Sashe 154
Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read
da matsanancin kuka... Ummih ta shiga aikin rarrashinta amma ta tubure tana fadin ummih taci amanarta ita da RASLAN, RASLAN ya daka mata tsawa jin tana neman raina masa uwa, ummih ta dakatar dashi, dole yayi shiru karshema ya tashi ya fice a dakin saboda baze daukaba a gabanshi ana raina masa uwa, sosai yaji ihsan ta fitar masa a rai gabaki daya. Motarshi ya nufa yusuf yaja suka fice a gidan. Yna zuwa gida yayi wanka ya shirya shirin zuwa katsina yusuf da ya bude masa mazaunin baya ya shiga, suma suka shiga nasu maxaunin yusuf da imran, imran yaja motar suka fice a gidan ma'aikatan gidan nata jero musu adduarh Allah ya tsare hanya. 3:pm suka isa gidan,imran na packing motar ya fito ba tare daya jira sun bude masaba, ma'aikatan gidan nata koro masa gaisuwa ya amsa a gaggauce saboda ya kosa ya ganta kwananshi biyu a abuja amma duk hnklinshi na kanta. Direct falon Annah ya nufo bakinshi dauke da sallahma... zaune take kan kujerar 3sttr Ta daura kafafuwanta a kan pillow a kasa Ta jingina bayanta da pillows Manya guda boyu Annah ta jera matasu a bayan nata, batajin dadin komi, yadda taga dare haka take ganin rana wasu lokutan kwancia ba dadih, zama babu dadih komi na dunia be mata dadih, duk tabi tayi wani him da ita ta narka uwar kiba, kibar ciki. Annah na zaune a kan kujerar dake gefenta, Anty Rukayya kuma tana zaune a kn carper din tsakiyar falon se mammatsa mata kafafuwanta dake kan pillow takeyi.. Kallo daya ya mata yaji tausanta ya gigitashi sanye take da yar riga shararah rigar iya cinyarta ta rufe, nanma rigar da kyar tasata da sanye take da dan zani shima taji ya isheta shine Anty Rukayya tasa mata wannan rigar, ta kurewa a.c falon gudu. Yana shigowa falon duk suka zubo masa ido bnda KYAUTAR ALLAH, dan ita a halin ynzu ko son ganinsama batayi, tanajin muryarsa ta kara lafewa ta kauda fuskarta gefe guda. Karasowa yayi ya zauna kusa da ita. Anty Rukayya da Annah nata masa sannu da zuwa, ya amsa hnklinsa na kan KYAUTAR ALLAH ya shiga jero mata sannu kin amsawa tayi, sam be damuba dan yasan halin datake ciki. Ya sauka kasa yace anty Rukaya ta barshi, shi yaci gaba da matsa mata kafafuwan nata, daman aikinshine dande bayanan ne Aikin ya dawo hannun Anty Rukayya. "Nan da 2 week dr zilai tace muje asibiti za ayi CS a ciro baby..." Cewar anty Rukayya. RASLAN dake zaune yanata mammatsa mata kafafuwan dakatawa yayi yace "Tou,tin tini nayi wani tunani koude muje indian ne a mata CS Din a can? Ina tsoro..." Annah ta zuba masa ido kana tace "Tsoron ne? A nan din ba Allah bane me yi, shi yakeyi a sanda yaso, nima nasama kaina tsoron Amma yanzu na cire, na yadda Allah ne ze mana da kyau..." Anty rukayya tace "Kwarai kuwa, Allah de ya rabasu lafia..." Duk suka amsa da ameen, KYAUTAR ALLAH de se binsu takeyi da ido, itama gani takeyi kmr mutuwa zatayi kmr yadda mahaifiyarta ta mutu gun haihuwarta, iyakar wahala ta wahala da cikinnan ainun. Da kyar Ummih ta shawo kan ihsan ta tsagaita da kukan datakeyi amma fa bata bar hawaye ba, se wadansu maganganu takeyi cikin fitar hayyaci....ummih ta sanar da hajiya hadiza ihsan na asibiti a haukace hajiya hadizan tazo