Sashe 119
Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read
in fada tekon maliya inyi wankan tsarki in lafta muku mutumci, lutsum lutsum*....... KYAUTAR ALLAH... *PAID BOOK..500 NAIRA ONLY.. 08136349646..* *Bana edeting*.... SAADATU BINTU ABDULLAHI Alhaji umar ya kalli Raslan, yaga ya wanisha mur ya hade girar sama da kasa , dukda yana mahaifinsa Amma seyajima shakkar yace masa ya saki KYAUTAR ALLAH, saboda yadda ya hade rai fuskarnan babu Annuri seya zama kamar wani qasurgumin namijin zakin daya shekara dubu a jeji, yana farauta, irin wanda ya gagari duk wani me rai. "Bada kai nake maganaba!" Annah ta kara daka ma umar tsawa jin yayi shiru be zartarda abinda ta umurcesaba. Firgigit Alhaji umar yayi ya kalli Raslan cikin sanyi da san yayawa, yace "Ka saketa..." Duk wata halitta dake dakin zubowa Raslan ido sukayi, wanda ya hade girar sama da kasa, kai kace mala'ikun mutuwa Aka Aika masa, ya harde hannayensa a kirji ya daura kafa daya bisa daya, yayinda bayansa ke jingine da bangon dakin har zuwa lokacin. Ihsan tayi shuru, hadi da yin kasaqe, dukta qosa taji meze fito daga bakin Raslan inda so samuntane kawai taji yace "Na saketa saki uku!" Har abadan kenan. Wata irin Ajiyar zuciya ta sauke,, hadi da dafe kirjinta tahau jero addu'ur'i kan taji ya furta wannan kalmar, da tunaninta ta bata. Raslan yayi shiru kai kace badashi Daddynsa ke maganaba. "Dan kutmar ubanka bada kai ubanka ke maganaba! Ko rashin tarbiyar hadda ubanka zakayimawa, in ni ban isa dakaiba ai ubanka gashinan ya isa dakai, kamar yadda ya umurceka kawai ka sakarmin jikata, tinda ba jini kuke da hantaba, ballan tana ace ba a rabaku..." Annah ta fada tana jijjiga rai a bace, kawai so takeyi Raslan ya sakar mata jika, ita knta in za a ritseta a kan meyasa takeso Raslan ya saki KYAUTAR ALLAH hujjarta dayace zuwa biyu. Na daya saboda Ummih, na biyun saboda raslan dan iska ne, acewarta. Raslan ya maida fuskarsa gefe guda kamar badashi ake maganarba, tin a nan ihsan ta sare dan tana hango Alamomin bedama niyar yin sakin, jikinta yayi sanyi. Ummih dake tsaye idonta tar a kan Raslan, harga Allah tanaso ya saketa kodan ta huta da matsalar Annah, hadda Auren dake tsakanin Raslan da kyautar Allah yakesa Annah kwata kwata bata sassautawa Ummih, kafin Auren tadanfi samun sassauci daga gareta, dukda ko babu auren na KYAUTAR ALLAH da raslan sam Annah ba ragawa Ummih takeyiba. Gaf ilahirin halittar dake dakin basuson rabuwar KYAUTAR ALLAH da Raslan, inka cire Annah da ihsan da ummih...Anty Rukayya tafi kowa son Auren KYAUTAR ALLAH da Raslan ya daure har Abadan. Haka itama Anty Sadia, da dukkanin mazan duk sunason Auren kodan kara karfafa zumuncinsu. kowa zuciyarsa cike takeda kunci saboda Annah ta matsa dole se Raslan ya saki KYAUTAR ALLAH, umarnin annah babu sha babu ketara ruwa. Abinda yasama tabar Auren ya jima dan basuyi ido biyu da Raslan bane. A bangaren KYAUTAR ALLAH tini ta bude idonta a kan Raslan tana jira taji ko ze saketa, dukda da bacin ransa dake tattare da ita, wanda ya jawo tsanarsa ga zuciyarta seda taji bataji dadin yadda Annah tace dole ya saketaba, ba son Daddynta takeba tabbas tausayinsa take kuma tausayi yafi so daraja da kima ko a mizali, saboda so na gushewa Amma tausayi baya taba gushewa ga zuciyar dan Adam inhar jijiyoyin jikinsa na bayar da jini. Tausayi