Sashe 155
Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta kira daddyU ta sanar dashi shi kuma ya kira sauran yan uwan nasa ya sanar dasu, alhaji abdullahi ma dukya kara kiransu ya sanar dazu zuciarahi fal farin ciki shima yaga yan jikokinsa. Kan kace kwabo asibitin ya fara cika da bataliyar safana da kuma abokanayen arziki saif ma ranar yazo, zuwa lokacin ta farka an bata babys dinta ta amshesu ta fasheda kukan farin ciki se kallonsu kawai takeyi tana ayyanawa a ranta duk wadannan natane, tayi godia ga Allah sau ba adadih, RASLAN ya hadasu da babys dinnasa ya rungume beji kunyar kowaba , sede yabar KYAUTAR ALLAH da kunya, annah tazo ta amshe yayan tanata jero masa farillan zagi, ummih de knta na kasa kar kaso ka bincika zuciarta dan farin ciki...duk wanda yazo ganin bby fah Annah taki bada babys ta kamasu ta riqe a hannunta gam babu me amsarsu da ance ta kawosuma seta dura maka zagi, hk kowa ya hakura ya bar mata baby, aka basu zam-zam kafin nono yaxo, da nonon yazo kuwa suka cafke suka hau tsotso RASLAN se kallo yakeyi tanata yatsina fuska saboda zafi Amma haka nan ta jure bata da yadda zatayi Anty Rukayya ta sata a gaba... Satinsu daya a asibitin aka sallamesu zuwa gidan Annah suna zuwa sukaga an canza komi na gidan ansa sabbi masu kyau da tsada an canzana gidan penti da de sauransu, duk aikin RASLAN ne, Annah tayita sanya masa albarka. Nan aka fara shirye shiryen suna daza a gudanar nan da sati me zuwa. .... Raslan ya saki kudi na fitar hayyaci dan gudanar da bikin suna, yayi other din manyan zannuwa da laces daza a raba ga duk wanda yazo bikin sunan, ciki Hadda mota kirar 206 da de sauran motoci na mata za a raba game rabo, da gidaje, duk daga bangaren Alhaji musa kyautar gida da motan suka bullo. Ummih na nan da ita za ayi shagalin sunan ta sanar da hajiya saude ta kd tace itama zatazo, duk ummih tayi tata gayyar. Ihsan kam data samu lbrin haihuwar a gun humaira matar saif, karamin haukane kawai batayiba taje ta samu bokannan ta rinka sirfafa masa zagi, da kyar maryam ta lallasheta, ta jawota suka dawo gidanta tayi zaman dirshan a kasa ta fasa ihu, maryam ta shiga rarrashinta, rnrfa seda maryam ta kira malamin anguwarsu yama ihsan rukiya ko aljnune, malam ta gaji da karatun iskokan basu saukaba ya yayyafa mata tiraren aljanu amma duk basu saukaba hakanan ya barta tanata haukanta, maryam ta zauna ta raf uban tagumi ta zuba mata ido saboda tayi iya nata amma bata hakuraba, dan haka ta batta inta gaji dan kanta ta bari, ai kuka ba kida bane, ko kidama aka gaji ballan tana kuka..... *saura kirisss....... Tnks for the love fans. *PAID BOOK...500 ONLY...08136349646* SAADATU BINTU ABDULLAHI Ranah bata karya sede uwar diya taji kunya! (Inji bahaushe) Ranar jumma'ah akayi bikin sunan yaran KYAUTAR ALLAH da alhaji RASLAN, inda hassana taci sunan Annah wato Aisha aka lakaba mata (Meead) ita kuma hussaina taci sunan Rukayya (wato mahaifiyar KYAUTAR ALLAH kuma sunan KYAUTAR ALLAH) ana kiranta da (Hannaah) kowa ya hallara dangi da abokanayen arziki, hadda na tsiyarma duk sun hallara, Ciki kuwa hadda ihsan Da qawarta Maryam wadanda gulma da kallon kwakwaf ne ya kawosu. Fatima da mamanta ma sun hallara, sun kawo kyaututtuka ba gani na fada, hajiya saude ma tazo da