← Book details Kyautar Allah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 164

Sashe 122

Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read

sakeki Amma inke bakison hakan Ai shikenan kinga duk fadan da nakeyi a kanki a banza nakeyi kenan kou..." Kawai se Annah ta fashe da kuka. Kyautar Allah ta sassauta da nata kukan hankali a tashe tashiga bawa Annah Hakuri saboda tasani ko Annah bata fadaba a kanta ne takeyin komi. Annah ta sassauta da kukanta tace "kiyimin Alqawari zaki kwantarda hankalinki a kan mgnr yaronnan kinga bakida cikakkiyar lafia...banaso in kara ganin hawaye a kan fuskarki inde a kan yaronnan ne..." Cike da jin zafi KYAUTAR ALLAH tace "insha Allahu Annah na miki Alqawari..." Ta fada hkn ne saboda Annah taji dadih Amma abun na cinta inside, tanason sanin a wani hali daddynta yake ciki, ba itaba hatta Annah nason sanin a wani hali yake ciki. Ummih da hajiya saude suka iso asibitin, zuwa lokacin an samu ya farfado daga doguwar sumar da yayi, ansa masa drib se numfarfashi kawai yake saukewa, cikin bacci me nauyin dayayi awon gaba dashi. Kallo daya ummih ta masa taji zuciyarta babu dadih, gani takeyi kamar itace silar komi saboda tasashi ya aikata abinda beyi niyaba. Ihsan kuwa tana nan manne da gadon da yake, zuwa lokacin an canza musu daki. Ihsan ce zaune gefen bed din da yake kwance fuskarsa na kallon sama har wata rama yayi ta dole fuskarsa tayi fayau da ita tayi wani irin haske na ciwo. Anty rukayya and anty sadia and mmn na'im, suna zaune kan kujero dayake dakin an kayatasa da kujeru na Alfarma hatta da gadon mara lafiyarma special ne. Alhaji musa alhaji umar alhaji harun Abdullahi na'im suna masallaci kasancewar lokacin sallar la'asar ne. Duk wanda ke zaune a dakin da abinda yake saqawa da warwarewa a zuciyarsa, anty sadiya kam zuciyarta cike takeda takaicin ummih dukda abinda tayi a wani fannin ta burgeta amma a wani fannin ta bata mata rai. Hajiya saude batabar asibitin ba se after isha'i kana tabar asibitin tanata kwantarwa da ummih hankali ta wuce da niyar zata dawo gobe. Byn ummih ta rakata ta tafi, kana ta dawo dakin, idonta dana alhaji umar, ne suka sarke cikin na juna, kawai ya dauke kansa daga kallonta saboda duk haushin juna sukeji. dawowa tayi kan kujerar dake facing gadon ta zauna hadi da zubawa Raslan ido wanda har lokacin idonsa rufe yake be farkaba,se sauke ajiyar zuciya kawai yakeyi time to time, kallo daya zaka masa kasan cewar yanajin jiki, dan haryamafi KYAUTAR ALLAH jin jiki. Be farkaba se tsakiyar dare around 12:30am idanuwansa na budewa bakinsa yamotsa da sunanta. "Fineness!! Fineness!! Fineness!!!" Ya fada da karfi kamar ze fasa dakin, yayinda duk abinda ya faru ya shiga dawowa kwakwalwarsa sabo fil. Duk wanda ke zaune seda ya tashi tsaye, duk suka karaso bakin bed din suka tsaya carko carko kowa zuciya cikeda tausansa, bnda ihsan da bakin ciki ya rufeta jin yanata ambatar fineness kowa yasan wacece fineness din tasa KYAUTAR ALLAH ce. Sannu sannu suka shiga binsa dashi ihsan kam se wani shafar kafarsa takeyi tana masa sannu ita a dole game miji. Binsu da ido ya shigayi dai-dai idonsa ya sauka a kan ummih kawai ya fasheda kuka kamar karamin yaro yana fadin. "Ummih dan Allah karkice in saketa! Wallahi ban saketaba! Ina sonta!! Itace