← Book details Kyautar Allah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 164

Sashe 147

Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read

tausanta,shide gindi gindi shine damuwarsa kullum, hade girar sama da kasa tayi, rai a bace tace "yanzu banda lafiyarma bazaka tausayaminba...inde bazaka fitaba bazanyi fitsarinba, na fasa..." Cikin tsiwa ta karashe magabar. Nairai-narai yayi da idanuwa kamar zeyi kuka yace "Kiyi hakuri dan ALLAH, sonki da sha'awarkine suke jamin hakan, ina da bukatuwa sosai dake, ko kwanaki biyu dakike gani banzoba, banasone in takura miki, ina sonki ina tausanyi kiyi hakuri dan ALLAH, nima ki tausayamin..." Ya kai hannu ze shafo nononta dake tsaye suna masa daquwa tayi hanzarin ture masa hannunsa tin kafin ya kaiga karasawa, ALLAH yasani ya addabeta sosai, ta fara gajiya kwata kwata ma batason takura a halin datake ciki yanzu. "Fitsari fa nace maka inaji..." Ta fada cikin fada,... Danne bukatuwarshi yayi yace "Tou...kiyi mana plx" ta zuba masa ido se taji tausanshi ya rufeta,,amma nan da nan ta kawar da tausanshi a ranta saboda shi din ba tausayinta yakejiba. "Ka fita to mana.." "To..." Yace kmr wani sauna ya juya ya fice a Toilet din badan yasoba, ya dawo dakin ya zauna, yacema jummai ta kai kata brush dinta, tace tou, ta zuge bag din ta dauko brush dinta ta matsa mata MacLean din Colgate ta nufa toilet din tayi mata knocking cikin matsifa tace waye,,jummai tace "ni ce..." Ta fito ta amsa tace ta kawo mata soson wanka, jummai ta tambayeta wanka zatayi tace "eah...ko baki kawo soso da soap dina bane?" Jummai tace "na kawo..bari in miqo miki.."ta juya ta dauko mata soson da sabulu da doguwar riga dazata saka in tayi wankan, duk RASLAN na kallonta tana tsaye bakin kofar toilet din tana jira Jummai, babu inda yafi kallo a jikinta kamar nononta, sosai yakejin sha'awarta, a wannan,karon duwawukanta ke tsole masa ido. Jummai ta karaso ta mika mata riga da soso da sabulun wankanta ta amsa ta hada da brush din dake hannunta wanda Jummai ta bata ta shige toilet din, ko kallon inda yake batayiba. Jummai ta dawo ta gyara bed din data tashi a kai. 20mnt ta dauka a toilet din kana ta fito bayan tayi wanka da ruwa me zafi sosai taji dadin jikinta duk gajiyar dake jikinta ta ragu, se abinda baza a rasa ba. Ido ya zuba mata tana sanye da doguwar rigar material army green me kananun flowers white and dark purple sosai rigar ta amshi jikinta ainun, duwawukanta yabi da ido , se motsi sukeyi, tana takawa a hnkli, amma duwawuknta da karfi suke motsawa kai kace tana sane take juyasu. Hijjabin jummai ta saka ta nufa dadduma, ta fara kawo sallarh magrib da isha'in jiya da batayiba, ga asubahi kuma ta sameta. Karshen sallarh a zaune ta karasa saboda ji tayi dukta gaji ga yunwar cikinta dake kara kwakularta. Idonshi na kanta se kallonta yakeyi kmr maye. Tana idarwa ta dawo kan gadon ta kwanta tana sauke ajiyar zucia wata zufa ta fara karyo mata, dukda sanyin a.c dake dakin. "Anty jummai karamin sanyin a.c dinnan, zafi nakeji.." Ta fada da kyar, da hnzari RASLAN ya riga Jummai miqewa ya dauko remote din a.c ya kara masa karfin gudu, kana ya dawo bakin bed din yana goge zufar dake karyowa ta goshinta da rigar jikinsa, besan meyasaba takeda mugun jin zafi