← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 137

Sashe 58

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ita ta kitsa maganar kenan, Binta! Binta! Wannan yarinya anyi shaidaniya amma babu komai karki saka damuwar komai a ranki ki kyalesu daga shi har itan kici gaba da kula da kanki da abinda yake cikinki. Idan kinji gidan ya miki qunci ki taho gidanmu tare mukazo da Balaraba kuma zata jima a nan dan zan tafi na barsu se na dawo sallah sannan zamu koma baki daya sannan dan Allah maganar nan ta tsaya ikar cikin gidan nan karki gayawa kowa in sha Allahu komai ze warware kansa kinji" Yakubu ya fada mata cikin lallashi. Ta share kwalla tace

"Shikenan zan zauna kamar yanda kace zan kuma cigaba da roqon Allah daya zabamun mafi Alkhairi, tabbas nayi dana sanin Auran Audu saboda bansan haka yake ba. Ban taba tsammanin bayan tsamoni da yayi daga rayuwata ta baya ba kuma zeyi amfani da hakan ya rusamun rayuwar dana ke qoqarin ginawa a gaba. Yanzu idan yaqi karbar dan da zan haifa ya zanyi? Da wane ido duniya zata kalleni?"

"Karki sake fadar haka babu abinda ze faru da kuma halastacce da ne da kansa ze amshe shi ba tare da wani ya tilasta masa ba, kedai Allah ya sauke ki lafiya kawai kinji kiyi haquri kuma kici gaba da Addu'a" daga haka yayi mata sallama ya tafi ta maida jakarta daki amma bata bude ta ba domin har zuciyarta bata aminta zata iya cigaba da zama da Audu ba. Bata shiryi qare rayuwarta cikin qunci da baqin cikin Miji da kishiya ba. Ta sani daman dole zata riski qalubale masu tarin yawa a rayuwarta amma bata tsammaci ta haka zasu bullo mata ba.

Shiru shiru ta tsammaci Audun ze shiga ya mata masifa amma har wayewar gari bataji duriyarsa ba haka suka kwana biyu ko qofar dakinta be leqa ba se a kwana na uku da dare tana zaune ya shiga ya tsaya daga bakin qofa ya miqa mata takadda fara a linkife fuska babu Annuri ta karba ta bude bata iya karatun boko ba dan haka ta mayar ta rufe ta ajiye a gefenta ba tareda ta tankashi ba.

"Baki ce komai ba, ko bakiga abinda yake rubuce a ciki bane" ya fada cikin murya me kauri, ta daga kai ta kalleshi irin kallon nan na daidai nake da lokacinka kafin tace
"Ka rubuto mun da Ajami idan kana so na gane abinda yake ciki har na baka amsa". Yaja tsaki ya koma inda ya fito. Tun randa Yakubun yazo yake auna daya da biyu akan yuwuwar ya amince da cikin jikinta amma ya kasa, Shaidan ya rigada ya yi kane kane a zuciyarsa yana raya masa abubuwa kala kala ga qaramar shaidaniyar dake nan gefensa tana qara ingizashi, duk yanda yaso daya daure yayi mata uzuri ya kasa musamman idan ya tuna dalilinta Yakubu ya yaba masa baqaqen maganganu ya kirashi jahili se yaji babu abinda zeyi ya huce irin ya saketa kawai hakan ko yayi ya rubuta mata saki har biyu a takarda ya linke ko Binta bata san da ya rubuta sakin ba se da kuma ya bata sannan yaji cewar yayi wauta data bude yaga babu damuwa ko kidima a fuskarta. Tuna masa da tayi bata iya karatu ba ya sanyaya masa zuciya kenan bata san me takaddar ta qunsaa ba da wannan sanyin ya juya ya tafi yana ayyana ze dawo ya dauke takardarsa kawai ya fasa.

Safiya nayi ta shirya ranar Asabar baya fita da wuri kuma da yake yanayin sanyi ya fara kankama kowa na daki yayi luqui a ciki. Ta dauki jakar kayanta da takardar daya bata ta kama hanya, tsakaninsu da gidan Yakubu babu wata tazara me nisa dan dayan tsallaken Titin Audun ya maida masa da filin sa daya karba yayi madaidaicin gida. Ta zabi da taje gidan Yakubu ne saboda ko babu komai shidin ya jibanci lamarinta sannan tana tsoron yanda Mahaifinta ze karbi wannan Al'amarin idan taje tana buqatar wanda zeyi masa bayanin da ze sauqaqa masa tashin hankalin da komawarta gida da cikin da ubansa yake kokonto ze jefashi a ciki.