rayuwata! Dan Allah ummih ku bawa Annah haquri ta barni da matata!!" Shine abinda ke fita daga bakinsa yana kuka kamar karamin yaro. Ihsan ji tayi kamar ta kashe knta dan bakin ciki, me yafiye mata wannan ciwo a gabanta mijinta ya rinka ambatar wata har yana fadin ze mutu a kanta, bakin ciki ya hadu ya cunkushe zuciyar ihsan. Alhaji abdullahi yaje ya kira dr Ibrahim zuwa lokacin dr hannatu ma bata nan taje gida ta huta. A tare da dr Ibrahim suka shigo dakin, har lokacin se kukan yakeyi . Dubasa dr yayi ya masa allura, ya kara saita ruwan dake tafiya a hannunsa, kana ya zauna da knsa yashiga kwantarwa da raslan hnkli, saboda hawan jinin sane ya hau sosai. Dr Ibrahim yakira duk mazan office dinsa ya sanar dasu hawan jinin Raslan ne ya hau sosai inyafi hakanma ze iya haifar masa da shanyewar barin jiki, ya basu shawara kan dole se an rinka kwantar masa da hankali saboda a samu jinin nasa ya sauka.. Duk sunyi mamakin jin RASLAN nada hawan jini a karancin shekarunsa, sannan sun shiga damuwa. Dawowa dakin sukayi Alhaji musa yaja ummih gefe ya sanar da ita abinda dr ya sanar dasu, ummih harda hawaye na tashin hankali. Dole ta daura aniyar kwantarwa da danta hnkli ko dan gudun kada ta rasashi ko yayi mutuwar tsaye, dawowa tayi gadon ta jawosa jikinta ta hau basa hkri hadi da kwantar masa da hankali, amma sam yaki dena kuka cewa yayi so yakeyi yaje yaga kyautar Allah daddyM ya sanar dashi ai kyautar Allah ta samu saukima harsun tafi garin katsina, ya gaya masa hakan ne dan hankalinsa ya kwanta. Kawai yaji DaddyM ne Amma yasan bade dan jiki yayi saukiba sede ko Annah ce ta matsa a kan hakan. Kwana yayi be rintsaba ko ruwa yaki sawa a bakinsa se maganar KYAUTAR ALLAH kawai yakeyi, shi yazama abincinsa kuma abin shansa. Seda asubah byn Alwala yayi sallolin da ake binsa a zaune saboda se tangadi yakeyi jiri na kwasarsa, bayan ya idar yashiga adduarh kan Allah ya saita lamarin nan ya maida matarsa dakinta, dan bayajin ze iya rayuwa babu ita. Komawa yy ya kwanta ummih tace ya tashi yasha ko tea ne, yace Ah'ah ya koshi. Sede Ummih ta zuba masa ido kawai zuciya babu salama. Bacci ne ya kwasheshi me cikeda mafarkanta, se kiran sunanta kawai yakeyi a zahiri ga ihsan a kusa nan wani bakin cikin ya kara kunsuwa a zuciyarta. 2:pm Saif yazo asibitin da niyar ya duba kyautar ALLAH nan ya tarar da uban gayyar ne babu lafia. Yana shigowa dakin raslan ya sauke idonsa a kansa ya fara tambayarsa ko yaga kyautar Allah, kai kace zautacce ne. Sosai saif ya tausawa abokin nasa dan yaga Alamar ciwon sone ke damunsa ba gaske. Da saif akayita jinyar Raslan, har kwanaki goma suka shude aka sallamesu zuwa gida suci gaba da jinyarsa a can ana hada masa da adduarh, zuwa lokacin ya dan fara samun sauki sede sam bayaci bayasha drib ne ya zama abincinsa. A zamansu a asibitib babu wanda bezo gaidasaba hatta da anty fahima tazo kuma taje katsina. Ana sallamarsu raslan yace katsina zeje yaga KYAUTAR ALLAH, da kyar Aka lallabashi akace ya bari ya kara samun sauki kana se yaje, da kyar ya hkra. Fly sukabi zuwa garin abuja, RASLAN Alhaji umar saif ummih anty sadia, ihsan,jirginsu ya daga zuwa garin abuja. Na'im harun abdullahi suka nufa garin katsina dan dubu jikin KYAUTAR ALLAH, daman matar Alhaji harun dinma tana katsinar. Anty