yanzu, dukda uban sanyin dake dakin amma a haka taci gaba da zufa, jummai ma har sanyi ta faraji ta dauko hijjabinta ta saka. "Me kikeso kici?" Ya tambayeta yana goge mata zufar goshinta. "Black plum dinnan nakeso..." Ta fada tana maida numfashi ji takeyi kmr tayi tsirara saboda zafin dake taso mata. Ido ya zuba mata, shifa a tunaninshi ta manta da abunnan ashe yana ranta. "Jia bansamuba, amma na siyo miki abinda ke kama dashi , bari in dauko miki ki gani..." Ya karashe mgnr yana nufar dan madaidaicin frij din dakin nan yasashi jiya da daddare, ya bude ya dauko ledar ya dawo bakin gadon ya miqa mata ta tashi zauna ta amsa ta bude taga inibi ne, sanyinshi yasata ta fara sha Amma bashi takesoba, se yaji dadih dayaga tana sha, saboda tin jiya bata sawa cikinta komiba se yau, yaji dadih mara misaltuwa, tin jiya shima beciba besha ba saboda itama bataciba bata shaba. Yana zaune yana kallonta tasha inibin sosai, har wani lumshe ido takeyi saboda sanyinsa dake ratsata. "Yaushe zaka kawo min black plum din?" Ta tambayeshi tana kai inibin baki. "Ban samu bane...amma zan kara dubawa, in kinaso se inyita siyo miki inibin..." Ya fada cikin kwantar da murya. Hade rai tayi tace "Ni bashi nakeso ba, d'inyar ai nakeso gaskia ka nemo min d'inyar. " ta karashe maganar tana ture ledar inibin dake gabanta, ji tayi ya fitar mata a rai. Ido ya bita dashi ada de yasan ba haka halinta yake ba, amma yanzu tana neman canza hali, ga matsifar tsiya data koyo ko a ina ta kayo oho. "Kici gaba da shan inibin xan nemo miki black plum din yau insha ALLAH..." "Na koshi ya fitar min a rai, black plum din nakeso..." Tayi maganar tana yatsina fuska saboda aman dataji yana taso mata, Kafin ta ankare ta fara kwararo Amai, da hnzari RASLAN ya miqe ya dauke ledar inibin ya ajeta gefe guda, ya rungumota jikinsa, se amai takeyi a kan bed din idanuwanta na fidda kwalla kmr zata amayar da duk kayan cikinta, cikin hanzari jummai ta taso daga inda take zaune ta karaso bakin bed din tana mata sannu, shima RASLAN se sannun yaketa jero mata zucia fal tausayinta. Ta jima tana aman seda ta amayar da duk inibin data samu tasha kana ta samu sa'ida,,,da knshi ya kimtsa gurin, itama ya kimtsata ya canza mata riga, se sannu yake mata, jummai taje ta amso wani bedsheet a gun nurses ta cire na kan bed din ta canza wanda ta amso,.. Tana kwance a kan jikinsa shi kuma yana zaune a kan kujera, duk jikinta yayi sanyi. Kwantar da ita yayi a kan bed din da niyar yaje ya kirawo dr zilai, jummai kuma tna toilet dan wanke kayan data cire dazu datayi wanka da kuma kayan data bata yanzu da tayi aman. Yana shirin ficewa daga dakin Dan liti ya danno kai cikin dakin Annah na biye dashi a baya tana sanye da hijjabi milk, abaibaima tasa hijjab din kallo daya zaka mata kasan cewa batama hayyacinta kwata kwata, jiya sam batama rintsaba saboda tunanin KYAUTAR ALLAH fuskarta tayi kubul kubul, kamar wadda sanyi ya kama. RASLAN ya bisu da ido, dai-dai Alhaji umar ya danno Kai dakin, Annah ta shiga nuna RASLAN tana fadin "Ka ganshi ko! Gashinan shine nan yace ze kasheni! A kan waccen yar iskar! "Ta karashe maganar tana muna KYAUTAR ALLAH,tin shigowarta idanuwanta suka sauka a kanta. Baki sake RASLAN ya bita da ido, yana tunanin sharri irin na