Balaraba na tsakar gida tana kauda kayan wasan yara da bata samu ta kwashe jiya da suka gama wasan ba taji ana qwanqwasa Get ta bude ganin Zubaidan ya bata mamaki sedai labarin da Yakubu ya bata na abinda ke faruwa a gidan Audun ya kauda mamakin nata ta matsa mata ta shigo tana mata sannu kafin ta karbi jakar hannunta. Bayan sun nutsu a falo, ta kawo mata Ruwan shayi da su madara da burodi tace

"Bari na soya dankali, bari nayi da se sun tashi a bacci tukunna"
"Ki barshi wannan dinma ya isa" Zubaidan ta fada a sanyaye amma Balaraba ta wuce kitchen tana ce mata yanzu zata gama.

Daidai wanda zataci ta soyo mata da kwai ta kawo, ta kalli kayan shayin na nan yanda ta ajiye su tace
"Na dauka kin hada shayin ya sarara kafin ma gama? To bari na hada miki"

"Baqi mukayi ne?" Suka jiyo muryar Yakubu dake fitowa daga daki yana tambaya. Balaraba ta amsa da cewar
"Baquwa dai" ya qaraso ciki yana kallon Zubaidan sam beyi mamakin ganinta ba domin yasan halin taurin da kafiya irin na dan uwansa. Yayi mamakin da har aka kwana hudu ma sannan ya ganta a gidan nasa.

*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*

*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓

*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*

*Muna da magunguna iri iri*

*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*

*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*

*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*

*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,

*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*

*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*

*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*

*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*

*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*

Seda suka gaisa kafin ta zaro takardar da Audu ya bata ta miqa masa ba tareda tace komai ba, ya bude ya karanta yayi shiru kamar ruwa ya cinye shi kafin ya ninketa yana sauke ajiyar zuciya ya miqe tsaye.
"Ki gyara mata dakinki seta zauna ciki kafin muga abinda Allah zeyi" ya fadawa Balaraba ya shige ciki. Balaraban ta miqe a sanyaye tabi bayansa ita kuwa Zubaida Fulas taja ta shiga hada shayi daidai wanda ze isheta ta tabbata dai saki ne a cikin takardar, ita kuma a kullum ta tashi Addu'a bata mantawa da neman zabin Allah a dukkan lamuran rayuwarta dan haka duk abinda ya sameta zata karbeshi da kyakykyawan Ikilasi.

A dakin Balaraba tayi masauki tana ta jaddada mata ta saki jikinta tamkar tana gida. Bayan da su Dada da qannenta biyu suka tashi daga bacci su suka ringa debe mata kewa harta manta da damuwar data kawota gidansu ta ringa jin zumudin itama dan cikinta ya fito duniya ta tabbatar koshi ya isa ya ringa bata nishadi yana debe mata kewa. Ta tuna sanda tayi cikin da bayan zubar dashi Audu ya maidota gida a lokacin taso ta bar cikin ta haifeshi saboda ta shirya barin rayuwar Bariki. Ta so ta haife dan ta raineshi da yaqinin wannan abin ya saka ta samu rangwame a gurin ubangiji na daga tarin zunuban data dibarwa kanta sedai daga baya tunanin irin rayuwar da Da ko yar da zata haifa da qalubalen da zasu fuskanta yasa ta kasa idar da qudurinta.

Sanda wannan cikin ya bayyanar mata tayi murna kwarai musamman dataga irin tarin murna da Zumudin da Audun ya ringayi shima ta ringa hasaso yanda zasu raini abinda zata haifa tare ashe duk mafarki takeyi zanen qaddararta daban abinda take tsarawa a zuciyarta daban.

Bayan fitar Yakubu har ya dauki niyyar zuwa gidan Audu se kuma wani tunani yasa ya fasa hakan, a karo na biyu kenan daya sake yanke danyan hukuncin da yake ganin hakan daidai ne a rayuwarsa.

A bangaren Audu seda hantsi ya daga kafin ya shirya ya fito ya nufin dakin Zubaida dan ya karbo takardar jiya. Ya tura qofar dake a bude ta sakayata yana sallama ciki ciki shiru babu motsi Tv da Radio da take yawan kunnawa duk a kashe dan haka ya dauka bacci takeyi seya wuce uwar daki nan ma qwalam bata nan. Tsaf ya bincike ko ina be ganta ba kuma bega takardar ba, yanayin dakin da be nuna alamar an dauki wani abu ko an hada kaya ba yasa yayi tunanin ko maqota ta leqa amma wannan ba halinta bane musamman da duk maqotan yan fadar Binta ne dukda haka ya qaddara wani gurin ta leqa seya koma daki da niyyar kafin ya gama shiryawa ta dawo.
Chapter 58 · 0% Book details