Sashe 2
Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read
godiyar ubangiji shima adduarh dayace Allah yasa macece me albarka kuma Allah yasa tayi kma da KYAUTAR ALLAH. Annah tasa anyi sadaka da dukiya ta fitar hankali duk dan saboda samun cikin KYAUTAR ALLAH ji takeyi kmr rnr ne zata fara samun jika. Family kam wasu na murna wasu na bakin ciki wasukam adduarh sukeyi Allah yasa a haifa namiji suga ta tsiyar Annah, kou ince suga iyakarta. A bangaren KYAUTAR ALLAH Kam tinda tasamu cikinnan shikenan tayi bye bye da lafia, kou ruwa tasha seya dawo duniya babuci babusha wani irin laulayine Allah ya jarabceta dashi me mugun azaba, ji takeyi kmr ta cireshi ta huta, bata kara tabbatr dacewar uwa mace nada darajaba seda tasamu wannan cikin, kullum cikin kuka take, ganin hkn yasa Annah taje da knta ta daukota ta dawo da ita gidanta, toufa nanmadin kullum suna hnyar zuwa asibiti kullum hannun KYAUTAR ALLAH na daure da drib domin shine abincinta shine abinshanta don bataci batasha. A haka cikin yakai wata biyar ana tsammanin chanji amma ina kullum se cigabama whlar keyi Annah dukta sare dabadan tasarai da cikinnanba data haqura a zubar kawai domin autar ta KYAUTAR ALLAH ta huta, ji takeyi daman ana amsa ta amsar mata ta huta, domin wata rana ita da knta Annah tasa KYAUTAR ALLAH takeyi a gaba tayita kuka, gabaki daya rayuwarsu tass takoma a asibiti, KYAUTAR ALLAH dukta lalace ta kode ta canza kamanni setayi wani irin fari, kuma ita ba fara bace chocolate colour ce,irin kalarnan me shekin tsiya baka ganin komi a jikinta se karan hanci da dara daran idanuwanta, dukta koma kashi. A haka wata rna Raslan yazo hutu yaje ya ganta, yna ganinta ya fasheda kuka, dukse yaji murnarsa ta koma ciki, yazo ya rungumeta yna kuka Annah Kam ta zabga uban tagumi. KYAUTAR ALLAH tayi murmurshi ta shafa kan Mohammed Raslan din cikin sanyin muryarta tace, "My son...kaga yadda kanwarka ke wahalar dani kou..." Wani irin hawaye me zafi yashiga bin kuncin Raslan ya shafa cikinta daya dan tasa, se kuma yaji sanyi a rnsa, yace" am sowie sweet mother a gaskia kanwarnan tawa bata kyautaminba...kiyi hkri pls mother zaki samu sauki very soon..." Smiling kawai KYAUTAR ALLAH tayi ta zubawa Raslan ido tana masa wani irin kallo, shima dago kai yayi yna kallonta. Rnr daze koma ingland haka ya dawo asibitin domin yayi mata sallamah domin yna tunanin inya tafi baze dawoba har zuwa lokacin dazata haihu. Kwance yasameta,tna sanye da riga doguwa maroon domin daman duk a kala tafison maroon kowa yasani a family,. Lokacin Annah na toilet tana wanka. Ido KYAUTAR ALLAH ta zuba masa, kna tasakar masa murmurshi naso da kaunah, matsowa yayi yaja kujera ya zauna daf da gadonta, ya dora hannu a cikinta, haka kawai yakejin wani irin matsifaffen so da kaunarh yna ratsa bargon jikinsa da jijiyoyinsa yayinda zuciyarsa ke amsar sakon kaunar cikin dake jikinnata, ji yakeyi duk duniya be tabason wani halittaba kmr yadda yakeson cikin dake jikinnata. "Allah yasa ki sauka lafia mother in dawo in ga kanwata..." Ya krshe mgnr da murmurshi. Itama murmurshi tyi ta damke hannunsa cikinnata, tace "Hmmm son inajin wani abu a game da rayuwata..." Dam yaji gabanshi ya fadi, yynda jikinsa yayi sanyi, yace "kmrya mother.." Ya fara a firgice. Murmurshi tasakar masa na kwantrda hnkli tace. "Dan Allah zan baka amana zaka amsa..." Cikin hanzari yace "ki