← Book details Kyautar Allah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 164

Sashe 153

Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read

din ya nufa mota da ita se godia yake mata, saboda ta bashi dadih a kan dadih. Ya turawa manager din nasu da kudin dakin da kudaden abinda sukaci, daman yanada account dinsa, kana yaja motar suka fice a hotel din. .... A kofar get din gidan ya sauketa ta dauki jakarta ta fice a motar ta nufa cikin gidan a matukar gajiye bayanta se ciwo yakeyi...tana shiga falon Ta iske Annah a zaune a kan kujera ta rafka uban tagumi. "Ina kika tsaya ne wai? Inata kiran wayarki kinki dagawa?'' Annah ta jefo mata tambayar kai dajin muryarta kasan tana cikin tsananin tashin hankali. Karasowa KYAUTAR ALLAH tayi da zata zauna gefenta, se kuma ta fasa, sbda gudun kada ta gane, Dan haka ta zauna kujerar nesa da Annah ta fara koro bayani "wayata na cikin bag ne, karatun ne na yau ya dau zafi, bake kikace in rubuta takaddar fita a secondary school ba, shine nake komarin rubutawa in fita gabaki daya, shiyasa kikaga na jima Amma ai na kiraki na gaya miki, ynzu haka fatima ce ta saukeni ita kuma ta nufa gidan su..." Annah tayi shiru tana saurarenta kana tace "to shikenam,ai kwara ki rubuta takaddar fita a makarantar ki huta, isilamiyyarnanma tinda kinyi sauka ya kamata ki tsaya hakanan ki huta, dan ALLAH..." KYAUTAR ALLAH tace "Ai mun kusan gama secondary school din isilamiyyar insha ALLAH,.." Annah tace "to ALLAH ya amince mana, cikin amincinsa ..." KYAUTAR ALLAH ta amsa da "Ameen.." Annah taci gaba da magana "to ya babyna?" KYAUTAR Allah ta rufe fuska a kunyace tace "lafia lau..." Murmushi Annah tayi, hadi da miqewa tace "masha Allah,Jeki huta bari in hado miki abinci, me kikeso kici?" KYAUTAR ALLAH tace "Dan wake da manja da yaji da kabeji ..." Annah tace "to shikenan..." Ta nufa kiching ita kuma ta miqe ta nufa bedroom din Annah, wankan tsarki ta karati, tayi alwalar sallarh magrib tana idar da sallarh ta nufa barhroom ta wanke uniform din data cire ta shanya a toilet din,... Annah ta kawo mata danwaken tacishi sosai ta kora da molt, kana tayi sallarh isha'i da shafa'i da wutiri ta kwanta domin bacci takeji.... RASLAN kam be shigo gidanba se goma na dare lokacin duk sunyi baccih, jummai ya kira a waya ta bude masa kofar falon ya shigo, ya nufa dakin Annah danya ganta yaji dakin a rufe, kwarai yaso ya ganta, hakanan ya nufa bedroom dinsa ya kwanta ya hau juye juye cike da sha'awarta kmr be citaba yau, bacci yayi awon gaba dashi ko a baccinma mafarkinta ya rinkayi Yana cinta..... Tin daga wannan ranar, kullum inde tana isilamiyya ko boko seya lallaba yace sunci juna dan itama ba baya ba gun son bura, shi kam daman wannan a rubuce take shi mayen gindi ne.... A haka rayuwa taci gaba da gudana, yama dena barin garin gabaki daya kullum yana katsina tinda yana samun abinda yakeso,... Cikinta na cika wata bakwai, aka kara scanning dan ganin menene a cikin Amma sam ba a ganeba ALLAH shi kadai ya barwa kanshi sani...Annah de kullum tasa goshinta a kasa se tayi adduarh ALLAH yasa macece.. Shide RASLAN beda zabi duk abinda ALLAH ya bashi yanaso me albarka yake nema kullum, har sallarh dare yakeyi. RASLAN ya bukaci KYAUTAR ALLAH ta rakashi suje kasashen