Sashe 143
Kyautar Allah Complete Hausa Novel · about 8 min read
a hankali a hankali taku uku hudu seta zauna ta huta tana maida numfashi se uwar zufa takeyi kmr wadda tayi karya aka kamata. A haka ta gama saukowa kasan a matukar galabaice Annah dake zaune kan kujerar 3sttr tin sakkowarta ta zubo mata ido, tana kallonta se zama takeyi tana hutawa harta karaso falon se nishi takeyi tana zufa ta karaso ta zauna kujerar dake facing Annah ta gaidata, Ansawa tayi idanuwanta na kan hannayenta dake bisa cinyoyinta. Sosai Annah ta kureta da ido musammanma yatsun hannunta dataga sun kara cika ba yadda tasansuba, kuma ita ta rame a jiki Amma yatsunta sunyi kiba, abinda yafi komi damunta yadda kullum take sanye da hijjabi kmr matar malam, tin bata tunanin tana boye mata wani abu ne, har a yau ta fara wannan tunanin. "Baki jin dadih ne yau ma?" Ta jefo mata tambayar, ... "Eah!" Ta bata amsa Se uban zufa takeyi har lokacin dukda sanyin a.c Dake falon, Amma sam bata jinsa wani irin zafi takeji na matsifa a yau din, tinda ta tashi take jin zafin. Annah tayi jim kawai tana kallonta tace "Wai wannan wani irin ciwo ne ke damunki? Se uban rama kikeyi kina kara haske wani irin ciwo ne wannan?" KYAUTAR ALLAH tayi shiru na yan wasu daki'qu kana ta miqe tsaye, hadi da miqa tayi hamma kana ltace "ulcer cefa .." Da ido Annah ta bita se miqa takeyi tana zabga hamma kmr wadda akawa duka. "Bazaki raka niba plx?'' Tayi mgnr tana marairaicewa . "baza kiyi karin kumallo bane?" Annah ta tambayeta. KYAUTAR Allah tace "Bana jin yunwa ..." Annah ta zuba mata ido kana tace "Bakijin yunwa...haka kike kullum babu ci babu sha... Wata rana zaki kashe kanki a banza..." KYAUTAR ALLAH da tini ta gaji da tsayuwa tace "Naji...nide taso muje ki rakani..." Miqewa Annah tayi ba tare datace mata komiba ta dauko sandarta ta fara takawa a hankali..KYAUTAR ALLAH na gaba ita kuma tana biye da ita a baya se karantarta takeyi har suka isa bakin car ta bude mata tayi ta shiga dreva yaja sukabar gidan. Komawa cikin gida Annah tayi zuciya cike da tunani hadi da nazarin KYAUTAR ALLAH. yau kimanin satinshi daya da barin garin katsina, kullum suna manne a waya, sam sam bata kewarsa saboda a fari tanason sex din Amma ynzu kwata kwata ma bata kaunar jin kalmar sex...Yau ta kasance weekend ne, basuje isilamiyya ba saboda daya daga cikin malamansu ALLAH ya masa rasuwa, tin 12:20pm fatima tazo gidansu sunsha hira sosai, se kallonta fatima takeyi saboda ramar da tayi, ga hasken da tayi kullum kara karuwa yakeyi. "Frnd wai ko kin fara shafa cream ne na bleaching?" Fatima ta jefo mata tambayar. Girgiza kai KYAUTAR ALLAH tayi tace "Ah'ah bana shafa komi wlhy, ...haka ake cewa wai nayi haske kuma bana shafa komi..." Da mamaki Fatima taci gaba da kallonta tace "Kai! Kinko yi kyau kinyi fresh sosai, kamar me sabon ciki..." Jim KYAUTAR ALLAH tayi tace "waya gaya miki me ciki tanayin fari?" FATIMA tace "nasani mana, ai ina gani da sister din momy ta samu ciki haka tayi fari sol da ita tayi kyau abun sha'awah, shine su mommy keta cewa ciki ne da ita, ashe kuwa da gaske ne, bayan wasu lokuta ta haihu......" KYAUTAR ALLAH tayi jim tace "Uhum ni ai nayi karama ma da samun ciki ai kanana basa samun ciki..." Fatima