bani amana kota menene wallahi nayi alqawarin zan riqe miki kouda hkn ze zama silar rayuwatane..." "Na baka amanar abinda zan haifa walau mace kou namiji..." Be dauki komi a rnsaba yy murmurshi yace"na dauka..." Dam ta kara rike hannunta cikin nasa, ta maimaita masa amanar har sau uku yace ya amsa, kna sukayi sallamah ya tafi yna waiwayenta,hk kawai yakejin jijiyoyinsa duksun sage. Cikin *KYAUTAR ALLAH* yacika watannin haihuwarsa Seda tajera sati biyu tana labour se haihuwa tazo gadan gadan se kuma tayi shiru dif, hankalin iyalan safana dukya tashi. Ana shirin shiga dakin tiyata da ita allah yasa ta sauka ta sambalo diyarta katuwa wadda taci ta koshi bul bul da ita kamarta sak kmr uwarta harma tafi uwar tata kyau, dukkanin jikinta gashine, gashi dukya baibaye fuskarta yayindaya kwanta luf a fatar jikin jaririyar tinda nake ban taba ganin jaririya me gashiba kamar yarinyar domin tsaf za a iya kitsa sumar dake kanta, ga kyau, ga farin jini dashiga zuciya. Toufa ga murna ga bakin ciki. Yayinda iyalan safana suka samu labarin haihuwar diya macen murna fal cikinsu annah kam baki har kunne, hatta raslan da bayanan ana haihuwar aka sanar dashi lokacin yna masallaci yanata ibada a kan nakudar da aka sanar dashi KYAUTAR ALLAH tanayi. A lokaci daya yaji labarin haihuwar da rasuwar KYAUTAR ALLAH bayan haihuwar kou second daya bata karaba tace ga garinku nan. Hmmm jimami da bakin ciki baya misaltuwa, Annah kam har suma tayi dakyar aka samu kanta, raslan da bayananma seda yayi qaramin hauka. Aka yima KYAUTAR ALLAH wanka aka kaita gidanta na gaskia. Yayinda akabar zuciyoyi da kewarta da kaunarta mijintama mutuwar ta tabashi amma haquri yazama dole, tsakanin mamaci dame rai adduarh ce babbar soyayya se muce allah yajikan rai mukuma allah yasa mucika da imani. Allah sarki, duk wanda yaji mutuwar seya tausayawa jaririyar. Washe gari raslan ya iso nigeria a hargitse kai tsaye ya nufo gidan Annah nan ake zaman makoki yayinda annah ke rungume da Jaririya ta hana kowa ganinta ballan tanama a dauketa, babban danta wato harun na gefenta yna bata baki yana mata natsiha,amma ina hawaye be dena zuba daga idanuwantaba, wai a hkma dan tna ganin jaririyarne har takejin sanyi ga rayuwarta, yayin data dauki son KYAUTAR ALLAH ta dorashi cas a kan jaririyar da tini tayi mata lakabi da *KYAUTAR ALLAH* itama. Bayan anyi arba'in uban yarinya yaso amsar diyarsa yakaiwa kanwarsa tacigaba da shayar da ita, amma ina beda dmr magana dole ya haqura, ya barma Annah KYAUTAR ALLAH wadda taci sunan Rukayya wato sunan mahaifiyarta, dukda ana jimamin mutuwa amma byn arba'in da kwana hudu Annah tasa aka kawo kosassun marikan shanaye har guda hudu aka yanka a cewarta na sunan KYAUTAR ALLAH ne, a halin yanzu babu wadda Annah keso fadin duniyarnan kmr jaririyarnan *KYAUTAR ALLAH* wai ance abun cikin kwai yafi kwan dadih. Jaririyar nada hakuri, madara ake bata, yayinda tinda tadiro duniya daman tana tsotson hannu, annah tayi tayi ta rabata da tsotson hannun amma ina da an cire seta fasa ihu, inkouda hannun a bakinta kou kuka batayi, yunwama bataji, sannan sam batada rigima. Raslan kam ai nan ya tattaro ya dawo gidan Annah, da kyar yasamu annah ta fara bashi KYAUTAR ALLAH, domin annah bata yarda da kowaba a kn kyauta allah.a hnkli, ragamar rainon KYAUTAR ALLAH ya dawo hannun raslan, shike ciyarda ita ya shayar da ita yaci