kyautar ta me tsoka, da matar saif dashima Saif din, duk sunzo da sha tara ta arziki. KYAUTAR ALLAH ta cancare cikin lace me tsadar gaske kalar maroon color me flowers milk, cikin kayan da Raslan yase mata, wuyanta kuwa gold ne kawai ke magana, haka hannunta tako ina de tasha ado ga kunshi hannu da kafa, sumar kanta tasha gyara, ta hadu iya haduwa kmr a saceta a gudu, hatta takalmin data saka a kafarta abin kallone, haka suma jariran duk an musu ado na fitar hankali kafa hannu wuya duk gold ne a jikinsu, an ninka tsaro matuka a gidan dama duk anguwar saboda sunan cuteness din RASLAN. Shima knshi angon karni ba abarshi a bayaba se cancara ado yakeyi, da kyautar ALLAH ta canza kaya shima ze shiga ya canza kaya haka suma babys se canza musu kaya akeyi, a awa daya sun chanza kaya yafi kala goma, duk inda sukabi masu videos nata binsu suna daukarsu, anty Rukayya da Anty sadia suke riqe da babys din. Annah ma ta cancare, ta cakare taci ado cikin dankareriyar shaddarta me walwali,,, ihsan de duk inda sukayi se binsu takeyi da ido ita da qawarta maryam Zuciyar ihsan se barazanar tarwatsewa takeyi, musammanma dataga anata hidimar arziki RASLAN ya balle hannu se barin kudi yakeyi kmr besan zafinsuba, daddyU yazo ya sauke kudi kirar dala dalah jaka daya yace na bbys sannan da company dinsa dake Lagos guda biyu yace duk na babys, DaddyM kuwa tashi KYAUTAR ta gigitace company dinsa na hada jirgin sama yabawa jariran kyauta, daddyH kuwa gidajensa manya manya guda biyu dake waje ya bawa jarirai kyauta da makudan kudade, Alhaji abdullahi KYAUTAR motoci ya basu masu kyau da tsada se kudade... Duk wanda yazo a family seya ajiye tasa kyautar zuciar ihsan kmr zata fashe nan taji tana sha'awar itama ta haihu kodan wadannan kyaututtukan da KYAUTAR ALLAH da yayanta sukasha, abunfa zar sha'awah ga masoya amma abin bakin ciki ga makiya...abinci kuwa anyi yafi kala talatin, ko ince ana kanyi, sannan ga drinks iri daban daban se abinda kkeso zakaci zakasha masu serving ma daban akayo hayarasu sunfi mutum arba'in, saboda yawan mutanen dake gidan ba kadan bane (knusan mutanenmu na yanzu da kwadayi inba kana dashiba babu meyi dakai, ko sha'aninka ba azuwa sena masu shi, saboda kwadayi da son abin dunia, pls mu gyara halinmu talauci jarabawace hakama arziki jarabawace, Allsh yasa mu dace) A cikin taron jama'arh nan da Annah ta kyallara ido taga ihsan tasha zagi da habaici har ce mata ta rinkayi juya, wadda bata haihuwa... Sosai ihsan ta kule Amma de ta shanye saboda bata da yadda zatayi... Tin safe akayi walima aka rarraba kyaututtuka na fitar hankali wasu gida suka samu wasu motoci wasu atamfofi wasu laces wasu kuma riguna jallabia wannan KYAUTAR daga hannun ummih ta fito, wasu kuma kyautar kudade, wanda ya fito daga hannun Anty Rukayya.... Da yammaci RASLAN ya kama tamfatsetsen hall a can kuma aka yada zango, Sukayi shiga ta Alfarma shida KYAUTAR ALLAH da cuteness dinsu, aka kira mawaka daban daban ranar kam daloline ke magana, bandir bandir aketa ballesu ana watsarwa... RASLAN ya shifa watsi da bandir bandir na dollars yanama KYAUTAR ALLAH liki dukda ba rawa takeyiba, hajiya Annah kuwa se gyada kai takeyi Anty Rukayya na mata liki,, Ihsan kam na gefe zuciarta na barazanar tarwatsewa... Ansha