← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 137

Sashe 64

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daren ranar bacci barawo ne ya saceta dakyar aiko tayishi da mafarkin wai Audu ya mutu an kwashe komai an bawa Yayan Bara'atu da Zubaida ita bata samu ba. Da safe kuwa dakyar ta iya zama jiran Jamila da ace tasan gidanta ma da ba zata iya zaman jira ba gara taje su wuce daga can. Wadanda suka dawo washegari son zuciya ganin yanayinta yasa suka watse dan a dare dayan ciwon qyashi da Hassadar data dorawa kanta ya zabgeta kai ka dauka kwana tayi tana gudawa.

Jamila bata zoba se bayan La'asar dalili kuwa Hashimu na gida ranar bayan ya gama Tijarata akan Zabonsa data dauka tayiwa Binta Miyar da ko dandanata batayi ba da safe da Sauda ta kai mata kayan Karin Kumallo tace ta dauke tuwon a bawa Yara. Seda ya fita kafin ta samu ta kammala duk abinda zatayi gudun kar sukai Magriba kafin ta fito. Tinqis tinqis se gasu a sabon gidansu Bara'atu Jamila nata zuba mata dan banzan Surutu ita ko Ruhinta da gangar jikinta suna ga su isa taga gidan da Audu ya ginawa Bara'atu.

Tun daga qofar gidan yanda aka lailayeta da fulasta tasha fenti yanayin tsari da taswirar ginin kai ba zakace a cikin Bechi yake ba. Wani abu me daci da maiqo ya taso mata har seda ta dafe qirji tana kallon qofar gidan dake garqame da kwado alamar basa nan. Jamila ta qarasa tana shafa qofar ta juyo ta kalli Binta da taje tunga tace

"Kinga basa nan, ko ina suka tafi se Allah amma babu komai gobe ma ranace se mu dawo" tana rufe baki sega Qanin Bara'atu ya shawo kwana ta washe baki tace
"To qila ma gasu nan kinga qaninta".

Ya qara gurin ya gaishesu a mutunce Jamila tace
"Ina mutanen gidan mun tarar qofa a rufe? Ka ganta can ka ganeta ko Matar Alhaji Audu ce tazo muku Allah sanya Alheri".

"Ai kuwa kunyi sabani dan basu koyi Minti Ashirin da fita ba sun tafi Rano" ya bata amsa. Ta dafe qirji tace
"Rano? Kai sun luluqa da nisa, to kuma yaushe zasu dawo?"

"Gaskiya ban sani ba" ya bata amsa cikin qaguwa da maganarta ya fara tafiya ta tareshi tana cewa

"Aida ka bude mana to taga gidan tunda kaga ita ba mazauniyar nan bace balle ace ta sake dawowa idan sun dawo, qaraso Hajiya ya bude mana mu Shiga" ta fada tana kallon sashen da Binta ke tsaye sedai wayan bataga kowa a gurin ba. Ta hau waige waige qanin Bara'atu me suna Isah yace

"Indai wannan Hajiar ce ai ta dade da tafiya tun sanda nace miki basa nan" daga haka shima ya wuce ya barta tsaye tana cizon yatsa. Bawai da zuciya daya ta sanarwa da Binta wannan maganar ba so tayi ta hada bala'i ta kuma so ace sun tarar da su Bara'atun dan ta tabbatar da Binta bazatayi haquri ba se tayi musu tijara da rashin mutunchi iyakar qarfinta.

Cike take da qyashi da hassadar ya za'ayi ace dukda Bara'atu bata tare da Audu kuma taci gaba da kere masu ta kowanne fanni na rayuwa? Shekaru Aru Aru suna zaune gidan qasa lokaci daya Audu yazo ya tadawa Bara'atu da Iyayenta ginin Jan bulo ya danqara musu gida kamar na wani sarki Alhalin su suna fama da jar laka? Shiyasa ta kwazawa Binta maganar tunda ta lura bata sani ba yanzun ko tasan inta koma Birni wacce za'ayi se Allah ita dai fatanta Audun ya kwace gidan kawai tunda dai yana tsoron Binta.

Farar safiya Binta ta kammale kayanta tsaf tasa a nemo mata shatar mota zata tafi gida. Goggo Fadi ta ringa tambayarta abinda ya faru data tashi tafiya gagaga haka Alhalin sati guda tace zatayi bata da abin fada mata a matsayin dalilin tafiyarta dan haka kawai ta laqawa Danta ciwo tace shine bashida lafiya gara su tafi ta kaishi Asibiti. A wata mota da Jaki ya fita dadin hawa da saurin tafiya ta kamo hanyar Kano, ita ma din da dakyar aka samo mata ita dan masu motocin daukar kaya tuni kowa ya fita ai kuwa taji jiki kafin taje gida, baya da qafafunta sun fada dan jinjirinta kansa ya gane kurensa a wannan tafiya seda sukayi jinyar gaske ita dashi ga qarin baqin ciki ta tarar Audu baya gari seda taje gidan Turai a kwana na uku bayan taji dama dama sannan ta gaya mata ai sun tafi Legas tareda Ali zasu dakko kayansu.

"Karki tareshi da hayaniya kibishi ta siyasa idan kika gano bakin zaren sannan musan abinyi" Turai ta fada mata bayan data shaida mata zancen gidan da Audu ya ginawa su Bara'atu. Haka kuwa akayi, tayi matuqar qoqarin boye tashin hankalinta da damuwa akan Al'amarin harya dawo daga tafiya seda ya kwana biyu ya ware gajiya kafin ta tada masa da zancen ai taga gida akace shiya ginawa su Bara'atu.