tace "ta ina ma zaki samu ciki bayan baki da miji...kinsan dole se in kanada miji zaka samu ciki Ai..." KYAUTAR ALLAH tayi shiru tana tunanin kalaman fatima kana tace "Meyasa dole se da miji za a samu ciki?" Fatima ta jefeta da wani kallo na mara wayau kana tace "eah mana in babu miji ta yaya za a haihu..har yanzu frnd baki da wayau keda aka taba miki abinda miji da mata keyi Amma har yanzu bakiyi wayau ba. ." KYAUTAR ALLAH ta gallara mata harara kana tace "Wayace miki bnda wayau.." Fatima tayi Murmushi ganin ta gallara mata harara kmr kwayar idonta zasu fadi kasa, tasan ta shaqane. tace " Yi hakuri me wayau..." KYAUTAR ALLAH ta sakar mata murmushi, itama ta mayar mata da murmushi....haka suka cigaba da hira se 5:pm fatima ta bar gidan. Bayan ta dawo daga rakata, shaf tama manta bata sako hijjabi ba, sanye take da riga da zani na atamfa tuma tuman duwawuknta kmr zadu fasa zanin dake jikinta sun kara girma sosai haka ma kirjinta dukda cikin dake jikinta be gama kai 2 month ba, but ya kusa. Gyara dankwalin atamfar dake kanta tayi, dai-dai ta shigo falon... Idanuwanta dana Annah suka sarke cikin na juna, cikin lokaci kankani Annah ta shiga karewa kirar jikinta kallo, ji tayi gabanta ya yanke ya fadi, ta zabura ta miqe tsaye da yar sandarta ta gyara glass din dake idonta dan tabbatr da abinda idonta ke gane mata..."me nake gani haka KYAUTAR!!!" Annah ta fada da karfi kmr zata fasa falon. *akwai kayan mata ingantattu, babu ne kawai babu....kude ku garzayo ku siya naku kada ku bari a baku labari 08136349646* *PAID BOOK...500 ONLY...08136349646* *Tou! Readers mutanenmu... Wasu da dama suna canza lambobi suna zagina nida iyayena, suna cewa zan gani! Insha Allahu bazanga komi ba se alherih..! Bn muku mugun baki ba Amma na farku da fitar rana da faduwarta.* SAADATU BINTU ABDULLAHI Gaban KYAUTAR ALLAH ya yanke ya fadi saboda yadda Annah tayi maganar da karfi seda yan hanjin cikinta suka kad'a, tunani ta shigayi meyasa Annah ta jefeta da wannan kalmar, nan jikinta ya bata yau asirin dasuke kullewa ya budu. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!" Ta fada a ranta, yayin da zuciarta keta up up kamar zata fito fili, hnklinta in yafi dari hudu seda ya tashi. Jiki na rawa Annah ta karaso inda take ta kamo fingers dinta na hannun dama ta shiga binsu da izo a razane, taga sun ciccika sunyi aiba bul-bul dasu, har wani shinning sukeyi fiye da ada, ta kara kamo dayan hannunta na na hagu ta zuba ma fingers din nata ido, , gabanta ya kara yankewa ya fad'i zuciyarta kmr zata faso ta fito fili, har wani zazzabi taji yana neman rufeta. "Na shiga tara ni a'ee!! Dan ubanki bude bakinki in gani!" Ta daka mata tsawa, kyautar Allah kam tini jikinta ya hau rawa, tini jinin dake jikinta suka rikide, suka fara bata zafi a cikin jikinta, nan da nan zufa ta fara karyo mata. Jiki na rawa ta budewa Annah bakinta,... Annah ta lalleqa cikin bakin nata, ta dawo ta daga harshenta, ta lalleqa, ta gwale kwayar idonta kallo daya tawa kwayar idon nata jikinta yayi sanyi, zuciyarta ta fara barazanar fitowa zahirin ALLAH ta'alah. "Haba! Wallahi ciki gareki!" Annah ta fada a razane Ba ita da tayi magabarba hatta KYAUTAR ALLAH seda hantar cikinta ta juya, ruwan dake