rukayya da alhaji musa gida suka nufa saboda su sunje garin katsinar sunga jikin na KYAUTAR ALLAH 4days ago. Jikin KYAUTAR ALLAH, yayi sauki ba lefi, kullum annah cikin kwantar mata da hnkli take, duk family babu wanda bezo gaishetaba sannan duk wanda yazo se Annah ta mayar masa da abinda ya faru hadda sakin da Raslan yayina KYAUTAR ALLAH. Fatima da mommyntama sunzo suma suna zuwa Annah ta gaya musu abinda ya faru, dukfa wanda yazo ko ba dan uwaba se Annah ta gaya musu abinda Raslan yayina kyautar Allah, itade kyautar nata ido ne. kullum da tunanin daddynta take kwana take tashi, kwanansu goma sha biyar a asibitin taji sauki sosai ta warware garas da ita, kmr ba itaba, har yan kumatu ta dan farayi saboda Annah tana matsa mata dacin Abinci. Aka sallamesu suka koma gida, babu abinda idanuwan KYAUTAR ALLAH ke mararin gani, se daddynta, kullum dashi take kwana tana tashi, suna dawowa ta fada dakinta ta rarumo picture din daddynta ta rungume a kirjinta kawai se hawaye....rnr hk ta kwana da hotonsa a kirjinta. Byn dawowarsu da kwana biyu Saif yazo ya duba jikin KYAUTAR ALLAH da kayab dubiya masu dumbin yawa, a ranar ya koma. a gidan Ummih suka sauka, nan ummih taci gaba da dubasa kullum cikin kwantar masa da hankali take, itama Anty sadia ba a barta a bayaba gun kwantar masa da hnkli, ihsan kam daman sam bata masan yadda ake mgna me dadihba ballan tana ta kwantar masa da hankali. Kullum shima da picture dinta yake kwana yana tashi a kirjinsa wata rana ya kwana yana kuka tabbas zuciyarsa na cikeda begenta da tsantsar kewarta, zumarta daya lasa sam ya gagara mantawa haka kawai in yana zaune ya tuna se yayi murmushi kawai se kuma yaji sha'awarta ta motsa a garesa, tofa ranar beda sukuni sam, yana yawan kiranta a waya Amma sam bata dagawa(wayarta na gidan Anty Rukayya)... Bayan dawowarsu da kwana biyu hajiya hadiza tazo ta duba jikin nasa. Kana suka dawo dakin ihsan suka kule can karshen gado . Ihsan ta sanarma da mahaifiarya komi dake faruwa kama daga ciwon KYAUTAR ALLAH har ya zuwa ciwon Raslan da sakin da RASLAN din yayima KYAUTAR ALLAH, nan hajiya hadiza tahau murna tana fadin asirinta yaci. Ihsan ta bita da ido tace "inafa yaci...kullumfa cikin mgnrta yake mommy kadanfa ya rage ya zama mahaukaci a kan tsinanniyar yarinyarnan, ni Wallahi nashama ya haukace ne.... A gabanafa mommy yake cewa baze iya rayuwa babu itaba..." Ta karashe mgnr tana fashewa da kuka. Nan hnklin hadiza ya tashi ta shiga bawa yar tata hkri tareda mata alqawarin zataje tasamu bokanta yasashi ya mnta da wata KYAUTAR ALLAH. Sosai taji dadih ta bawa uwar tata wuqa da nama. Rnr hajiya hadiza bata bar gidanba se after isha'i byn sunsha hira da aminiyarta ummih. Washe garin rnr da hadiza ta nufa garin zamfara dan tasamu lbrin wani boka can taje ta kai masa kukanta, ya bata wani mgni a wata yar kwalba yace ta bawa ihsan tayi amfani dashi a gabanta da zarar Raslan ya kusanceta ze manta da komi inba itaba, sannan se yadda tayi dashi, Hajiya hadiza Taji dadih ta amsa maganin ta cika bokan da kudi na fitar hnkli ya amshe jiki na rawa daman su yake nema. Nan ta kwana a hotel washe gari ta dawo garin abuja, batayi qasa a guiwaba ta kawowa ihsan maganin tace tayi amfani dashi Amshewa tayi cikin
Chapter 122 · 0% Book details