Sashe 162
Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read
lantana ta tambayeta ya jikinta, ta amsa da dasauki, dan tasan RASLAN ne ze gaya mata bata da lafia.. Dauko yaran tayi duka suka fito falon bahbah lantana na biye dasu , har suka iso dinning ta zauna da yayan a cinyarta , bahbah lantana tayi serving dinta, ta fara cin abincin yaran na kallonta ta sa musu a baki suka cinye, dan suna dan cin abinci zuwa ynzu. Bayan ta gama cin abincin ta basu nono suka kama cikin zumud'i ta zuba musu ido zuciarta fal adduarh ALLAH ya tsare mata yaranta daga fadawa abinda ubansu ke aikatawa. Ranar wuni tayi zuciarta da dan sassauci. da lokacin data keda lecture yayi tayi wanka ta shirya ta fice a gidan nan gida ta bar yaran nata da bahbah lantana.... Da rana ya dawo yafi a kirga be gantaba tana school ya addabeta da kira taki dagawa kuma tana gani, hk ya koma office dinsa jiki babu dadih. Da daddare ba gidan yakeba amma seda yazo kmr maye, ina dakina na rufeshi gam da key yazo yayita bugawa inaji nyi bnza dashi ya gama magiyarsa ya fice a gidan zuwa gidan ihsan gashi yna cikin tsananin bukatuwa kuma hnklinsa baya kwanceba, ya samu ihsan da niyar ya rage zafi ita kuma bata da lafia ciwon ciki ya tasata gaba kwanan nan ga jinin dataketa zubarwa babu kakkautawa , ta fada masa yace su shirya suje asibiti gobe. Washe gari da safe suka shirya sukaje asibitin, likita ya didduba ihsan nan ya gano maganin hana daukar cikin datasha ne a baya, ya lalata mata mahaifa (ta denasha ynzu danta samu haihuwa) dr Hussain ya zayyannoma RASLAN bayani dallah dallah, yace Dole ynzu sede a cire mata mahaifar ma baki daya. RASLAN ya juyo ya kalli ihsan tayi kasa da kanta. "Ashe kin dade kina cutata? To bani kika cutaba kanki kika cuta..." Ya fadi hkn a matukar hasale, be tabbatr ihsan munafuka bace se yau. Fashewa tayi da kuka kmr ranta ze fita se ynzu take nadamar abinda ta aikata a baya gashi tajawa knta, babu ita babu haihuwa har abadan. Tashi yy ya fice a office din a fusace, ta mike ta biyoshi tana Kuka, suka shiga mota suka fice a asibitin a motar ma se kuka takeyi, RASLAN beyi packing a ko inaba se a gidansu ihsan, ta juya ta gansu a kofar get din gidansu. " na sakeki saki daya.." Ya fadi cikin bacin rai. Ta juyo ta kalleshi a razane ta kara fashewa da kuka kmr ranta ze fita. "Dan ALLAH kayi hakuri, karka sakeni ..." Ta fadi a gigice. juyowa yy ya zuba mata ido, yauce rana ta farko data taba bashi hkri a tsawon zamanshi da ita , haka kawai ya farajin tausanta a ranshi ganin yadda taketa kuka kmr ranta ze fita, gudun kada zuciarsa ta karaya yasashi daka mata tsawa "banason kukanki! Ki fitarmin a mota nace, na sakeki saki daya!!" Ta kara fashewa da kuka hadi da masa magiya, ya daka mata tsawa tsole ta fice a motar tana kuka ta shige gidansu, RASLAN ya jima a bakin kofar get din kana yaja motarshi yabar harabar gurin. Ihsan na shiga gida ta fashe da kuka ta sanar da mahaifiyarta komi, hajiya hadiza ta fashe da kuka ta kira ummih ta sanar da ita, ummih tace karsu damu zata kirashi, aiko ummih tayi kiran duniarnan RASLAN yaki dagawa, kuma yna ganin kiran ummihn saboda yasan kwanan zancen ne yasashi yaki