← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 137

Sashe 19

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana i gobe zasu tafi da maraice Balaraba ta haihu ta samu ya mace wannan karon Ubangiji ya bata da sauqi dan da tasowar ciwon gaske da haihuwar beyi awa daya ba, Audu ya fita qaraso musu siyayyar dan abinda zasu buqata kafin su koma Kano se dawowa yayi ya tarar da yar Baby me kama da Dadarsu sak haka ya kwasheta seda sukaje Asibiti aka tabbatar ita da yarta duk lafiyarsu qalau, farin ciki ba'a magana, Yakubu yayi mata hudu ba da Hafsatu zasu ringa kiranta Dada dan duk wanda ya gabta se ace Dada ta tafi Dada ta dawo. Haihuwar tasa suka qara kwana biyu, yan Uwan Balaraba suka dauketa zuwa gida wanka Audu ya wuce Kano tareda Yakubu daze koma Ikko. Wata daya bayan haka Audu da Bara'atu tareda Baballiya sukayi qaura Kano, qarshen zamansu a Bechi kenan.

Ranar da zasu tafi mota guda ya dakko aka kwashi yan rakiya dan an kwashe kayansu daman tuni. Yan uwan Bara'atun uku Yayarta daya se Matar wanta da qanwar Babarta sauran sukace a hankali zasuje suga inda suka koma se murna suke tasu ta koma Birni suma sun samu gurin zuwa haka Inna Hajara har wani qafafa take tana yadawa wanda suka ringa Adawa da Auran Bara'atun da Audu magana ciki harda Babanta. Yan gidansu Audu ma kafataninsu su Bilki dasu Amina harda Matar Yaya Baba data Aminu da Amaryar Hashimu wadda se bayan sun tafi ya samu labari ya ringa tijara yana rashin mutunchi Goggo Fadi da tabi hanyar Allah tuni tun bayan rasuwar Dada batace masa qala ba, ita kanta taso zuwa amma ciwon qafa daya sakata gaba kwana biyu ya hana amma Audu ya mata Alqawarin da kansa ze dawo ya dauketa taje ta kwanar musu biyu kuma tafiyarsu ba tana nufin sunmanta dasu bane, basu da wasu dangi a duniya bayan su, su goman nan da Mahaifinsu ya haifa sune dangin Kansu.

Yan Bechi suka ringa santin gida, kwanan su daya suka juyo Audu ya hado su da sha tara ta Arziqi qememe Abdullahi yaqi bin Babarsa Audu yace a barshi daman ai Abdullahi Dansa ne, uwar bata so ba dan daman ita ba wai son zaman da yake a gurin Bara'atun take ba kawai dai dan Aminun tsayayyae ne yasa ta kasa magana yanzun da Audu yace a barshi tace
"Amma Babansa be sani ba zeyi fada idan aka koma babu shi"

"Idan kin koma ki gaya masa ni Audu na riqe Abdullahi idan yana da jaa yazo ya dauke shi da kansa" ya fada mata zata sake magana Amina ta harareta tana cewa
"Sedai kece zaki cr bakya son zamansa a nan dan dai Yaya Aminu ya dade da fadawa kowa ya barwa Audu Dan nan kuma wannan baqin ciki kikewa Danki ze zauna a Birni yayi Karatu me kyau ya tashi a waye"

"Meye haka Yaya Amina?" Audu ya katseta, ta sake cewa
"Gara na fada mata ai idan kuma ta ce se a bata danta gashi nan ta tarkata su tagi dana Koma zan hadowa Muzammilu kayansa a kawo maka shi ga Yaran nan tuli a dangi har wanda zaka riqr ze gagara ne?"
"Audu yayi murmushi kawai jin abinda tace ya tashi ya fita bayan ya Ajewa Aminar saqon maganin ciwon qafa yace ta kaiwa Dada, haka suka koma Bechi aka bar su Bara'atu a sabon guri.

Sannu sannu rayuwa taci gaba da tafiya, Balaraba ta yada wanka har taje Bechi daga nan tayo Kano ta kwanarwa su Balaraba Biyu kafin suka kama hanya da Audu daze rakata dan Yayanta Iro ya tafi da Shanu matarsa kuma tana da ciki ta kusa haihuwa wannan yasa Iyayensu sukace ta zauna ta haihu tukunna ta koma. Seda Audu yayi sati ya dawo rayuwa taci gaba. Sosai kasuwancinsa yake garawa. Kudin gonar su da suka siyar ya qara jari da shekara ta zagayo sun ninka kansu wannan yasa ya shawarci Bilki data kawo musu ziyara akan me ya kamata suyi, sun yanke cewar su nemi qananan Gonaki a ringa siya ta yanda a hankali kowa ze mallaki tasa aci gaba da juya kudaden kamar yanda yakeyi yana kuma fitar da riba yana bawa kowa saboda buqatu, gidansu ma Bilkin cewa tayi suyiwa su Hashimu tayi ko zasu siya dan ya mayar da gurin Rumbu kayan gonarsa yake ajiyewa a ciki Audu yace mata Aa su barshi saboda idan sunje su samu gurin sauka ze dai saka a gyara gurin a hankali.
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR*
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*HALIN KISHI*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*FREE PAGE 9*

Ranar wata Talata Bara'atu ta sauka a Asibitin Murtala inda Audu ya yankar mata katin Awo tun bayan dawowarsu Kano ta samu Da Namiji murna gurin Audu dasu Baballiya ba'a magana, wata maqociyarsu Baba Larai da suke mutunchi da Bara'atun tun tarewarsu ce tayi mata biqin kwana biyu kafin Audu ya tattarasu suka tafi Bechi, se ganinsu sukayi da jinjiri aka ringa murna a gidansu ta zauna seda akayi suna yaro yaci sunan Malam wato Tijjani suke kiransa da Babangida, Raguna biyu manya Audu ya yanka haka ya mata kayan barka irin na Birni duk inda ka shiga a Bechi labarinsu akeyi, lafiya lau tayi wankanta kwananta Hamsin da Haihuwa suka dawo Kano rayuwa taci gaba da garawa cikin ludufi da Amincin ubangiji.

