Sashe 15
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka ya fara shirin tafiyar jiki a salube danma Balaraba ta dage da qarfafa masa guiwa tana gaya masa duk saboda ita da abinda zata haifa zeyi wata rana kuma komai ze zama labari a sannu idan yaje garin ma ya gane kan komai zasu iya tafiya tare dan ita akwai Yayanta da yake kai Shanu can Kudun saboda yawan zuwan da yakeyi ya kai matarsa daya can take zaune wannan yasa hankalinsa ya dan kwanta amma idan ya tuna ze tafi ya barta da ciki qila har se abinda zata haifa ya fara zama ko rarrafe ze zo ya ganshi duk se yaji abin ya qara fita a kansa. Haka ya shirya, duk wani abu da ze iya nema na dangin abincin da ba lallai ya samu can ba Dada da Balaraba sun hada masa. Harda dambun nama Dada tayi masa, gasu Yaji, quli quli harda Alkaki Audu ya ringa dariya wai kamar me tafiya qasar waje. Randa zasu tafi Kano Balaraba ta kasa daurewa ta ringa kuka duk ta qara sanyaya masa jiki dakyar ya iya tafiya Goggo Fadi da yan fadarta suka ringa yadawa Dada magana wai ta watsa yara sun tafi Bariki ga Yaran mutane sun auro sun ajiye wannan ai ba daidai bane iya dai bata kulasu ba suka gama jajanta tafiyar su Audun kafin kowa ya dauki dangana sukaci gaba da rayuwa yanda suka saba.
Audu kuwa seda ya raka Yakubu har Ikko, tafiya ce kamar ta yada shege musamman su da basu taba zuwa ba a hakan ma wai dan mota me kyau suka hau basu bi motar Arha wadda ake loda mutane ba. Satinsa daya ya juyo bayan Yakubu ya samu gurin zama ya gama duk wasu abubuwa har ya fara shiga aji. A dan tsukin Seda Audu ya leqa kasuwa ya gano sabgogin arziqi aiko ya qyarawa Yakubu da zarar ya gama gane kan gari ya shiga kasuwar Hayatu ze taimaka masa ya dubo musu abubuwan da ake buqata a Arewa da suke sauqi acan.
Ya dawo Kano cike da kewar Dan uwansa ya kuma cigaba da kasuwancinsa ka'in da na'in, sabanin da da yake share watanni yanzu wata biyu yakeyi yaje Bechi wani lokacin ma wata daya da kadan zeje ya kwana uku ko hudu ya juyo haka ze musu siyayya kuma ya hada harda yan uwansa dukda barakar da suka samu be fasa yi musu ba suma kuma babu kunya basu qi karba ba. Balaraba nata rainon cikinta daya fito sosai yana wata na bakwai sannan. Ba yanda Audu beyi akan suje Kumbotso Asibiti ba tunda su nan babu amma Dada taqi a cewarta Ahalinsu kaf babu wadda ta taba zuwa wani Asibiti kuma lafiya lau suke rainon ciki su haihu duk wani taimako kuma daya kamata tana bawa Balaraban shima zaman Birni yasa har yake wani zancen Asibiti banda haka a garin kaf wayaga tana zuwa wani Asibiti banda Matar Shafi'i Hedimastan primary su Baballiya da aka bude.
Har fushi yayi amma Dada taqi saurararsa, ya samu Balaraban akan ta shirya a sace ze kaita dan shi fa ya daukarwa Yakubu Alqawarin kula masa da iyalinsa ba kuma yason kowanne tsautsayi ya gifta wani abu ya same su ma se Balaraba tayi dariya tace
"Bana jin komai Yaya Audu lafiyata qalau kamar yanda Dada ta fada in sha Allahu zan haihu lafiya base munje Asibiti ba daga can Rugar mu ma Innata tana yomun aiken saiwoyi babu wata damuwa da yardar Allah".
Badan yaso ba ya barta, watan Haihuwar Balaraba na tsayawa ya dawo Bechi yanda kasan shi za'ayiwa Haihuwar, kwanan sa biyu da dawowa Balaraba ta fara Naquda cikin dare har garin Allah ya waye bata haihu ba duk irin taimakon da Dada da Goggo Fadi tareda Unguwar zoman da suka kirawo suka baya amma abu ya gagara, haka ta sake wuni sur cikin ciwo kuma abin takaici sun hana akaita Asibiti acewarsu dama haihuwar fari akan dade, hankalin Audu ya tashi ganin har duhun Magriba ya fara kawo kai amma Balarana shiru zuwa sannan kuwa ko baa fada ba ka kalleta kasan qarfinta ya fara qarewa. Beyi shawara da kowa ba ya fita neman motar da zata kaisu Kumbotso, duk masu motocin daukar kaya na garin abin takaici kamar hadin baki duk gurin wanda yaje ae yace masa bashi da Mai yau ko aiki be fota ba.