dagawa, direct office dinsa ya Nufa,be tashiba se 6:pm ya nufa gidansa zucia dauke da fargaba, ya shigo gidan tana zaune a falo, jikinsa na rawa ya karaso idonsa na knta, tasa wasu riga da wando najan magana, ya zauna kusa da ita ya rungumota jikinsa. Kmr an tsunguleta ta mike ya zuba mata ido "Me ke faru ne pls? Ko jikin ne? Ya jefo mata tambayar jikinsa na rawa, batabi ta kan ma me yake cewaba ta fice a falon ta nufa dakin yaranya ya biyota , tayima dakin key ta zauna gefen bahbah lantana wadda ke riqe da twins RASLAN yahau buga kofar dakin ta hana bahbah ta bude masa, itama taki budewa harya gaji ya wuce jiki bb laka. Bahbah lantana ta tambayi kyautar Allah me yasa ta masa hk, murmushi tayi tace "Ba komi bahbah, muna yar wasane nidashi..." Bahbah ta jita ne kawai. Hk tayita gwara masa kai, sam batabi ta knsa, a ynzu har tsoronta yakeji, ya rasa ina zesa rayuwarsa yaji dadih. A hk sukayi sati daya a dakin yaranta ma take kwana bahbah ta mata tambayar duniarnan kan meyasa hkn tace mata bakomi. KYAUTAR ALLAH na ankare dashi ynzu be zuwa gidan ihsan ko meyasa bata saniba. Kullum cikin adduarh take ba dare ba rana sannan bata rintsawa da daddare kwana take tana gayawa ALLAH damuwarta hadi dama iyayensa da Annahrtah da duk " Al'ummar musulmi Adduarh. Ihsan taje aka mata cs din aja cire mata mahaifir, tayi jinyarta harta warke aka sallamesu, suka koma gida. Kullum ihsan cikin kukan rashin RASLAN take, batasan yanada muhimmamci a rayuwartaba se a ynzu da basa tare, kullum cikin kiran lambarshi take baya dagawa, sede tayita kiran ummih, ummihn na bata hakuri, dan itama be daukar wayar tata. Mahaifin KYAUTAR ALLAH yazo ya dubata dashi da Anty fahima rnr nan suka wuni se yamma suka hau hnyar komawa kaduna. A yan kwanakinnan se baki iri iri KYAUTAR ALLAH keyi dan hk dmwarta ta ragu, bata taba barin kowa ya gano damuwartaba ballan tanama a tambayeta meke damunta. Anty sadia ma tazo ta wuni nan, ta kawowa KYAUTAR ALLAH magungunan mata masu kyau ta amsa ta mata godia sosai itama nan ta wuni kana ta bar gidan domin laulayin ciki takeyi. 8:30pm Zaune take a falonta da charbi a hannunta se lazimi takeyi yaranta na gun bahbah lantana sunyima baccih, tana shirin mikewa kenan ya shigo falon, sam batayi tsammanin zezoba tasha yana gidan matarshine. Ta juya da sauri tana kokarin barin falon ya karaso ya kamo hannunta, ta fisge ya kara riqo hannun nata gam a cikin nasa. "Dan dan darajar iyayenki kiyi hkri ki bani mintina biyar inaso ne muyi magana..dan Allah da manzanninsa badan niba, nasan na miki babban lefine saboda fushi kikeyi dani..." Ya marairaice kmr ze fashe da kuka. Ta gefen ido ta kallesa taga yayi wata uwar rama yayi baki, duk ramar datayi bata kaishi rama ba se taji tausansa ya cika mata zucia. Jin tayi shiru ya bashi karfin guiwar Kamo hannunta ya zaunar da ita a kn daya daga kujerun dake falon, ya raba gefenta ya zauna ya kamo hannayenta duka biyu, jikinsa har yana kakkarwa. "Dan ALLAH ki gayamin lefin dana miki, nayi miki alqawarin bazan karaba har abadan, sannan zan rokeki gafara, dan ALLAH ki gayamin lefin dana miki, axabar dakikeyimin ta isheni haka, kin sani a uquba, kin hanaki