hotuna daban daban da video iri iri,..basu suka bar hall dinnanba se 12:am suka nufa gida daman KYAUTAR ALLAH duk a gajiye take, kwancia kawai tayi tayi baccinta tabar su Anty Rukayya da anty sadia da cuteness dinta. Ihsan kam daganan asibiti suka nufa ita da maryam saboda a mota ta zube a sume saboda bakin ciki... Seda akayi sati cir ana bikin sunan a sati na biyune mutane suka fara watsewa kowa ya kama gabanshi amma banda Anty Rukayya wadda tace bazata koma gida ba se KYAUTAR ALLAH tayi arba'in, ... RASLAN kam ya zama kmr wani na mamajo tin kafin yan biki su watse yaketa bin KYAUTAR ALLAH duk inda tayi seya bita mutane se binsa sukeyi da ido ciki hadda ummihnsa, daya samu mutane suka watse kuwa ai nan abun nashi ya karu yaci uwar nada..... Sati daya period din KYAUTAR ALLAH yayi ya dauke, anty rukayya na ankarewa da hakan kuwa tacema KYAUTAR ALLAH kada ta kuskura ta bari RASLAN ya gano hakan, danta kula rawar kanshi yayi yawa, a hakanma dukya kosa su kebance ta bashi gindi yaci gaba da gabza,,, Anty Rukayya ta matsa sosai gun gyarama KYAUTAR ALLAH jiki da kayan gyara masu kyau da inganci daman tini ta tanadesu, musammanma na matsi dana karin ni'ima dukdade bada kanta ta haihuba Amma ai tanada bukatar gyara, Aiko ta fara shan gyaran dan a sati daya taji jikinta ya canza kullum cikin canza pant take saboda yoyon datake tayi kmr an kunna famfo... ALLAH ya bata lafiyar shayarwa se feeding babys dinta takeyi da nononta dayake tanada ruwan nono sosai, sannan kullum cikin mata kunun kanwa takeyi... ALLAH ya daurawa Anty Rukayya son jarirannan ita da Annnah bnsan gwaniba, da kuma fahima da sadia kullum cikin kira suke suna tambayar lafiyar cuteness. Kwanan ihsan biyu a asibitin ta kira RASLAN tace masa bata da lafia tana asibiti, yace ALLAH ya kara sauki..tayi jim kana tace "Baza kazo kaga jikin nawa ba,kwana na biyu fa ina kwance.." Da kmr zece eh se kuma yace "turamin adress din asibitin zanzo anjima.." Yana fadar hakan ya katse wayar, ba jimawa kuwa ta tura masa da adress din asibitin. Da yammaci ya shirya cikin kananan kaya wadanda suka amshi jikinshi yayi kyau ainun. Ya fito falon se sheki yakeyi jikinsa nata barin kamshin perfume dinsa.. Zaune take a falon ita da anty rukayya wadda ke riqe da Meead ita kuma tana riqe da hannaah tana bata nono, Sanye takeda doguwar rigar atamfa me zip a gaba saboda bada nono Aka mata zip a gaban rigar, kanta babu dankwali sumar knta se sheki takeyi, ya karaso falon idonshi na knta, itama dagowa tayi ta zuba masa ido kallo daya ta masa taga yayi mata kyau Ainun. Karasawa yayi ya amshi hannaah dake hannunta ya amshi meead dake hannun anty Rukayya, duk ya manna musu kiss a kumatu ya rungumesu a jikinshi duk abinda yakeyi idonshi na kan KYAUTAR ALLAH, wadda ke maida nononta zuwa cikin riga., lashe baki yayi saboda idanuwansa dasuka sauka a kan nononta dake zubda ruwa, saboda hannaah ta jawoshi bata shanyeba ya amsheta. "Zan sha nono.." Ya fada a hnkli ta yadda ni dayace zanji, kasa nayi da kaina danni a sorace nake dashi Anty Rukayya tacemin ina bari ya kusanceni zanyi wani cikin , niko banaso saboda nasha matukar wahala.. Murmushi yayi idonshi na kaina ya kara kissn yaranshi kana ya mikawa anty rukayya Meead ni kuma ya dawomin da