Sashe 124
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Data fara dariya har seda hankalin Lecturer ya dawo kansu duk aka juya ana kallonsu babu ɓata lokaci kuwa ya korasu waje kuma har sannan ba wai ta bar dariyar bane guri ma ta samu ta zauna tana ci gaba da abarta dan harga Allah abin na Afeeyah mugun bata dariya yayi, Jay Afeeyah zatace ta gani a cikin ABU Zaria? Jay ne ze shigo Zaria ba tareda garin ya girgiza ba? Da ace Afeeyah na kallon Ball ko ta taɓa nuna ra'ayi akan Jay Footballer da se tace tsabar yanda ta kwallafa rai akansa ne har yasa ya fara mata gizo amma yanzu ta tabbatar wani ne yake so yayi mata wasa da hankali amma ya akayi har Afeeyah tayi falling wa cheap trick kamar wannan da sauri haka?
"Bana son iskanci Badar me kika daukeni ne?" Afeeyah ta faɗa a fusace se Badar ta nuna ta tace
"Da alama zaman da kikayi a waje kwana biyu kinyi gamo dan wannan maganar da kike batayi kama data me cikakken hankali ba". Ran Afeeyah ya ɓaci ta hayayyaƙo mata tace
"Wato kin gama akan Ahmad yanzu kuma kin samu sabo ko? Wani Badar me kika ɗaukeni ne? Alfarma maza sukeyi mun su soni ko kuwa ban kai macen da za'a ce ana so ba?".
Kafin ta bata amsa Sahid ya kwaso da gudu kamar wani ƙaramin yaro har yana ture waɗanda suke fitowa daga class ɗin alamar an gama lecture ya tsaya a gabansu yana haki yace
"Afeeya i have been looking for you all round the school, na yesterday i remember where i know that Guy's face from, he is JAY Afeeya the great JAY of Gunners was in front of me but i couldn't recognised him God i was so stupid, definetly my village people are behind this misfortune but still I'm lucky and I'm happy that i gave him your number i hope he called? If yes please Afeeya do me this favour of introducing me to him as his ride or die fan wallahi....."
"Sahid haba mana ya isa" ta dakatar gashi ganin maganar bata da alamar ƙarewa s zuba yake kamar wanda kanda ya ƙone, a fusace ta sake maida kallonta kan Badar dan ta ƙarasa zazzaga mata abinda ke ranta rungunar da tayi mata tareda fasa ihu kamar zata toshe mata kunne bata ko damu da a waje suke ba ta shiga tsalle tama kasa magana kamar wata wawiya se ihu takeyi.
"Innalillahi Badar kinyi haukane ko yaya sakeni dan Allah karki kayar dani" Afeeyah ta faɗa tana Ƙoƙarin yakice Badar amma taƙi sakinta cewa takeyi
"Da gaske JAY ne yake son Afeeta innalillahi daɗi kasheni" ta sake fasa wani ihu Sahid na tayata yana mata rantse rantsen wlh shine, yau da safe ya kalli Recap na wasansu kawai ya ganshi shine ya tuna
"Amma taya akayi ya shigo harya fita babu wanda ya ganeshi se ku biyu?" Badar data tsagaita da ihub ta tambayeta, Afeetah tayi tsaki tana tafiya tace
"Seki nemo shi ai ki tambayesa, ni taya zanyi na sani?" a gurin ta barta saboda haushi ta tafi Hostel tana tafe ranta na suya akan abinda Badar tayi mata so takeyi dagaske ta yarda izgilanci yasa take mata irin waɗannan abubuwan amma zuciyata ta gaza karbar hakan.
Da gudu ta bi bayanta dan tayi nisa sosai, ta rungumeta har suna shirin faduwa tace
"Haba mana Afee wai fushi kuma kimayi?" wai dan Allah dagaske kin hadu da JAY? Kedai kina da sa'a Afeeyah ga Ahmad yanzu kuma ga Jay kin samu, na daɗe ina crushing akan JAY amma nasan nisan dake tsakanina dashi kamar nisan sama da ƙasa ne shiyasa na sahalewa kaina Afeeya ke me sa'a ce kina zaune yazo har inda kike ya tarar dake na miki murna Allah ya sakamu a danshinku Miji kam se kin zaɓa kin darje" ta faɗa idonta suna kawo hawayen da batasan na menene ba. Wani iri taji, can kuma haushin cewar da tayi Jay crush ɗinta ne shi yasa ta tureta tana cewa
"Ni dalla cikani, me kika gama cewa? ban kai kalar matan da yake kulawa ba wani ne yake mun ƙarya dashi"
"Afee ki fahimce ni, wlh ruɗewa nayi. Kamar fa nace miki Shahrukhan ya kirani yana sona dan Allah zaki yarda kai tsaye?" ta faɗa da iyakar gaskiyarta, Afeeyah ta fincike hannunta tana cewa
"Ai ni ba shahrukhan nace miki ba, Jafar nace Bahaushe kamata dan Kano kinga kuwa ko sarkin ingila ya zama ba abun mamaki bane dan ya so wadda suke da tushe daya. Sannan naji kamar kince crush ɗinki ne ko? Gara da kika faɗamun tunda wuri ba se anyi nisa kizo kina mun ihu da hayaniya a gaban mutane a kansa ba saboda kishi. Zan gaya masa kina sonsa Allah yasa ki masa tunda yanzu na gane ko Nurain da kike mun masifa kina hanani haɗuwa dashi ashe son sa kikeyi".