Annah danshi besanma a yaushe ne yace ze kasheta ba. Alhaji umar na shirin bude baki yayi magaba dr zilai ta turo kofa tare da wasu nurses suka shigo dakin Da sallahma, amsa sallahmar duk sukayi. Kana suka gaisa a mutumce, direct dr zilai ta karasa bakin gadon da KYAUTAR ALLAH ke kwance idonta na kan Annartah. Dukkaninsu suka karaso bakin gadon a tare da dr zilan. Tambayarta ya jiki dr zilai tayi, KYAUTAR ALLAH ta amsa da da sauki,. Dr zilai ta tambayeta yanzu ina ke mata ciwo ta girgiza kai alamar bako ina, RASLAN yayi carab ya amshe dacewa "tayi amai yanzu dr, kuma batacin abinci..." Dr zilai ta juyo tayi facing RASLAN dake mata bayani, kana tace "Eah! Daman zata tsinci kanta a wannan yanayin, laulayi takeyi!" A matukar razane duk suka zubawa Dr zilai ido, Ko wannensu fuska dauke da mamaki, amma banda fuskar Annah wadda ke dauke da takaici ta zubawa KYAUTAR ALLAH idanuwanta masu cike da takaicint. Dan liti de se kasa kunne yakeyi saboda besan me ake cewa ba, se bin bakunansu yake yi da ido. Cikin rashin fahimta RASLAN yace "Laulayi kuma dr? Laulayin me?" Dr zilai tayi jim tana nazarin fuskokinsu, tasansu ta riga datasan duk nan babu bare inda jummai da dan liti ba sune ma'aikatan safana family. "Laulayi na ciki....kuna nufin bakusan tana dauke da cikin watanni biyu bane? Yau cikinta ya cika wata biyu cir,,,ni kaina nayi mamakin ganin ciki a tattare da ita, amma nasan ku fulani ne kunawa yaranku Aure da wuri,, amma fa na girgiza sosai, da nakai jininta lab aka turomin da result din tanada ciki ba karamin mamaki nayiba, saboda naga tayi kankanta da daukar ciki gaskia, Amma ba a mamaki da ikon Allah sede muyi fatan Allah ya raba lafia..." Bakin RASLAN ya gaza rufuwa da murna da farin ciki jinsa yakeyi kmr a mafarki ake gaya masa wannan kyakyawan result din yama rasa yazeyi da rayuwarsa domin tsabar farin ciki, itakam KYAUTAR ALLAH tayi shiru tana sauraren me dr zilai ke cewa tama rasa me zatayi murna ko bakin ciki oho. Alhaji umar kam se kallon Raslan yakeyi cike da mamaki, yanada tabbacin wannan aikin na RASLAN ne, tin zuwanshi Annah ta sanar dashi KYAUTAR ALLAH nada cikin shege kawai ya jita ne ya riga dayasan cikin na dansa ne, Jummai ma sosai ta nuna farin cikinta a fili....nurses din dake tare da dr zilai kuwa se kallon KYAUTAR ALLAH sukeyi suna mamakin karamar yarinyar da cikin haihuwa. Annah ta zube kasa ta kurma wani mahaukacin ihu, tana fadin "Shikenan ta debo kin dan shege! Wayyo na shiga ukuna!! Yarinyar nan ta bata min zuri'arh!" Ta hau kuka tana birgima a kasan tiles din dakin. Dr zilai da nurses duk suka zubowa Annah ido, xucia fal mamakin kalaman Annah dr zilai tace "ashe cikin shege be!" Ta fada a ranta da dumbin mamaki a fuskarta, se yanzu take nadamar fada musu taba da cikin da tayi a gaban mutane harda bare. RASLAN ya zubawa Annah ido rai a matukar bace dajin kalamanta da ranshi da lafiyarshi Annah na sheganta masa cikin da yayi shekara da shekaru be samuba se yau. "Gaskia Annah kidena shegantamin ciki!! Cikinane!" Ya fada da babbar murya babu alamar kunya a kwayar idonsa, Annah ta tsagaita da kukanta ta zubawa RASLAN ido tanajin kalamansa na amsa kuwwa a cikin kwanyar kanta,. Duk halittar dake dakin zuba ma RASLAN ido
Chapter 147 · 0% Book details