shine Ainihin soyayya ta gaskia. bason daddy takeyiba kaunarsa takeyi, kaunarce ta disashe a ranta Amma tausayinsa na cikin zuciyarta, kawai taji ta tsanesane saboda shi baya tausanta kamar yadda ita take tausansa. Rintse idanuwanta tayi gam, tunawa da tayi da azabar da yayi mata dukda dumbin magiyar data rinka masa amma sam be tausaya mataba, sema yayi biris da ita. Dan haka tafi tunanin sam Daddynta baya sonta. "Na tsaneka daddy saboda baka tausayina!" Ta furta a bayyane saboda disashewar muryarta, sam babu wanda ya samu danar jin me take cewa. hawaye ne ke zirya a gefe da gefen idanuwanta, sauri tayi ta kauda fuskarta gefe ta yadda babu wanda ze gane kwallar tata. "Dan ubanka bada kai Ake maganaba!" Annah ta kara dakawa Raslan tsawa wanda yy gefe da fuskarsa, dukda yajita Amma ko juyo da fuskarsa beyiba, kai kace da gunki Ake magana. "Umaru kasa yaronnan ya sakarmin jikata, tinda ba tare uwarsa ta kawosu duniyaba, in kuma taren ta kawosu se inji...Kai yau ko tare uwarsa tsohuwar karuwarnan tayi naqudarsu zuwa duniya seya sakarmin jikata yau Yau dinnan babu ketarewa..." Annah ta fada fuska babu alamar wasa. Sam yaran nata basu taba ganin serious a kan fuskartaba kmr na yau, dan haka se jikin kowa yayi sanyi a dakin, tabbas babu makawa yau da wuya Raslan ya ketare,... "Ka saketa..." Daddy ya kara furta masa umarnin da mahaifiyarsa ta bashi, shima ya bawa nasa dan, a wannan karon babu sanyi a tattareda muryarsa. Still raslan ko gezau beyiba, kai ka rantse da Allah ma badashi Ake magana, ko a hularsa. Ran Annah ya kara harzuqa ya baci ganin Raslan na neman maida ita yar iska, ta kudurta a ranta yau zata kawo karshen iskancinsa abinda yasa duk iskncin da yake mata ta rinka daga masa kafa kenan saboda tanada inda zata fanshe. "Wallahi na baku minti biyu kusa yaronnan ya sakarmin jika ko in tsine muku Albarka dukkaninku, inhar ni na haifeku kuna tsoron tsinuwata kawai kusa yaronnan ya sakarmin jika! " ta fada babu Alamar wasa, a tattare da ita, serious dintama yaci uwar nada, dan yanzu fito musu tayi a Ainihinta na Aishatu. Hankalinsu duk ya tashi saboda jin ta Ambaci tsihuwa kuma babu Alamar wasa. Alhaji unar jikinsa har yana rawa ya kai dubansa ga Raslan yace cikin tsawa "A kan ka uwata bazata tsineminba...ka saketa nace ko in tsine maka!" Yayi directing dinsa babu Alamar wasa rai a bacr. Juyowa Raslan yayi a matukar razane jin kalmar data fito daga bakin mahaifinsa da zafi zafi, na ze tsine masa, sam bega Alamun wasa a tattare da mahafin nasaba. Nan da hankalinsa ya tashi, ya gaskata cewar abun da gaskene dan ada ya dauka kawai zeyi wasa da hankalinsune yayi tafiyarsa, kuma a basa matarsa dole. Bashi kadaiba duk ilahirin halittar dake dakin seda hankalinsu ya tashi inka cire ihsan. Ummih knta tashiga damuwa ganin damuwa da tsantsar tashin hankali a tattareda dan nata, Amma ga fiti tafiso Raslan ya saki KYAUTAR ALLAH kowa ya huta ta gajida gutsiri tsoma. hatta na'im seda ya natsu yashiga taitayinsa, yayi shiru ya zubawa Raslan ido, cikeda tausayawa harga Allah duk fam dinsu yafison Raslan saboda beda damuwa gashi dason dan uwa a takaicede yanada zumunci sosai .... Haka kawai taji gabanta ya yanke ya fadi, dajin furucin Annah, tini ta goge hawayenta, ta dawo da dubanta Ga Raslan, wanda zuwa yanzu fuskarsa ta canza kala zuwa ta tausayi, da