"Karki gaya mun maganar banza Afeeya saboda ma kinga ina lallabaki shine zaki ringa botsarewa bafa ke kadai kika iya tijara ba" Badar ta faɗa tana ja baya yanda fuskarta ta nuna lallai taji zafin abunda Afeeyah ta faɗa mata. Itama seta riƙe ƙugu tana kallonta ta sake cewa
"Na faɗa ɗin ko ba haka bane? Duk sanda Nurain ze kirani kin ringa baƙin rai kenan kina bin bini se kinji me muke cewa ba zaki taɓa barina na fita gurinsa ni kaɗai ba haka Ahmad a koda yaushe cikin gasa mun magana kike kina nuna ban kai ba Alfarma yamun daya soni haka kullum cikin yaba kirkinsa kike da nuna da zaki samu kamarsa ba zaki tsaya sokonci iri na ba and now Jafar kai tsaye kin gaya mun he is your crush duk hakan me yake nufi Badariyya?"
"Meye haka Afeeyah lafiya kuke taaye kuna hayaniya akan hanya? Abdurrazaƙ course mate ɗinsu daya ƙaraso gurin ya faɗa. Badar data kasa cewa komai tunda Afeeyah ta fara magana ta tsaya kawai tana kallonta ta sauke ajiyar zuciya kafin jiki babu kwari ta fara tafiya ta barsu a tsaye.
"Yanzu Afeeya saboda abun kunya keda Badar za'a gani kuna faɗa a kan hanya? Ai koma me ya haɗaku kamata yayi kuje ɗaki ku sasanta amma ba anan ba gaskiya kun bani kunya kuma da alama kece bakida gaskiya dan naji wasu daga cikin maganganun da kikeyi" Abdurrazaƙ ɗin ya sake faɗa. Ajiyar zuciya ita ma ta sauke, bata ce masa komai ba ta juya itama ta tafi, Ribadu Hall ta shiga gurin Islam, ƙawartace tsohuwar Roommate dinsu kuma. Ta kwanta akan gadonta duk tana jin babu daɗ kuma akan abinda ya faru amma ta rasa abinda yasa ta kasa controlling kanta duk abinda ya tunzurata kuma cewar da Badar tayi Jay crush ɗinta ne sosai takejin zafin abin a ranta har sannan akan me zata faɗi haka bayan da tasan suna waya kuma hakan yana nufin maganar So ta shiga tsakaninsu?
Islam ta dafa Indomie ta juye a plate kafin ta hau gadon tana cewa
"Tashi muci, in Badariyyah na ganki ke kaɗai? Koda yake nasan faɗa kukayi.
"Naqoshi, kuma wayace miki faɗa mukayi?"
"Ai tunda na ganki ke kaɗai kinzo kin kwanta kamar Manja daman nasan da walakin indai ba bata school ba to faɗa ne kawai zesa ba'a ganku tare ba kuma kece da laifi wato har yanzu dai ba zaku canza hali ba kamar kaji kullum se kun raba hali? Da ana ganin kamar kece abar tausayi Badar ce rigimammiya se wanda ya zauna daku ne ze gane halinki tsaf Afeeyah baki da daɗin sha'ani idan baki so ba"
Ƙaramin tsaki tayi tace "You know how Badar can be annoying, rainin wayonta ya fara yawa wlh shiyasa nake kasa yin shiru yanzu"
"Yes i know, amma Afeeya kin fita zafin kai maganar ta gaskiya. Na san Badar da faɗa amma da wuya tayi akan rashin gaskiya ke kuwa kina sane kike fitittikewa kiyi abu duk kuma yanda mutum ze nuna miki kuskurenki se kinga dama zaki yarda" Islam ta faɗa calmly. Afeeyah tayi shiru dan tasan gaskiya ta faɗa ko a gida haka Ummansu take cewa tanada rikicin gangan kamar yanzun dai in dai gaskiya ne be kamata maganar Badar ta batamata rai ba amma bata san me yasa take hasala ba duk sanda irin hakan ta hado su dukda cewar koda da gaske tana goranta matan ne batayi ƙrya ba, bata kai matsayin da Maza masu Aji kamar Ahmad da Jafar zasu ringa karakaina akanta ba. Ko a layin ƙawance tsakaninta da Badar ɗin kanta akwai tazara matsayinta na yar Ex Sanetor ita kuma ɗiyar me gyaran mota.
"Ke kika takaleta ko?" Islam ta sake tambayarta, a taƙaice ta faɗa mata yanda sukayi da abinda ya haddasa faɗan,
"Ke ɗince ai baki iya magana ba Afeeyah ga rashin fahimta kuma da gangan kikeyi"
"Yanzu ko wani ne yace miki Badar zata so saurayinki Afeeyah seki yarda balle harke da kanki ki ringa wannan tunanin? Gaskiya kin bani kunya lamarinki kuma ya fara shallake hankali. Tabyaya kina zaune da ita for good three years amma ace babu trust a tsakaninku? kin taɓa kamata da laifin cin Amanarki ko me da zaki ringa wannan tunanin akanta?" Islam ta faɗa cikin fushi kamar wata Mamanta. Ta girgiza mata kai alamar Aa kafin tace
"To amma Islam aikin san yanda kullum take mun akan Ahmad, ke kanki shaida ce tasha faɗar da ita ta sameshi da tuni wata maganar akeyi yanzu ba wannan ba"
"To ai ko ni zan faɗa miki wlh dani Ahmad yake so Afeeyah da yanzu na haihu ma a gidansa, dan bazamu rufa six months da haɗuwa ba zamuyi aure. Ke kinsan yanda samun Nagartaccen Mijin aure yayi wuya kuwa? Ki ajiye maganar wasata samun me nutsuwa wanda idan ya aureka ze mutuntaka ya mutunta iyayenka ma kaɗai sunyi wuya balle harda Bonus na Tsabar dukiya ga kyau ke kuwa me kike nema a duniyar nna da baki samu ba kike ta bulayi?