Bashir be tura musu ba amma Ali ya kore su.
"Bana fatan na daukarwa Ahalina bashin zina dan ban san wanda ze biyashi ba, iya abinda mukeyi Allah ya yafe mana shima ina masa fatan ya shiryu ya dena abinda yakeyi" Ali ya fadawa Audu sanda yaga shaidan yana qoqarin ingizashi ya karbi tayin wata Kilaki datazo kansu tana duk wani abu data san zeja hankalin Namiji gareta, Alin ya mata korar kare.
"Nifa Ali da akwai yarinyar dana gani, kuma wlh ba sha'awarta nake ba ji nayi kamar sonta ya kamani a kallon farko" Audu ya fadawa Ali abinda yake zuciyarsa dan tunda ya zauna Tunanin Zubaidan yakeyi duk kuma macen data shiga se yayi fatan Allah sa idan ta fita ita ce zata biyo baya amma be ganta ba.
"A nan kaga macen da kake so? Ko kuma kawai kace mun kaima zaka fada ruwa" Ali ya fada yana gyara kwanciyarsa.
"Wallahi dagaske nakeyi, baka kuka da ita ba? Wata yar baqa haka ta saka jan kaya, dana kalleta se na ganta kamar Matata ta farko da muka rabu tunda na zauna a nan nake tunaninta" Audu ya sake fada. Ali ya juya masa baya yana cewa
"Lallai ka haukace Audu" daga haka yayi shiru. Audu kuwa be iya runtsawa ba se gabanin Asuba, tunanin Zubaida ya addabi ransa. Jin ta yakeyi a zuciyarsa kamar wadda ya shekara da sani abin tamkar Asiri a dan baccin da yayi kafin gari ya waye ma har mafarki ta yayi.