asibitin Ihsan na ganinta ta narke ta kara fasa ihu, ta shiga zayyana mata abinda yayi silarta zuwa asibitin, itama hajiya hadizar ta kurma ihu ta shiga gaggayawa ummih maganganu wai hadda ita aka munafuncesu, ummih de se basu hakuri takeyi ta rasama ina zatasa rayuwarta.... Kwanansu ihsan biyu a asibitin aka sallameta ta koma gidanta ita da uwarta suka shiga kulle kulle, musammanma da RASLAN be kara zuwa dubataba har aka sallameta karshema da ummih ta kirashi ce mata yayi shi bayama garin yana gun iyalinshi me cikin haihuwa... Ummih kam tasha maganganu kafin a sallahmesun. Ihsan ta kira qawarta ta gugar jigida wato maryam ta sanar da ita abinda ke gudana, a gigice maryam tazo gidan, taga ihsan duk tabi ta rame, nan suma suka shiga nasu kulle kullen malamai da bokaye. A ranar sukaje gun wani boka a nan garin abuja sukace sunaso ne a zubar da cikin KYAUTAR ALLAH bokan yayi yan dube dubensa da kiraye kirayen iskokansa kana ya kyalkyale da daria yace su tafi an gama, suka cikashi da kudade masu yawa kana suka dawo gida kowannensu zucia fal farin ciki nanma a gidan cigaba sukayi da kulle kulle. Tin ana gobe ranar daza ayi mata CS din suka nufa asibiti can suka kwana washe gari 7:am akasa mata rigar operation, ji tayi jikinta duk yayi sanyi, dangi da yan uwa duk sun hallara ciki hadda mahaifinta da anty Fahima, se adduarh suke binta dashi wannan ya rungumeta wannan yazo yayi kissing dinta, RASLAN kam se rungumarta yakeyi yanasa mata albarka kawai ta fashe da kuka, da kyar aka samu aka rarrasheta tayi shiru duk tayima yan uwanta bankwana ta roki RASLAN gafara yace bata masa komiba inma ta masa ya yafe mata, kawai ya tsinci knsa da yin hawaye a boye kuma ya goge a boyen . da knshi ya tura kujerar datake zaune har dakin operation din, ya dauketa ya daurata a gadon operation ya mata addu'ur'i hadi da fatan alheri ya juya ze fice a dakin ta rigo masa hannu ya juyo ya zuba mata ido, ta sakar masa murmushi tace "Ina sonka daddy...ko zamu kara rayuwa oho?" Tayi maganar hawaye na zirya daga kwayar idonta Kwallar dayaketa boyewa suka gaza boyuwa suka hau zirya a kn kuncinsa. "Insha Allahu zamu cigaba da rayuwa...yara goma xaki haifamin Insha Allah, inkin haifa wannan kinga saura 9 kenan kou?'' Ya karashe mgnr yana sakar mata murmushi itama ta sakar masa murmushi tayi kissn hannunsa, shi kuma yayi kissn goshinta. "I love you all over of my heart and my mine!" Ta fadi masa cikin muryarta me dadih. Sosai yaji dadih yayi kissn kumatunta kana ya dawo yy kissn lips dinta yace "i love you more than I love my safe my partner...Allah ya fito dake lafia..." Ta amsa da "Ameen..." Kawai ya fashe da kuka kmr karamin yaro, itama ta fashe da kukan, Alhaji abdullahi dasuke tsaye suna hangensu ta jikin kofar dakin, ya shigo yajashi suka fice a dakin, likitoci suka fara kokarin nasu aikin.... Direct masallaci suka nufa shida alhaji abdullahi sukayi alwala suka shiga masalllaci suka dukufa adduarh Allah ya fito da kyautar Allah lafia da dukkanin daukacin musulmai.... Cikin ikon Allah da temakonsa aka samu nasarar ciroma KYAUTAR ALLAH yaranta biyu duk mata, masu mugun kyau. Daman an kawo akwati na kayansu dan haka aka shiryasu cikin kayansu na sanyi