waje dan siyayyar kayan jarirai Annah ta tubure tace ina, sede yaje shi kadai bade da KYAUTAR ALLAH ba, hakanande ya hakura ya tafi dubai din shi kadai daga can ya nufa US ya nufa indian har China seda yaje duk dan siyayyar kayan jariri dana uwar jariri. Satinshi biyu a zagayennan ya dawo da uban dumbin kayayyyaki na fitar hankali, akwatina dozing bakwai yayima jariri sena uwar jariri dozing hudu, na Annah kuma dozing biyu , duk kayayyakin dayasa babu me karamin kudi. Da Annah ta tasa kayan a gaba wuni tayi tana kallonsu bata gamaba ita da kanta seda tama RASLAN fada kan yayi almubazzzaranci da kudi, babu abinda be siyaba na bukatuwan baby dana uwar baby, ita knta KYAUTAR ALLAH dataga kayan seda ta masa magana saboda kudin da yayi barna a gun sunyi yawa, sede yace mata ai bema gamaba, ta shiga rokonshi kam ya barsu haka dan ALLAH.... Cikinta ya fito yanzu sosai, inka ganta cikin kake fara hange kafin ita, ta danyi duhu, sannan da kyarma take iya daga kafafuwanta dan haka dole ta hakura da yawan zirga zirga sabodama bata iyawa jikinta ya fara nauyi, bacci kuwa ya fara gagararta kwancia ma seda dabara take samu ta kwanta, , tinda de babu fita Raslan kuma babu cin gindi se hakuri... Cikinta na cika wata takwas anty Rukayya ta dawo garin katsina gabaki daya, itama da nata kayan arziki irin na masu kudi, komide acan-acan se san barka, da fatan Allah yasawa dukia albarka.... RASLAN kam be bar kayan hakaba seda ya karo akwatunan baby dozing biyu na uwar baby dozing daya,suma na gani na fada, Annah ta rufeshi da zagi saboda yayi barnar kudi harna fitar hayyaci... Dr zilai kam bata taba fashin zuwa mata awo ba, tace in cikin ya shiga watan haihuwarsa za a kawota asibiti saboda C.S za'ayi mata bazata iya haihuwa da kntaba... Kallo daya zakama KYAUTAR ALLAH ka gane kamminta duksun canza wasu lokutanma rasa inda zatasa rayuwarta takeyi taji dadih, kullum zuciarta na kusa kusa, ko murmushi baka gani a kn fuskarta haushin ubn kowa takeji musammanma RASLAN, KYAUTAR ALLAH de ta zama se a lallaba auren zamani.... Alhaji abudullahi alhaji harun alhaji musa alhaji umar duk a rana daya suka kawo nasu uban kayayyakin baby dana KYAUTAR ALLAH hadda na hajiya Annah, da kudade masu yawa,... Anty fahima ma ba a batta a baya ba itama akwatuna biyar tayima baby, se uwar baby akwati biyu, se Annah akwatuna uku ita kuma,... Hajiya ummih ma ba,a batta a bayaba jikojinta kawai tama akwatuna dozing biyu ta cikasu tamfas da uban kayayyaki na ban mamaki,,, dakuna biyu aka ware kawai na ajiyar kayan baby, kai kace ynzu za,a fara haihuwa a familyn. Anty sadia ma ba a batta a bayaba, sarkar dankareren gold tasema KYAUTAR ALLAH, se kayan baby akwatuna biyu. KYAUTAR ALLAH kam a halin ynzu sam abubuwan dunia ma sun dena burgeta duk tabi ta sukurkuce ta koma kmr mahaukacia ko wanka ma sede Annah tayi mata, ko anty rukayya... Annah tashiga amsowa KYAUTAR ALLAH rubutu tanasha tin cikin na watanni shida har zuwa ynzu da yakeda watanni takwas.... RASLAN ya koma garin abuja, ya samu kadade masu yawa ya narkawa ihsan ta account dinta saboda yana cikin tsananin farin ciki, kullum zaka gansa da baki a bude, ganin kudaden ya girgizata saboda be taba mata KYAUTAR Irin wannanba, da daddare tayi wanka ta shirya cikin sexy