tsantsar tashin hankali... Girgiza kai kawai ya shigayi saboda harga Allah bakinsa baze iya furta mata kalmar sakiba, ya riga yakamu iya kamuwa, ji yakeyi a kan ya asashi ya saketa kwara kawai a kashesa Ya zamana baya numfashi a doron duniya, domin kuwa da ransa be taba iya sakinta, yana gani ta Aura wani yaje yayita cinta, Ai abindama baze taba yuwwaba kenan, inko ya saketa to tabbas macewa zeyi. Ihsan ta zuba masa ido tana murmushin mugunta a zuciyarta, ga dukkan alamu mijinta na gab da dawowa tafin hannunta, dan tanada tabbacin inde yana tareda KYAUTAR ALLAH sam bazatayi tasiri a garesaba, karshentama yazo, musammanma yadda taga Alamun gaban macen tasan mijinta dolema ya haukace a kn KYAUTAR ALLAH, saboda shi ya fara Amfani da ita a doron duniya, abinda yafi komi tsaya mata a rai kenan da ranta taga mijinta yayi Amfani da kishiyarta sannan babu wanda besan cewa shi ya fara Amfani da itaba, Itako a bayyane yake mijinta shida knsa yasan bashi ya fara Amfani da itaba, ko wannan ya isa ihsan ishara a doron duniya. Kafin taga gaban KYAUTAR ALLAH bataji zafi sosaiba bisa ga yanzu dataga gaban nata a memakon Abin ya damu KYAUTAR ALLAH a matsayinta na Kishiyarta se Abun ya tsayawa ihsan a rai, kuma tabbas ya tsaya mata a ran Ainun, kishiyartade kamilah ce ba kmr itaba ballagaza wannan kuwa a bayyane yake, kwad'o yafi gaya. "In be saketaba zan iya mutuwa!" Ihsan ta fada a ranta nan da nan wasu kwalla masu zafin rad'ad'i suka shiga zirya a kn kuncinta. "Umaru!" Annah ta kira sunan Alhaji umar babu alamar wasa. Jiki na kakkarwa Alhaji umar ya Amsa da "Na am Annah...." "Kasa danka ya sakarmin jikata Nace, bazan kara maimaita makaba sede kaji tsinuwata a gareka..." Annah ta kara fadi babu wasa. Hankalin Alhaji umar ya kara tashi dajin kalaman mahaifiyarsa a karo na biyu. "Ka saketa nace Muhammad!" Daddy ya kara fadi hadi da daka masa tsawa. Kawai se Raslan ya zube kasa still yana girgiza kai ba tare dayace komiba, se Aikin girgiza kai kawai yakeyi. Dakin ta dauki tsif yayibda kowa da abinda yake saqawa a cikin zuciyarsa, musammanma mazan da bakinsu ya mutu suka gaza mgna, jikinsu ya dauki sanyi. "Ka sake ta dan ubanka!" muryar ummih ta karade dakin, yayinda muryarta tayi Amsa kuwwa a dakin , Kai dajin yadda tayi mgnr kasan *cikin zafin rai take Ainun* . Kamar saukar aradu kowa yaji muryar ummihn. Ihsan kan tsabar farin ciki seda ta murmusa, ummih bata taba burgetaba kmr yau. KYAUTAR Allah kuwa a gigice ta dawo da dibanta daga knta Raslan zuwa kan Ummih... "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!" Itace kalmal data fito daga bakin Raslan murya na rawa, hankalinsa a matukar tashe, yayindayake zube bisa guiwowinsa, ya daura tafikan hannayensa kan cinyarsa, kawai seya fashe da wani matsakaicin kuka me cin rai, yana girgiza kai... Dole duk wani me imani ya tausa masa a dakin Amma banda ihsan, wadda bakin ciki ya rufeta, kawai seta fara ganin juwa dukda tana a zaune, ganin mijinta na kuka a kan wata banza karamar yarinya, yar da bata wuce yar cikinsaba ko wannan bacin cikin Allah ya batta dashi ya isheta isharah. Duk wani wanda yaji tausansa bayan KYAUTAR Allah yake, hatta ummih data haifesa KYAUTAR Allah tafita jin tausayinsa, musammanma dataga hawaye na zirya bisa kuncinsa yauce rana ta farko tin tadowarta data taba ganin hawaye