Kasuwancin Audu kam yana habaka dukda dai har sannan yana kan canje canjen sana'a dalili da duk wadda ya fara tabawa da an kwana biyu se abin ya fara sakin hannunsa tilas yake sake cafkar wata sana'ar ya dora wannan dalili yasa yana da ido acin kusan duk wata sana'a da ake juya kudi a samu riba, ba babbab ba qarama duk yana tabawa ita kanta Bara'atu be barta a zaune ba ya sakata tana taba sana'oi na mata na cikin gida kuma tana samu babu laifi ga Kitso da daman ta iya shima tanayi shiyasa idan suka tashi zuwa Bechi Sallah, Biki ko suna bayan abinda Audu ze bata haka itama zatayi ta Alkhairi wa yan uwanta da nasa, gida su kuwa baya rabo da dangi duk wanda ya samu dama ze zo Kano ya kwanar musu biyu ya koma.

Yakubu na Ikko abinsa tunda Balaraba ta bishi seda suka shekara biyu kafin suka zo lokacin ya rage masa shekara daya ya kammala karatunsa kenan. Daga shi Har Balaraba idan kalle su seka qara, Yakubun ya waye ya zama wani baqin Bature hatta shigarsa ta canza zuwa coat baqa da farar yar ciki irin dai shigar su ta masu karatunshari'a ita kanta Balaraba Turanci har ya kama bakinta saboda suna tsakiyar wanda zo in kashe ka basu sani ba da Hausa. Ga Dada data jima da yayewa tayi kubibi abinta fatarta me haske irinta uwarta har sheqi take saboda zama cikin lullumi ga cin naman ruwa da suke se tsohon cikin da take dashi haihuwa ko wanne lokacin dalilin dawowar tasu ma kenan.

A Kano suka sauka suka ringa yiwa Juna tsiya ita da Bara'atu da itama take dauke da ciki na Biyu watannin Babangida goma sha daya ta samu ciki sati daya kenan Inna Hajara ta dauke mata shi tunda ta kusa sauka amma ba bisa son ran Audu ba. Seda suka kwana biyu suka huta kafin suka tafi Bechi gaba daya niqi niqi da tsaraba daga can Balaraba taje garinsu su kuma suka juyo Kano seda ta gama kwanakinta ta dawo.
Zamansu gwanin dadi, idan safiya tayi Mazajensu suka fita Kasuwa inda Yakubu yake bin Audu Baballiya da Abdullahi su tafi makaranta duk wadda ta riga gama aikin bangarenta zata shiga gurin yar uwarta, nan ma girki daya suke kowa ta dibarwa iyalanta.

Wannan karon ma Balaraba ce ta fara haihuwa ta sake samun Mace kwana biyar tsakani Bara'atu ma ta haihu ita kuma Namiji wannan Dalili yasa Audu da Yakubu da duk sukace babu wadda zataje gida aka hade taron suna, ranar kwana bakwan Balaraba akayi mata yanka yarinya taci suna Maimunatu amma taro seda da dan Bara'atu Yusuf dayaci sunan babanta ya kwana bakwai akayi Yan Bechi sunzo da dangin Balaraba an sha buduri sosoi taro ya watse se yan zaman wanka da kowacce aka kawo mata daga gida Yakubu ya koma Ikko saboda makaranta haka suka cigaba da wanka Balaraba na yada wanka taje garinsu da Bechi tayi musu sallama Audu ya kaita tasha da Yayanta suka bi Yakubu Bara'atu kuma taci gaba da rainon Babannan da Babangida wanda Audu ya kafa kwarzaba seda aka dawo masa da Dansa ga kuma Baballiya da Abdullahi abinsu gwanin Dadi suke zaune.

Bayan Baballiya sun rubuta jarabawar kammala sakandire wadda tsallaken Aji akayi masa saboda girmansa akayi sa'a kuma yana gane karatun daman yana Aji Takwas suka baro Bechi dan haka suna zuwa Kano Audu yasa aka kaishi Aji biyu na babbar Sakandire, ya dage akan shidai aikin soja yakeyi, tun Audu baya daukar abinda muhimmanci har nacin Baballiyar yasa shi tambayar yanda ake shiga makarantar sojojin. Wani Maqocinsa a Kasuwa ya tambaya dan yanajin yana fadar da akwai qaninsa daya tafi aikin soja, shiya gaya masa qanin nasa yana makaranta a Kaduna shima wani Dan uwan mahaifiyarsu ne dayake zaune a can ya samo masa kuma ance daya gama ze fito a babban soja ne ba kurtu irin wanda mutanen mu a wancan lokacin suke zuwa suyita wahalar banza ana kashe su a yaqe yaqe ba.

Wannan dalili ya saka Audu shirin tafiya Kaduna kai Baballiya makaranta. Yace masa ya shirya kayansa kala hudu zuwa biyar a jaka ya kuma hada takaddunsa, Bara'atu ta ringa musu dariya tana cewa
"Dukda dai bamyi karatu ba amma nasan ba haka taka ake kai mutum makaranta ba dole se anbi matakai ka nemi gurbi idan ka samu kafin ka tafi ko?"
Chapter 19 · 0% Book details