dressing dinta,ta shigo falonshi se faman zuba kamshi takeyi, ya daga ido ya kalleta, taci bleaching hadda na Allah ya isa, hatta da jijiyoyin dake yawo a fuskarta ana gani saboda akwai yalwar haske a falon , kallo daya biyu ya mata ya dauke kanshi.... Ta karaso ta zauna daram a kan cinyarsa ta manna masa kiss a kumatunsa ta fara mgna cikin muryarta ta kissa "Alhajin ALLAH naga kudade masu yawa, kode kayi makuwar kaine..." Ido ya zuba mata, itade har gobe bazatayi tarbia ba inda sukayi sabani da KYAUTAR ALLAH kenan komi yayi mata se tayi godia, ita kuwa a memakon tayi godiar shine take tambayarsa ko yayi makuwa ne. "Dayake kinsan shaye shaye na fara...." Ya fada a hasale, ta tabe baki tace "Uhm abun be kai nanba...nasha ma aure zaka kara ai..har gabana ya fadi.." Raslan ya zuba mata ido yadda katon bakinta keta talewa tana magana, ko controlling bakin bata iyayi saboda dabbanci, "kamar ya?" Ya fadi idonshi na kanta. "Yeah nasha kudin fadar kishia ne ka turomin Ai..." Ta fada itama idonta na kanshi. Murmushin gefen baki yayi kana yace "Kudin fadar kishiya kuma? Ha? Ta ina zan kara aure? Ku biyu ai kun isheni,..." Gabanta ya yanke ya fadi jin ya ambaci ku biyu ai kun isheni, fuskarta dauke da rashin fahimta tace "Mu biyu kuma kamar ya?" Ta tambaya a matukar razane . "Af! Ku biyu mana da kyautar Allah...kudin dana tura miki kema kiyi hidimar suna matata ta kusan haihuwa insha Allahu..." Ya fadi hkn kansa tsaye. Kunnenta suka dauke daji na wasu yan dakiku jin abinda ke fita daga bakinta, idanuwanta suka fara neman dena gani. "Me kake fadi pls? Dan Allah me kunne na ke jiyemin? Cikin shege kama KYAUTAR ALLAH?" Ta fada a matukar gigice hadi da kid'imewa... "Cikin sunnah! Karki kara shegantamin ciki..." Ya fada a hasale zucia fal haushin tana neman sheganta masa cikinsa dayafi kauna fiye da kowa a halin yanzu. Miqewa tayi tsaye a haukace kai kace ta zarene ta shiga girgiza kai tana fadin "karya ne wallahi! Inde inada rai baka isaba ka haihu da wata diya maceba inba niba..." Ta fashe da kuka ganin gaskia a kan fuskarsa, tabbas ba wasa yake mataba da gaskia ne duk maganganun dasuka fito daga bakinshi. Zubewa tayi kasa sumammiya saboda tsananin tashin hankalin dake tattare da ita na dumbin kishin mijinta,,, a matukar razane ya kwasheta sumammiya ya fice da ita a Falon, ya kwalowa yusuf kira a guje ya karaso ya fito da motar ya shiga da ita gidan baya ya daura knta a kn cinyarsa yusuf yaja motar suka fice a gidan ko numfashi batayi. Direct asibitin dasuka saba zuwa sukaje, aka amsheta aka shiga bata taimakon gaggawa. Yasa yusuf yaje ya sanar da ummih a lokacin 9:pm ne. Yusuf na zuwa ya sanar da ita tare suka dawo asibitin da ita, hnklinta a tashe, ta shiga tambayar RASLAN meya faru, be boye mata komiba ya sanar da ita,abinda ya gaya mata daya sata doguwar suma gashi ynzu likitoci nata fama da ita,... Ummih ta rufeshi da matsifa kan meyasa ze gaya mata mgnr datayi silar suman nata, ta fara shiga ta inda take shiga bata nan take fita ba , RASLAN de hkri ya shiga bata... Ihsan kam bata farka ba se washe gari 6:am ummih da RASLAN na zaune gefenta, tana sauke idonta a kan ummih abubuwan dasuka faru suka shiga dawo mata cikin kwakwalwar kanta, kawai ta fashe
Chapter 153 · 0% Book details