Sashe 102
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To ai kasan sunana Fatima kuma nan ne gidanmu" maganarta ta maido shi daga tunanin daya tafi. Ya saki murmushi, jan Ajin nata ya fara yawa, ya zata kuma tunda har yaga mahaifinta kuma zata ɗan sake masa tasan dai bada wasa yake yi ba. Ya gyara zama yace
"Nasan sunanki Fatima kuma naga gidanku amma ai ni ba iyakar abinda na faɗa miki a kaina ba kenan, na gaya miki mena karanta, aikina har adadin yan gidanmu da wanda nafi so seda na gaya miki fa"
Tayi shiru tana jinsa, idanun daya zuba mata su sukafi damunta da alamu kuma idan ba magana tayi ba baze dena kallonta kamar ze hango yan cikinta ba dan haka tace
"To ai ni banida wani abu da zan gaya maka ne, amma dai kamar yanda nace maka nan ne gidanmu, mu uku ne ai kaga Anty Sauda itace babbarmu se Yah Malam.."
"Jafar? wanda yayi mun sallama da Baffa?" Ya katseta, kai ta ɗaga masa kafin taci gaba da cewa
"Shi nake bimawa, ni kuma banida ƙani ko ƙanwa, ina makaranta a Zaria Level two zan shiga ina karantar English Literature, bayan Baffa da Umma dasu Anty Sauda Ina da Best Friend Badar i think iyakar abinda kake buƙatar sani akaina kenan" ta ƙarasa tana yamutsa baki.
"Masha Allah ku uku kacal a gidanku kenan, ashe ke ɗin Autace shiyasa shagwaɓarki tayi yawa, shekarar ki nawa toh"
"20" ta bashi amsa a gajarce tana ci gaba da murza zoben hannunta. Sukayi jugum shi yana kallonta ita kuma tana faman juya Zobe, wayarsa dake Aljihuce ta katse musu shirun ya cirota ya duba, Jafar ne yake kiransa, ya nuna mata screen ɗin wayar yana cewa
"Jafar ne yake kirana".
Tankar wadda take zaune akan ƙaya ta miƙe da sauri tace
"Ka amsa toh, bari naje ciki kafin ka gama". Kallonta yayi kaɗan ya kasa fassara yanayinta amma dai kamar she is not comfortable with him, ya mata uzurin haɗuwar farko ne dan haka ya miƙe shima yana laluba Aljihubsa yace
"Ai inaga zan wuce kawai idan naje gida se na kirashi wayarmu bata yankewa da wuri ga dare ma ya farayi karna zaunar dake a waje" Kuɗi ya zaro masu yawa daga Aljihun nasa ya miƙa mata yana cewa
"Kinsan farin shigan zuwa hira ne ni, bansan me akw tafiya dashi zance ba kiyi haƙuri ga wanan kisha Sweet kafin na sake zuwa"
"Nagode" ta faɗa ba tareda ta karbi kuɗin ba se wani kallo da ta musu ta ɗauke kai kamar taga wani abunda bata so. Wayarsa ya sake miƙa mata uace ta saka masa Number ta wancan ta goge, nan ma seda taji jum sannan ta karba, ta saka number ta mayar masa. Akan kujerar data tashi ya ajiye mata kuɗin ya juya yana cewa
"Zan kiraki idan na isa gida se kiyi saving number ta. Ki gaida Umma, se na sake dawowa" Ganin ta tsaya kamar wata sokuwa kawai tana kallonsa yasa yayi murmushi ya fice daga soron yanajin wayarsa nata ƙara yasan Jafar ne bala'in wutar ciki ne dashi yanzu idan ba ɗauka yayi ba ya ringa kira kenan ga Mita kamar Mace.
Jiki babu ƙwari ta haɗe kujerun ta ɗauke farantin ruwan da be ko taɓa ba daman tasan ba sha zeyi ba Umma ce tace ta kai masa. Iyayen nata na yar hirarsu ta shiga. Seda ta ajiye kujerun a mazauninsu kafin ta isa gaban Baffa ta Zube kuɗin da Ahmad ya bata.
"Wannan fa?" Baffan ya tambayeta yana kallon kuɗin, a sanyaye tace
"Shi ya bani wai bezo da komai ba danaƙi karɓa shine ya ajiye akan Kujera ya tafi"
"Toh madallah amma idan ya sake dawowa ki gaya masa na hana karki Ƙara karɓan kuɗinsa" Baffan ya faɗa ta amsa da
"Toh Baffa" kafin ta miƙe tsaye zata wuvmce yace mata
"Kwashe kije dasu ai ke aka bawa"
"Ni babu abinda zanyi dasu Baffa" ta bashi amsa tana juyawa.
"Zo nan Mamana, me yake damunki? Ko wani abu yayi miki?" Baffan ya sake dakatar da ita saboda lura da yanayinta sam ba daidai take ba, murmushi ta ƙaƙalo tace
"Babu komai Baffa kaina ne yake sarawa zanje na ƙarasa shirya kayana sena kwanta"
"Toh Allah ya sawwaƙa ki samu magani kisha kafin ki kwanta ɗin idan be dena ba da safe se kije Asibiti, sannu ko" Baffa ya faɗa cikin tausayawa. Seda ta shige sannan Umma ta gaya masa abinda take zaton shine sikar tsumewar Fatima. Yayi murmushi yace
"Ina ruwan Mamana, wato kunya ce duk ta dabaibayeta, to ya za'ayi abu ya rigada ya faru ta yuwu ma ya manta idan kuma ya ganota ya samu abin tsokanarta ai" tana jiyo Baffan daga ɗakiz harta hasaso Ahmad ya dawo da zancen ai lumewa zatayi a ƙasa kawai ta huta.