kashinta yasha fitsarinta, shike mata komi, har goyata yakeyi yayita jijjigarta, in KYAUTAR ALLAH batayi bacciba, tou shima raslan rnr baze rintsaba. A lokaci kankani wani irin so da kauna yashiga tsakanin raslan da jaririya KYAUTAR ALLAH, yayin dashi ke kiranta da Jaririyar, itama yarinyar tini ta ganeshi. Saboda Kyautar allah raslan ya haqura daci gaba da karatunsa a Ingland saboda bayason nesa da ita daidai da bacci bayayi se in kyautar allah tayi bacci, shima a kn cikinsa take bacci, wani abunma sede annah tazuba musu ido, domin kou ita bata tunanin son datakewa kyautar allah yakai rabin wanda raslan keyi mata, kwata kwata baya bari masu aiki su tabata har nanny aka daukar mata amma ya sallameta. Wata rana Cikin dare KYAUTAR ALLAH ta rinka kuka, raslan yayi rarrashin amma takiyin shiru Annah ma tayi rarrashin amma takiyin shiru, Raslan ya rasa ina zesa rayuwarsa kukan yarinyar na taba masa zuciya ji yakeyi kmr zuciyarsa zata tarwatse, shima kawai seya fasheda kuka me tsanani Annah ta zuba musu ido tana kallon ikon allah a nan ta kara tabbatr dacewar Raslan nason KYAUTAR ALLAH fiyeda tunaninta. Tin daga rnr inde knaso kaga hawayen raslan tou KYAUTAR ALLAH na kuka nanne shima zakaga nasa kukan. KYAUTAR ALLAH ta taso batasan kowaba se Raslan, da bakinta ya fara budewa da sunansa ya bude yayin datake kiransa da Abbah. Hartakai shekara daya batabar tsotson hannuba, amma ita nata tsotson hannun kyau yake kara mata ainun. Yayin da tana girma tana kara kyau kamanninta da mahaifiyarta nata kara bayyana a tare da ita. Hajiya Rukayyat amaryar alhaji musa wadda bata haihuwa, allah ya dora mata son KYAUTAR ALLAH,don hk duk inda taga kyale kyale seta siya, ta kaima KYAUTAR ALLAH ji takeyi, daman Annah ta bata KYAUTAR ALLAH, Amma so ba samu bane, sede da soyayyar kyautar allah a zuciyarta. Hknne yasa suke shiri ita da raslan. KYAUTAR ALLAH ma tana kaunar takwarar tata. Wannan tarewar da raslan yayi a gidan Annah abin naciwa Hajiya zainab tuwo a kwarya, musammanma data lura da jarabar son dayakewa KYAUTAR ALLAH, ita bawai tana bakin ciki bane, amma jikinta na bata wani abu i mean something bad. Duba da yadda Annah ta tsaneta, aikou ba dadinta bane ita kuma jininta yaje ya manne da jinin wadda ta tsaneta, dukdade bata da yadda zatayi ta raba hanta da jini. Kwanci tashi ba wuya, game rai da lafia. Yayinda kyautar allah takai shekara biyqr, ga kyau gata bulbul da ita sam maraici be tabataba, ragamar rayuwarta na hannun raslan, hatta kitso shi yakeyi mata, a knta ya koyi kitso, dayakema ita kyautar allah akwai gashi domin kuwa sumarta har baya, jefi jefi yake mata kitso, wata rana yakaita, gun saloon. Komi da komi shi yakeyi mata hatta pant shi yake siya mata, kuma sam batasa kayan nigeria sede na Dubai. Shaguwa daso da kaunar raslan dashi KYAUTAR ALLAH ke girma batasan komiba se raslan ita duk a tunaninta da yadda ta daukeshi shine mahaifinta. Duk bayan kwana biyu se safana family's na nesa dana kusa sunzo ganin KYAUTAR ALLAH, allah yasa sonta a zuciyoyin duk wani dan safana family. Haka mahaifintama duk byn kwana daya yna hnyar zirya domin ya dobu diyar tasa har zuwa lokacin, ya gazayin aure don gani yakeyi baze taba samun kmr marigayiyyar matarsaba. KYAUTAR ALLAH nada 7yrs mahaifiyar raslan ta matsa dole ya dawo gida ya kama tasa sana"arh dukda lokacinmashi yna business dinsa don be yadda