yawo a jijiyoyin jininta suka birkice saura kadan su hade da jinin jikinta saboda tsabar firgici. Mamakin da Annah keyi shine ina ta samu ciki, bayan tayi period da RASLAN ya sadu da ita ballan tana tace cikin nashi ne, tana ma da tabbacin a lokacin da wuya in ciki ya shiga, kuma ma ai ita a ganinta RASLAN be haihuwa ta ina zema KYAUTAR ALLAH ciki, bayan matarsa da suke tare sunfi shekara da shekaru ko batan wata bata tabaji ance tayiba. "Na shiga tara! Na lalace! Na mutuh! Na tambad'e! Duniyata ta tankad'e da ni! Ni naga shiga uku takabar siriki! Wannan yarinya kin cuceni kin cuci rayuwata!" Annah ta fashe da matsananincin kuka rai a dagule, KYAUTAR ALLAH ma fashewa tayi da kukan cikin tsananin dimauta da dumbin tashin hankali. "Shegiya! Yar iska! Kukan uban me kikeyi! Dan kutmar ubanki ina kika samu ciki!!" Annah ta jefo mata tambayar cikin kuka da tsananin bacin rai. Kara fashewa da kuka KYAUTAR ALLAH tayi ta sauke idonta kasa, tana girgiza kai kawai fuskarta dauke da dumbin tashin hankali, hadi da rud'ani. se zufa kawai ke kwarara a goshinta, da duk sassan jikinta lungu ds saqo, zanin dake jikintama barazanar faduwa yakeyi ta kamoshi ta riqeshi gam a hannunta. Ran Annah ya kara baci matuka tinda take da KYAUTAR ALLAH bata taba bata mata rai ba irin na yau, ta riga ta gama sadaqarwa wani dan iskan ne ya lallabo yama KYAUTAR ALLAH ciki, da ace RASLAN na haihuwa ne dase tace shi ya zagaya ya narka mata ciki. "Na shigesu! Na bani! Dan kutmar ubanki baza ki bani amsaba! gidan durun uwar waye kika samo cikin shege! Wani la'anan nan ne ya miki ciki!" Annah ta fada zuciya cike da tsananin bacin ranta ji takeyi kmr ta kasheta da duka a lokacin. Zubewa kasa tayi hadi dayin kneel down a kan guiwowinta kawai ta kara fashewa da wani matsanancin kuka saboda batasan wacce iriyar amsa zata bawa Annah ba a kan tambayar datake mata. Annah ta kara fashewa da kuka har lokacin idanuwanta nata yawo a duk sassan jikin KYAUTAR ALLAH, ta riga ta gama tabbatrwa shigar sabon ciki gareta a jikinta, ga alamomi nan sun bayyaba, basema an gaya makaba, Fashewa ta karayi da kuka "kin cuceni! Kin cuceni! Asheke muna fuka ce bansaniba! Haba daushen goro yayi kama da goro! shine dalilin dayasa kullum kike kunshe da hijjabi! To yau dubunki ta cika! Kin cuceni kuma kin cuci kanki! Iya cutata kawai kikayi amma baki lalatamin rayuwaba! Ke ko kin cuci kanki kuma kin lalata rayuwarki a banza a hofi! Kin bawa wani katon banza al'aurarki ya lalataki a banza a hofi! ALLAH ya isa tsakanina dake rukayya!!" Zuciya ta debeta kawai ta shiga rada mata sandar karfen da take dogawara, sam bata gani saboda tsananin bacin rai, tana dukanta da sandar tana tambayarta "gidan ubanwa kima samu ciki!! Wani dan gaba da fatihar ne yayi miki cikin gaba da fatihah! Kin cuceni kin batamin zuri'ah! Kin dauko min dan shege! ALLAH ya isa tsakanina dake!!!" Annah ke fadi still se dukanta takeyi da sandar, sosai takejin zafin sandar nan ta shiga kurma ihu, kmr ranta ze fita, taba bawa Annah hakuri... Ihun nata ne ya ankarar dasu jummai da laraba dake kiching suna shirya abincin dare, dakatawa sukayi da aikace aikacen dasukeyi saboda kukan dasukejiyowa a falon Annah, ba wani bata lokaci suka nufo falon