Harta bacci ya fara fizgarta wayarta ta tayar da ita, Data ta a buɗe yake dan haka taga sunan Ahmad Bechi a truecaller, kamar ba zata ɗauka ba se kuma zuciyarta ta kwabeta kan wulaƙanci babu kyau.
"Allah yasa ban tasheki a barci ba" ya faɗa bayan data amsa wayar, cikin muryar da bacci ya fara tasiri a cikinta tace masa
"Aa".
Ahmad ya gyara kwanciya akan Gadonsa, tunda ya shiga gida suke waya da Jafar daya kai masa ƙarar Hajiya wai ta kirashi akan seya Rantawa Faisal Kuɗi ze fara harkar Crypto kuɗaɗe kuma ba Ƙanana ba take cewa ya bashi ita lissafin Ribar da Faisal ɗin yace mata kawai za'a samu takeyi bata hango Risk da yake tattare da sabgar ba kuma wai rance bama kyauta take nufi harda bashi zuwa lokacin da ze turo kuɗin shine ya kawowa Ahmad ƙararta ita da Faisal ɗin se kace ze iya masa wani abu akai be samu sun gama maganar ba se yanzun yana ta Allah Allah kar tayi bacci ba suyi magana ba.
"Kara zakiyi mun amma muryarki ta fallasaki, kiyi baccinki toh in Allah ya kaimu da safe sena kiraki ƙarfe nawa kike tashi daga bacci?"
"Ko yaushe ma" ta bashi amsa cikin ƙaguwa, ya fiya tambaya take ayyanawa a ranta. Ahmad naso suyi hira dan so yake ta sake dashi da sauri amma kuma bayaso ya shiga haƙƙinta dan haka ya mata sallama akan ze kira da safe dukda bata gaya masa sanda take tashi ba ya kuma jaddada mata kan tayi saving number sa.
Tsaki tayi bayan ta kashe wayar baccin data fara ya gudu se ta shige WhatsApp tana duba saƙonni kafin baccin ya dawo. Dm na samari gasu nan babu Adadi unread messages ɗinta sunfi dari duk ta tsallake ta wuce kan number Badar dataga ta mata magana da ita suke hira daman baccin ya kwasheta.
"Al'amin yace inya kiraki wayar bata shiga, a WhatsApp kuma baki buɗe chat ɗinsa me yasa?"
"Blocking ɗinsa nayi" ta bawa Badar ɗin amsa ganin tana online. Tana turawa kuwa ta buɗe ta shiga yi mata voice.
"Kina kuwa yanda ya gigice Afee zuwansa fa gidan nan biyu yau wlh se in kira masa ke a wayata na kira kuma bata shigo ba lokacin wai me ya haɗaku ne? Dan Allah ki tausayawa guy ɗin nan wlh Al'amin yana sonki sosai fa" cewar Badar.
"Uhm duk ya gama haukansa can ya nemi daidai shi a gaba, wai ni Badar shikenan Namiji baze so ni saboda Allah ba se dan wata buƙata ta daban? Ki faɗamun tsakaninki da Allah ko da akwai wani abu da nakeyi mara kyau da yake Attracting yan iskan Maza zuwa gareni? Ni kenan duk wanda zece yana sona seya nemeni da lakata me nakeyi daya sa suke mun kallon Mara kamun kai Badar?" Fatiman ta mayar mata da Voice note muryarta na rawa kamar zata fashe da kuka saboda zafin abinda take ji a ranta.
Allah ya mata farin jini bana wasa ba, bata taɓa fita ta dawo gida Namiji be tsaidata ko an biyota gida ba amma duk wanda ta kula take ganin kamar zasu samu daidaito da tafiya ta fara nisa se ya kauce layi ya shigo mata da wani zancen na daban. Tun abin baya damunta har yazo ya fara bata tsoro ta yaya za'ayi ace duk wanda yazo yana sonta seya nemi ya taɓa jikinta se kace ita kaɗaice Mace a duniya ko kuwa duk suma sauran Matan haka ake musu??
"Na gaya miki Afee wannan matsalar fa bake kaɗai ta shafa ba, abinda yasa kuke mun kallon Masifaffiya kenan na kasa tsaida saurayi ko ɗaya saboda ni bana iya shiru, mutum na zuwar mun da shirme a take nake tsigaleshi gara nayita zama single dina har Allah ya kawomun Mijin Aure na na gaske, ke kuma duk wanda yazo miki da suffar Salihai seki saki jiki se mutum ya nuna miki true color kizo kina ciwon rai kenan shima Al'amin ɗin shegene da gemunsa kamar Na Allah ai da kin gayamun da wuri wlh da daya zo ɗazun sena wulaƙantashi dan iska shege me ci da buguzun da fuskar Salihai" Badar ta hau spark daga nan suka cigaba da tattauna abinda yake damunsu ya kuma zama ruwan dare a zamanin nan. Samari sun zama abinda suka zama kawai, sun maida mata tamkar wasu Takalma da zasu ce se sun gwada sun samu wanda yayi musu daidai kafin su siya a irin haka waɗansu da ƙadda take hawa da wanda suke kasa jure jarabawar ubangiji yayi musu suga kamar idan Saurayin ya gudu ba zasu samu wani ba se su bayar da kai bori ua hau wanda daman samarin yan latsine da sun samu abinda ya kawosu su fece shikenan se a shiga lahaula da Innalillahi Allah ya rufa asiri.