"Badan Bara'atu na gina musu gida ba nayine saboda Yarana, ya za'ayi ace da raina ban mutu ba a watsarwa da Yayana da uwarsu kayansu a waje bayan ina da halin da zan iya siye garin gaba daya ma ba iyakar gidan da suke ciki ba (kuji fariya). Shiyasa na yanke shawarar yi musu gini na Alfarma irin wanda babu shi a kaf garin da makwafta" ya bata amsa. Binta tayi murmushi a qoqarinta na boye tashin hankalinta tace

"Gaskiya hakane amma dai basu kyauta ba suma se kace ba yan uwa ba? Kuma naji ma kamar nace fin qarfi kawai suka gwada musu amma tun Baban nasu yana da rai ya fitar da kowa ya bashi kason kudinsa?"

"Oho musu wannan su ta shafa tunda na rigada nayi abinda nayi, gidan ma kuma zan siyeshi na mayarwa dasu Bara'atun se naga ta tsiyarsu ko?" Ya bata amsa, ta zabura se kuma tayi saurin daidaita zama tace

"Aiko dai, ka barwa su Bara'atu ko ka barwa su Babangida?"

"Ita dasu ai duk dayane kuma duk abinda zanyi mata Alfarmarsu take ci ko iya ruqonsu da takeyi ai tayi qoqari Alhalin ubansu nada rai kuma ina da yanda zanyi"

"Uhm hakane, ni da zakayi haquri ma ka yafe abinda ya wuce daka maido su munci gaba da zamanmu kawai hankali kwance. Duk se naji rashin dadi saboda mutane zasuyi ta kallona a matsayin wadda tayi silar raba Yaya da Mahaifinsu" Bintan ta zartar da hukuncin da take ganin shi kadai ne ze datse alaqar Audu da Bara'atu, tunda dai yace saboda yara yake mata komai to gara a kwaso mata yaran suzo suyi ta dabdala a tsakar gida da dai uwarsu tacigaba da morar Audun.

Wani kallo ya watsa mata me ma'anoni da yawa fuskarsa ta nuna mamaki qarara yace
"Dagaske kike ko wasa? Kina nufin kin yafe mata abinda tayi miki su dawo muci gaba da zama tare?"

Seta rausayar da kai ita ala dole gata Allah tace
"Abinda ya faru ai ya rigada ya faru na dauki qaddara tunda Allah ya qadarta Yaron bame doguwar rayuwa ko bata silarta ba ze mutu, kuma yara ai basu suka mun laifi ba itan ma kuma na yafe mata Albarkacinsu"

"Amma naji dadin wannan magana matuqa in sha Allahu nan bada dadewa ba kuma zan shirya dawowarsu, harkin wankemun baqin cikin abinda ya faru kuma kin qara daraja a zuciyata saboda ba kowa za'ayiwa babban laifi irin wannan ba ya yafe harya cigaba da zama da mutum" Audu ya fada cikin madaukakin farincikin da shi kansa besan dalilinsa ba.

Ta maka masa harara a fakaice kafin tace
"A kullum burina kenan na faranta maka rai, inda na san wannan ze saka naga farin cikinka haka da tuntuni an aiwatar dashi amma yanzun ma lokaci be qure ba".

Daga haka suka tashi daga maganar da kowannensu da kalar manufarsa akan abinda yake fadi.
Binta tana maganane akan Babangida da Babannan, su take nufin Audu ya dakko su dawo gidan saboda kar Bara'atu taci gaba da cin arziqinsa ta dalilinsu yayinda shi kuma tasa kwakwalwar ta fassara masa Maganar ta a matsayin ya maido da Bara'atu taci gaba da zama da Yayanta a gidan wannan ne ya sanyashi farin cikin da beyi tsammani ba. Allah ya sani bazeyi qarya ba ba kuma ze iya boye tarin qaunar da yakeyiwa Bara'atun ba saboda ita ya fara so har kawo yau kuma be dena sonta ba Halayen dara tsiro dasu daga baya ne sukayi tasiro gurin ruguza zamansu wanda yake fatan a yanzu ta hankalta ta gane kuskurenta.

Abu na biyu daya qara masa jin dadi shine ya san maida Auransa da Bara'atu ze gyara alaqarsu da Yan uwansa data gurgunce musamman Yakubu da Bilki, wannan farin cikin kadai ya hanashi bacci ranar, washe gari kuwa yayiwa Bechi tsinke sedai ya tarar da su Bara'atun har sannan basu komo ba.
Izza da girkan kan dai yana nan, ya saka a ransa Mace tayi kadan daya je bikonta, Hayatu Abokinsa ya barwa sallahu akan idan Sun Dawo yaje ya tuntubeta yaji ra'ayinta akan komawa gidansa.

"Kai yanzu Audu kana nufin kafi qarfin ka tare ta baki da baki kuyi maganar nan?" Hayatun ya tambayeshi cikin mamaki.

"Ga Amsar nan ka bawa kanka ai, ko yanzun saboda Yayana zan mayar da ita bawai dan ta cancanci na maida itan ba" ya bashi amsar da har ransa yasan qarya ya fada.

"Ai shi kenan, girman kai dai rawanin tsiya, kuma shi ya halakar da mafiya yawan Magabata" Hayatu ya bashi amsa.

https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 25*
Chapter 64 · 0% Book details