Sashe 137
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Alƙali Yakubu be damu da cewar a Reception ɗin Asibiti suke ba kuma da mutane suna ta kai kawo a gurin duk anyi cirko cirko ana sauraronsa ya wanke Hajiya Binta tas da soson kaba haɗi da klin da hypo, yanda yake maganar murya a sama zaka tabbatar da cewar yau zuciyar Mazan ta harzuƙa dab kuma yake daya kwasa mata mari muddin tace zatayi inkari akan abinda yake faɗa. Hajiya kuwa hannaye biyu ta aza akai tana kuka tana cewa
"Daman na sani kaf dangin Audu babu wanda ya tsaneni ya tsani zuri'ata irinka Yakubu, ni kake kira La'ananniya? Nice shaiɗaniya? To bari naje seya tashi ya Zaɓa koni ko kai. Idan kai ya zaɓa daga nan gidanmu zanyi dan babu abinda ze sake zaunar dani a inda ba'a san mutunchina dana Zuri'ata ba idan kuma ya zaɓeni wlh se dai ya rabu dakai ya zareka daga Al'amuransa tsaf babu mu babu kai. Shikenan kawai saboda kai matarka bata da zuciyar haifar Yaya Maza seka ringa baƙin ciki da ɗaukakar da Allah ya bawa nawa dana haifa? Ai nasan duk ba komai bane baƙin cikinka saboda Audu nada Magada kuma Yayana nane akan Dukiyar Audu yau idan ya faɗi ya mutu ko sillin gashi baka da gado a cikin tarin Arziƙinsa. Takaicinka kuma yanda kullum Yaya nane a gaba sunfi duk sauran yayan da aka haifa a gidan Ƙashin Arziƙi".
Alƙali Yakubu yayi wata dariya, da alamu ya mance da inda suke shiyasa yake zaro maganganu duk yanda sukayi masa. Kallonta yayi sama da ƙasa yace mata
"Ina Alfahari da Yayan da ubangiji ya bani Mata, Namiji gudan daya bani ya fiye mini taron Yuyuyu irin wanda ke kike iƙirarin kin haifa. Ke hai kinyi haihuwar da zaki bigi ƙirji kiyi Alfahari da ita Binta? Arziƙin yayan da yake cuɗanye da na sata da na ƙazantacciyar harƙallah? Bari kiji, wlh idan naso jirkita rayuwarki a cikin taƙaitattun sa'oi se kin bazama neman inda zaki boye a cikin ƙasar nan, kije ki fara gyara tarbiyyar Yayan da kike tinƙaho dasu kafin su zama abin Alfaharin, ina mai tabbatar miki Binta da raina ko na mutu akwai ranar da baƙin cikin waɗannan yayan da kika cuta kika gurbata musu rayuwa kika koya musu zalama da rashin wadatar zuci irin naki se sun saukar miki da Ciwon da in bakiyi wasa ba shi zeyi Ajalinki"
"Dan girman Allah Baba kayi haƙuri, ba anan ya kamata ayi maganar nan ba, Ahalinmu sanannu ne yanzu se kaji zanje yana tashi a Kafafen sada zumunta daga nan Allura seta tono garma" Dr Hassan daya matsa kusada Baba Alƙali ya faɗa yana kama hannunaa, shiyasanme Alƙalin yake magana akai.