Sashe 49
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A haka dai gata kamar salaha amma wai tsohuwar kilaki kai jama'a Allah ka tsarkake mu ka tsarkake mana zuri'a" wata da bakinta bashida birki wadda kuma ta fita danyan kai ta cafe tana cewa
"Kedai bari Tsahare, aini abinda yafi bani mamaki ma Audun daya dakko wannan aba, anya ba juyar masa da hankali tayi ba dan dai wannan al'amari beyi kama da na wanda yake cikin hayyacinsa ba sedai aikin sihiri" seka rantse su kadai ne a gurin yanda sukayi maganar hankali kwance babu wata damuwa tattare dasu kamar wadanda aka saka maganganunsu kuma sun isa kunnen kusan duka mutanen gurin, Zubaida ta sake sadda kai qasa kuka na neman kwace mata, abinda take gudu kenan wanda ta tabbatar da seya faru, shi yasa bata tsarawa kanta yin aure ba koda ace ta bar rayuwar bariki sedai komai ya faru kafin ta farga, haduwarta da Audu, komawarta gida ga kuma aure ubangiji ya fita sanin hikimar yin hakan kuma koma yayane ta godewa Allah daya tsamota daga mummunar rayuwar data fada ba kuma zata butulce masa ba zatayi haquri ta jure duk wani qalubale da zata fuskanta amma tabbas tana tausayawa kanta tana kuma tausayawa Yaran da zata haifa a gaba dan ta bar musu abin gori har jikokinta idan ba'ayi wasa ba.
"Meye haka Jamila? Ke Tsare wace irin magana kukeyi haka saboda Allah?" Goggo Fadi ta tsawatar musu, a maimakon maganar ta mutu se ya zama abin cece kuce, wanda a kunji kunji sukaji labarin suka gasgata qus qus ya tashi ko ace qaramar hayaniya kowa na tofa albarkacin bakinsa masu fadar Alkhairi nayi masu tofin ala tsine sunayi wannan ya tilastawa Zubaida da qanwarta Surayya fashewa da kuka sauran yan uwansu kuwa jikinsu yayi laqwas tamkar an watsawa Kaza ruwan zafi. A can Kano a unguwarsu ba kamar yanda ake taammata ba Zubaidan bata samu qalubalen kyara ko hantara ba domin har wanda basu santa ba labarinta suka samu a sanda ta dawo sun karbeta hannu biyu saboda wannan ya taimaka mata gurin sakewa ta fara manta rayuwarta ta baya ta fuskanci gaba.
Sun dauka yanda suka manta komai haka sauran Al'umma zasu manta sedai basu san wasu yanzu nema suka samu abin jajantawa da gorantawa. Yanda maganganu suke tashi ya saka dole aka maida Amarya daki tana rusa kuka kamar me domin babu shamaki suke aibatata, tamkar Binta zata taka rawa saboda murna, gumu yayi gumu, masu tsawatarwar basu da yawa dan haka maganar taqi mutuwa har seda. Maza suka shigo ciki, Tsahare uwargidan Yaya Baba data fara tada zancen seda ta karbi Tukuicin saki daya, Jamila matar Aminu data tayata dai ya aikata gida itama amma be furta saki ba, wannan yasa washe gari Asubar fari Audu ya kwashe su suka bar Bechi bayan ya kaftawa Matan Yayyen nasa da sauran Jama'a dake gutsiri tsomar warning, Yan uwanta dai saboda mutuwar jiki basu ko iya rakata dakinta sukace da Direban daya kaisu ya maida su inda ya kwaso su, saga ita se Audu da Binta suka wuce gida.
Kwanakin Amarcin Zubaida dai basu zowa Audu a yanda ya tsara su ba dan abinda ya faru a Bechi ba qaramin tabata yayi ba gaba daya ta rasa nutsuwarta balle ta samar masa da tasa. Abin yawa Binta sugar har ta ringa ganin wautarta da tun farko bata hasaso haka ba, data sani Bechi ta tafi tun farko ba Kaduna ba, qila da yanzu gori ya saka Zubaidan neman saki da kanta amma yanzun ma ta samu nayi, ba duka ba zagi amma In sha Allahu da kanta zata tafi dan ba zata barta tasha ruwa a gidan ba. Yanda Angon duk yake a wani sukurkuce ya qara bata damar kafa kanta da nuna masa ita ta Allah ce har a gabansa ta ringa tausar Zubaidan tana gaya mata ta cire komai a ranta ta bar ta mutane. A haka Audu ya gama kwana ukunsa ya komawa Bara'atu kafin yayi kwana biyu ya dawo Qanwar Mahaifiyar Zubaida ta kai mata ziyara. Ita tayi mata maganar data maido da ita hayyacinya, ta gaya mata damuwa ko kuka ba zata mata maganin komai ba qaddararta ce a haka kuma me afkuwa ta afku dan haka ta manta baya ta toshe kunnenta daga jin duk wasu munanan Kalamai ta kuma maida hankali ta gyara gidan Auranta domin a yanzu bata da kowa bata da komai se Mijinta da gidan Auranta, ta dage ta nemi Aljannarta ta kuma tabbatar da cewa tayi tuba na gaske, abubuwan data aikata a baya da suke laifi yanzu lada zata samu akansu dan haka ta dage ta kama Mjinta.