masu kyau na alfarma, kalar kayan peach and milk ne aka nadesu a bargon daukar jarirai masu kyau kalar milk, dr hannatu da dr zilai suka fito da yaran a hannunsu su kansu yaran sun kwanta musu a rai ainun sannan suna cike da mamakin yadda karamar yarinya ta iya daukar yara biyu a cikinta, cikin juria da aminci lallai wannan shi ake kira da ikon ubangijin rabbussamawati wal'ardi.... Zuwa lokacin ummih da anty sadia sun iso duk sun zazzauna sunyi jugun jugum Alhaji abdullahi ma ya fito daga masallacin da carbi a hannunsa se lazimi yakeyi yana zaune. Drs din suka nufosu da bbys a hannu, duk miqewa tsaye ummih da Annah da anty rukayya da anty sadia sukayi da da Alhaji abdullahi, dr hannatu tace albishinku...har suna hada baki gun cewa goro... Kawai suka miqa ma ummih baby na farko ta amsa Annah ta miko hannu ta amshi na biyun, sukabi likitocin da ido suna neman karin bayani.... "Sune abinda muka ciro a cikinta, yan biyu ne duk mata..." Cewar dr hannatu. Nan guri ya kacame da murna wadanda ke zaune basu tasoba duk suka taso dan ganin babyns dake hannun Annah da ummih, saboda tsabar murna Annah ta fashe da kuka hadda shasheqa, Anty Rukayya ta shiga rarrashinta Annah tace " barni in kokah rakiya ashe da raina zanga wannan abin arzikin..." Anty Rukayya gaza jurewa tayi itama ta fashe da kukan farin ciki ta amshi babyn dake Hannun Annah , Annah ta amshe tana fadin bari inji dumin abuna... Anty rukayya ta amshe ta hannun ummih wadda ta zubawa babyn indo tinda ta shigo hannunta, babyn ta burgeta ta bata sha'awa kamarta daya da ubanta Raslan kamar yayi kaki ya ajiye, haka dayarma kamarsu daya, bakama iya bambamcesu sede dayar nada bakin tabo ta gefen idonta na dama itace hasanar... Anty sadia ta fice a guje taje ta kirawo RASLAN a masallaci ta kamo hannunsa suka karaso inda suke tsaye da baby a hannunsu idanuwasa ya sauka a kan babys din kawai ya tsugunna yayima Allah sujjada ganin yaya har biyu kuma nasane halak malak, ya daga hannayensa duka biyu sama ya fara jero sunayen ALLAH dari ba daya, har seda ya kai karshe kana yayima Annabi kirari, ya fashe da kuka ya kalli dr yace "Dr ya matata take?" Dr hannatu tace "tana cikin koshin lafia yanzuma zamu fito da ita mu kaita dakin hutawa, zata farka ba jimawa...." RASLAN ya kara godema Allah suko sauran duk hnklinsu na kan baby shi kam hnklinsa biyu ya kasu da kan babys din da kuma kan matarsa. Dr hannatu ta amshi babys din ta bawa RASLAN ya riqesu a hannayensa ta nuna masa hassana kuma ta nuna masa hussaina ya rungumesu a jikinsa dukkaninsu sunyi kama dashi sak duk farare ne tar! Kmr a wanke hannu kafin a taba. Seda ya dauki 5mnt yana kallonsu hadi da musu addu'ur'i neman tsari daga lalacewar dunia, kana dr ta amshesu da kyar ya batasu ta kaisu dakin hutu. Suna nan tsaye aka fito da KYAUTAR ALLAH kwance a kan gado kamar matacciya RASLAN ya zuba mata ido dagani kasan tasha wahala ta fitar hankali, a zuciyarsa ya rinka sa kata albarka. Aka wuce da ita dakin hutu... RASLAN ya dauki waya ya shiga kiran dangi da abokanayen arziki yana sanar dasu KYAUTAR ALLAH ta haihu yan biyu...Annah daman tusa hali ballan tana anci wake itama tini ta fara yadawa, dangi da abokanayen arziki.. ummih ma