Har gurin Alhaji Magaji yaje wanda a lokacin shi kadai yake da motar hawa a garin amma be samu alfarmar ya taimaka masa su kai Balaraban Asibiti ba ga duhu yayi dan tuni anyi magriba Isha ake shirin yi. Zuciyarsa ta quntata ya rasa abinda zeyi, be taba jin burin mallakar abin hawa na irin na wannan dare. Hankalinsa be qara tashi ba seda Bara'atu ta fito tana kuka hankali a mugun tashe take sanar masa Jikin Balaraban ya qara rikicewa har ta fara zubda jini gasu Dada can duk sun rude suna salati. Suna tsaye nan cikin rashin mafita kamar daga sama sega Kasim, Abokinsa ne amma irin wanda alaqar bata da qarfi sosai. Audu ya sauke ajiyar zuciya yana yiwa ubangiji godiya daya kawo masa Kasim din. Alfarmar Baburinsa ya nema ya bashi haka aka cocciba Balaraba da sam bata cikin hayyacinta Dada ta hau bayanta suka sakata a tsakiya suka tafi Kumbotso aiko wannan abu ya qara hura wutar gori Goggo Fadi ta ringa masifa tana fadar maganganu cewar Dada batayi kara ba. Ita kuwa Dadan tsabar rudu da tashin hankali yasa sam bata san sanda ta haye mashin dinba dan gani takeyi idan wani abu ya samu Balaraba itace sila tunda babu yanda Audu beyi suje Asibiti ba tun gari nada haske.
Assalamualaikum, My name is Maryam hassan, I sell Laces range from 35k to 250k beautiful n classic designs, kids clothes , materials, shadda gezner men materials range from 30k to 120k , women veils , 8k,12k,15k,25k,all available muna bada sari muna maraba da masu siyan daya, muna hada na lefe da kayan barka , location Kano, FREE DELIVERY NATION WIDE🌹KWARAI KUWA DILIBIRI KYAUTA FA just buy what u want n we deliver safely in Sha Allah,,,,,,,, 07088361522
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR*
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*HALIN KISHI*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*NAGODE*
*FREE PAGE 7*
Cikin hukuncin Allah isarsu Asibitin babu jimawa Balaraba ta sauka sedai yar tazo babu rai wanda ko ba'a fada musu ba sun san wahalar data sha a ciki ce tayi Ajalinta ita kanta Balaraban babu yanda take hankulansu basu dan kwanta ba seda Likita ya tabbatar musu da Balaraba zata samu lafiya da yardar Allah. A nan cikin Asibitin suka kwana, da sassafe Audu ya tafi Bechi tareda gawar yarinyar can aka shiryata akayi jana'iza kafin Bilki ta hada duk abinda Balaraba zata iya buqata suka juya Kumbotso tareda Bara'atu da Mariya matar Aminu se Maimuna Amaryar Hashimu da itama tana hulda dasu Balaraban dukda mijinta baya so. Goggo Fadi data kwafe tun jiya cewa tayi ba zataje ba dan haka sula tafi. Seda Balaraba ta kwana uku Asibiti kafin aka sallamota dan ba qaramin jiki taji ba. Ta rame fiyau se haske data qara kamar mara jini duk wanda ya ganta seya tausaya mata ga rashin jaririyarta ga Yakubu baya kusa yana can nisan duniya bema san abinda ya wakana ba. Haka sukayi ta tausarta harta saki zuciyarta, kwananta Ashirin da haihuwa Dada tayi mata izinin tafiya can Rugarsu dukda yan uwanta sunzo sun dubata har sun bar mata yayarta daya ita ke kula da ita amma Dadan tace taje ta huta kota qara rage kewa a sannan tuni Audu ya koma Kano ya kuma aikawa da Yakubu wasiqa ya sanar masa da abinda ya faru.
Haka aka cigaba da lallaba rayuwa, Su Yakubu sun samu hutun shekarar farko a karatunsu ya taho gida cike da kewar matarsa da kuma Alhinin yarsa daya rasa. Tsaraba niqi niqi yayo daga ikko, kowa seda yasan da dawowarsa domin dangi kaf kowanne gida seda abin Alkhairinsa ya leqa. Yaya Baba da kansa yake cewa
"Tabbas yaran nan sun san Alkhairi, ka dubi duk abinda mukeyi musu amma basu riqe mu ba ba kuma su canza daga kyautatawar da sukeyi mana ba"
Hashimu da yayi maganar a gabansa yayi tsaki zuciyarsa tayi baqi, haka siddan shedan yake hura tsanar su Audu a zuciyarsa yana qissima masa cewar duk abinda suke samu shida yan uwansa ya kamata ace sun same shi amam basu Audun ba.
Shidin mutum ne me shige shigen zuwa gurin Malamai, a yawonsa aka binciko masa cewar Yayan Dadan suna da taurarin arziqi, yabi malamai sun fi nawa amma kamar hadin baki duk inda yaje se a ce masa su dun zasu daukaka irin daukakar da beyi zato ba, da yake yayi ammana da zancen Malaman nasa shikenan qyashi da hassada ya darsu a ransa ya kuma dage ta duk wata hanya dayake tunanin daukakar zata zo musu yake qoqarin tosheta sedai rashin sani irin nasa fadar Malaman tsibbunsa ba gaskiya bace, idan kuma anyi katari sun canki daidai to wayo ko dabararsa basu isa su canza abinda ubangiji ya qaddara faruwar iya wuya se abinda ubangiji ya qaddara ya faru.