Wannan ya zaburar da ita randa Audu ya koma Dakinta Binta bataviya bacci ba saboda lukutin tashin hankalin daya sameta, a garin muguwar dabi'arta ta labe ta jiyo abinda ya kusa zauta mata tunani. Ta yi qoqarin shiga dakin ta dakatar dasu daga abinda sujeyi amma qofar a kulle dole ta wuce dakinta tana kuka wiwi qarin takaici da baqin cikin yanda Audun ya bude baki yana ihu tamkar farin shigan Hauka yanda kasan yau ya fara sanin Mace, washe gari kuwa taga qarshen bariki dan bata tsammatar Audu ya fita sallar Asuba kuma bataga kyallin idonsa ba se yamma lis shima tareda Amarya suka fito suna raha da dariya hannayensu sarqafe da juna yanayin shigarsu ya nuna mata cewar fita zasuyi.
"Idan na yarda Allah ya tsine mun albarka" ta fada yana miqewa tsaye harda cire dan kwali tayi damara.
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE 19*

Duk su biyu suka dakata suka kalleta, fuskar Zubaidan dauke da murmushi harda rausayar da kai tace
"Ina wuni Yaya Binta?"
"A gidan ubanwa na zama yayarki? Ni zako gwadawa Karuwanci? Koda yake na manta sana'arki ce ai ba a qasa kika tsinta ba" Bintan ta fada murya a sama,
"Meye haka ne Binta? Ke baki iya magana a hankali bane dole se kin daga murya kamar meyi da mutanen sama sannan wannan damarar da kikayi ta mecece haka?" Audu ya fada yana kallonta se kuwa ta shiga qara tamke damararta tana cewa
"Ba shakka dole ka tambayeni me nakeyi haka wato kaima an dora maka darasi irin nasu na tsofaffin kilaki ko? Saboda tsabagen rashin Adalci tun daren jiya rabona dana sakaka a ido, haka ka kwana kana kurma ihu a gidannan kamar wanda ya samu abinda baze qare ba sannan yau ko kyallin qeyarka ban gani ba se yanzu zaku fito cikin shiri da alama ma waje zakuyi wato ga banza jaka ka ajiye wlh ba zan yarda ba" ta qarasa maganar tana qoqarin fashewa da kukan takaici saboda tuno daren jiya da tayi.
Wani murmushi me tafe da qaramar dariya Audun yayi ya kalli Zubaida data sunkuyar dakai, Karuwa da Binta ta kirata ya soki ranta amma tayi shiru tana qoqarin danne damuwarta tareda hana kanta karaya a gaban Bintan,
"Ashe dagaske kike da kika ce duk maqota suna jina yanzu yaya zan kalli mutanen waje idan na fita bayan na tafka abin kunya qato dani ace yar yarinyar kamar ke ta sakani ihu a daki? Gaskiya mu koma an fasa fitar nan gara na hada kunyar jiya data yau gaba daya gobe na fita dan bazan fasa ihu ba"
Da Binta ta rasa abin fadi se kawai ta fasa kuka me kama da ihu ta juya ta shige daki, Zubaida kuwa dariya ta fashe da ita tana kare fuska saboda kunyar maganar tasa,
"Mu koma ciki" ya sake fada yana kama hannunta ta zame tace
"Babu ruwana kaje ka rarrashi Yaya Binta kar kasa ta qullaceni"
"Ki barta zan lallasheta gobe dan bazanso abinda ze sosa mun rai ba bare harya hanani ware murya dakyau nayi ihun dadi"
"Allah ya isa tsakani na dake yar iskar Karuwa, idan ma kuma Asiri kikayi kika shigo gidan nan na rantse da Allah sena karyashi zaki gane dani kike zanje" Binta data fito da Hijabi a jirkice ta fada cikin kuka kafin ta fice daga gidan ko ina zata se Allah,
"Ka bita mana kana kallo ta fita" Zubaida ta fada cikin yanayin damuwa, ko a jikin Audu ya juya ciki yana cewa
"Duk inda taje ma zata dawo" daga haka ya jata suka koma ciki fitar da suka niyyata aka fasa.
Binta kuwa bayan fitarta rasa inda zata nufa tayi, Turai bata nan ta tafi Gumel suna Yayarta ta haihu kaf Kano kuma ita kadai ce qawar da take kaiwa kukanta. Haka nan tasha kwana ta tasamma gidan Lantana wanda tunda ta fara mata aiki shekara uku kenan sau daya ta taba zuwa sanda Salisu Babban dan Lantanar ya rasu se yau data rasa gurin zuwa kawai zuciyarta ta raya mata taje can. Lantana da makwaftanta biyu na tsakar gida sun baza faifan Binta suna caccaka, haka nan kullum aikinsu kenan yanzu labarin kishiyar da aka mata dake neman zauta ta take basu
"Ai in gaya miki alqadarinta ya karye, badai ta kori ta Allah ba ai gashi nan an hadota da wadda zataci ubanta ta kowanne fanni, kilaki fa akace yo har a gaya mata iya kissa da kisisina" daya saga cikin matan ta fada, Lantana ta buga cinya ta bude baki zata bada sharhi Binta ta doko sallama suka zabura gaba daya daka kallesu kaga marasa gaskiya
"Hajiya, kece?" Lantana ta fada bayab data miqe tana sosa kai kamar me kwarkwata, Bintan ta kallesu irin kallon raini kafin ta nufi wata Farar Kujerar roba dake ajiye a tsakar gidan,