ganinki, kuma kin hanani saduwar aure dake, har ta kaiga kin hanani ganin yarana dana haifa dake kanki, wannan azabar ta isheni, Wallahi kwara kimin komi a kan wadannan abubuwan dakike yimin, kin hanani jikinki bayan na saba dake, inajin dadinki, kin hanani, nasan ba banzaba, na qurekine saboda kinada tsananin hakuri, ki gayamin me na miki yau dan Allah dan darajar mutumcin iyayenki?" Ya karashe mgnr kwalla na tarar masa a ido. Kanta na kasa ko kallanshima batayi ba, haushima taji ya fara bata saboda abinda ya aikata ya dawo sabo dal a zuciarta. "Ni bakayimin komi ba," ta bashi amsa a takaice. Ya zubawa karamin bakinta ido, da kirjinta dake cike taf. "Kawai kinasone ki wulakntani?" Ya fadi murya cike da rauni, dagowa tayi ta kalleshi bata tabbatr namiji beda kunya ba se yau, wai tanasone ta wulakantashi bayanshi wulakncin daya mata bazema faduba, ko a mafarki akace mata ze iya bawa wata mace jikinsa bazata yaddaba ashe ba hakan takeba, shiyasa akace namiji, bakin maciji. "Hmmm..." Kawai tace idonta na knsa. Hmmm din nata ya bashi ma'ana daban daban sannan ya kara tabbatr masa da lefinsa babbane, duk zurfin bincikensa ya gaza gano wani lefi ya mata. Zamowa yayi kasa ya tsugunna a kan guiwowinsa ya kamo hannayenta duka biyu ya fashe mata da kuka yana fadin "Dan darajar iyayenki ki gayamin me nayi miki..dan ALLAH, ki yafemin dan darajar ma'aikin ALLAH ki yafemin , bazan karaba, na tuba! na tuba! Wlhy na tuba!! Nasha wahala! In kika kara azabtar dani mutuwa zanyi!!!"' Ya fadi hawaye na zirya a kan kuncinsa, yana saukowa bisa hannayenta. Bin hawayensa dake zirya a kn hannayenta tayi da ido, ta dago ta kalli kwayar idonsa da gaske kuka yake mata, ji tayi zuciarta tayi sanyi amma batajin zata iya yafe masa, duk abinda take masa tanayi ne danya gaji ya saketa ta huta da auren sa na mazinaci... Ya cigaba da mata magiya tayi shiru kawai tana jinsa harya gama ya zarce da romances dinta kmr mahaukaci, duk abinda yakeyi sam taki tayashi dukda tana cikin bukatuwa dashi, yayi juyin duniar nan taki mayar masa da amsa, shi yayi kidinsa yy rawarsa se iface iface yakeyi jikinsa na bari, shima dan bata da yadda zatayine, ta fashe da kuka saboda haushin knta ma taji data yadda ta bashi jikinsa. Duk duniar dayake ciki hkra yy ya cire burarsa a gindinta ya shiga bata hakuri,. Batama sauraresaba ta nufa bedroom dinta ta fada bathroom nan ta fashe da kuka tayi kukanta ma'ishi kana tayi wankan tsarki. Tin daga ranar ma bata kara bashi jikintaba, shida ita se kallo, aiko ta kara haukatashi danta masa dandani haukace. ana hk akasa ranar saif da fatima, ashe tini sun dinke se ynzu mgna ta fito, ansa ranar biki 1 month aiko humaira kmr zata haukace, da kyar aka samu ta natsu. RASLAN ya kira anty Rukayya ya sanar da ita abinda KYAUTAR ALLAH ke masa, ta kirani ta tambayeni me yayimi nace mata ba komi ,nan ta rufeni da fada hadda zagi kmr Annah part 2, ganin ta harzuqa yasani saukowa na hkra kawai nasawa kaina salama amma ina kallonshi da abin sannan in mukazo kwanciar aure bn tabuka masa komi, wasu lokutan har kuka yake yimin. Ana hk bikin fatima ya matso tin ana saura 3days na masa mgna kan ya barni inje gobe,